AMN Hausa

AMN Hausa ku Kasance da AMN HAUSA 🌍
Domin Samun Labarai, Video da Bayanai Cikin Harshen Hausa Daga Nigeria 🇳🇬 da Kasashen Ketare.

Bayan Kasar Najeriya ta samu 'yanci daga mulkin Turawa, Shehu Ibrahim Inyass RTA ya kawo ziyara Najeriya ta musamman dom...
25/08/2026

Bayan Kasar Najeriya ta samu 'yanci daga mulkin Turawa, Shehu Ibrahim Inyass RTA ya kawo ziyara Najeriya ta musamman domin taya murnan samun 'yanci, da Shehu ya gana da Firayim minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya kamata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu (SAW), kamar yanda abokin aikin ka Shugaban Kasa wato (Head Of State) Namdi Azikiwe yake hutun Kirsimeti, nan da nan Sir Abubakar Tafawa Balewa ya Aika da bukatar wannan Dokar Majalisa. Bayan Anyi Zafaffiyar Mahawara Daga Karshe dai Majilisa ta Amince da ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal na kowace shekara ya zama ranar hutu, kuma nan ta ke Tafawa Balewa ya sanya Hannu a wannan doka. Wannan shi ne dalilin da yasa duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal gwamnati ke bada hutu.

Follow AMN Hausa

24/08/2026

Kashedi zuwaga Naja'atu daga Mal. Alkali Zaria

Follow AMN Hausa

Akwai Malamai Magada Annabawa,Akwai Malamai Magada ArnanBaya,Allah Kasa Muna Cikin Almajiran Na Farkon Bil Haqqi....Foll...
24/08/2026

Akwai Malamai Magada Annabawa,Akwai Malamai Magada Arnan
Baya,Allah Kasa Muna Cikin Almajiran Na Farkon Bil Haqqi....

Follow AMN Hausa

Za mu koyar da malamai irin huɗubobin da za su gabatar wa mabiya domin fahimtar muhimmancin sake zaɓen Shugaba Bola Ahme...
24/08/2026

Za mu koyar da malamai irin huɗubobin da za su gabatar wa mabiya domin fahimtar muhimmancin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 matsayin sa na musulmi ~ Shaikh Saleh Pakistan

Follow AMN Hausa

Sheikh Halliru Maraya Ya Samu Mukamin Daraktan Tattaro Goyon Bayan Al’ummar Musulmi A Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu....
22/08/2026

Sheikh Halliru Maraya Ya Samu Mukamin Daraktan Tattaro Goyon Bayan Al’ummar Musulmi A Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu.

Follow AMN Hausa

Muna Kira Ga Masu Yin Abubuwan Da Ba Su Dace Ba Da Sunan Bikin Mauludi Da Su Ji Tsoron Allah, Saboda Da Yawa Ana Yin Abu...
21/08/2026

Muna Kira Ga Masu Yin Abubuwan Da Ba Su Dace Ba Da Sunan Bikin Mauludi Da Su Ji Tsoron Allah, Saboda Da Yawa Ana Yin Abubuwa Waɗanda Ba Addini Ba Ne, Kuma Irin Waɗannan Mutanen Ko Ba A Ranar Mauludi Ba Sun Saba Yin Irin Wannan Ɓarnar A Gidajensu, Don Haka Su Ji Tsoron Allah, Cewar Ustaz Junaidu Bauchi
Follow AMN Hausa

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, a ƙasar Nijar.Jarumin ya ...
15/08/2026

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, a ƙasar Nijar.

Jarumin ya bayyana cewa ya yi sabon auren ne da fatan dacewa da wannan lokaci na watan Rabi’ul Awwal, yana mai neman addu’a daga masoyansa da magoya bayansa domin samun zaman lafiya da dorewar auren.

A wani bidiyo bayan bikin, Zango ya bayyana godiyarsa ga Allah, tare da tura saƙo ga masu sukar sabon auren nasa.

Jarumin ya ce bai taɓa shiga aure da niyyar ya rabu da matar ba, yana mai cewa rabuwar da ta faru a auren da ya gabata ƙaddara ce.

Zango ya kuma yi kira ga masoyansa da su ci gaba da yi masa addu’a, musamman domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a sabon gidansa.
Follow AMN Hausa

Duk Nigeria ba gari kamar Kano. Inji Jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq. A wata hira da aka yi da shi a wani gidan jarid...
14/08/2026

Duk Nigeria ba gari kamar Kano. Inji Jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq. A wata hira da aka yi da shi a wani gidan jarida, ya fadi hujjojinsa duk da cewa shi ba haifaffen jihar kano ba ne, ya zo ne daga garin Jos, amma ya zabi ya rayu a jihar Kano saboda Aminci da kariya da garin ya samu saboda darajar Bayin Allah da suke rayuwa a garin.
Sadiq ya ce a Kano ne za ka tarar mutane za su tafi kasuwa amma a hanyar su ta zuwa kasuwar suna tafe suna ambaton Allah (zikiri) ya ce kaso 90 cikin dari haka mutanen kano suke. Ya alakanta zaman lafiya da yalwar arzikin jihar kano da wannan kyakkyawar Dabi'ar ta mutanen Kano. Shiyasa wasu da dama ba su san cewa shi ba haifaffen jihar kano ba ne. Saboda ya jima da tattaro kayansa ya dawo kano da zama na dindindin shi da iyalansa gabadaya.
Sadiq ya na son nishadi da wasa musamman kwallon kafa, kuma ya iya sosai. Kuma gaskiya yana da Addini. Shiyasa Kanawa su ke sonsa kamar yadda ya ke son su.

Allah Ya karawa kano Arziki da albarka da sauran Jihohin Arewa da Nigeria da dukkanin Kasashen Musulmi a duniya.

AMN Hausa

Aljani ya fi tsoron ɗan'adam akan yadda ɗan'adam yake tsoron aljani. Idan Allah Ya sa ka haɗu da aljani ya ƙura maka Ido...
13/08/2026

Aljani ya fi tsoron ɗan'adam akan yadda ɗan'adam yake tsoron aljani. Idan Allah Ya sa ka haɗu da aljani ya ƙura maka Ido, kai ma ka zare masa Ido zai gudu. Idan ka ga aljani ka ji tsoro ka gudu to ya samu kanka kenan; saboda haka, in ya taho kai ma ka tunkare shi kana karanta Ayatul-Kursiyu ba yadda ya iya da kai".

‎In Ji Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemo, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Follow AMN Hausa

Na janye fatawar da na bayar cewa idan mutum ya saida fili, gida ko gona ya sanya kuɗin a kasuwanci kuɗin ba zai yi alba...
12/08/2026

Na janye fatawar da na bayar cewa idan mutum ya saida fili, gida ko gona ya sanya kuɗin a kasuwanci kuɗin ba zai yi albarka ba; jarin zai rushe. Bayan zurfafa bincike da tattaunawa da malamaina na gano cewa hadisin bai inganta ba". In Ji Farfesa Mansur Isah Yelwa.

Me zaku ce?

Follow AMN Hausa

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share