MAI ALAWA Schools TOFA

MAI ALAWA Schools TOFA

Share

Madallah muna fatan cigaba a wannan makaranta mai albarka. Alfarmar Annabi Muhammadu

18/03/2023

ﺗﻤﻨﻴﺖ ﺍﻟﺮﺣﻴﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
ﻟﺸﺪﺓ ﻣﺎ ﺭﺃﻳﺖ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻔﻮﺭ

ﻧﺴﺎﺀٌ ﻗﺪ ﻛَﺸَﻔْﻦَ ﻭﺟﻮﻫﻬﻦ
ﻭَﺃﻋﻨﺎﻗًﺎ ﻭﻣﺎ ﻓﻮﻕ ﺍﻟﺼﺪﻭﺭ

ﻟَﺒِﺴْﻦَ ﻣﻼﺑﺴًﺎ ﻻ ﺧﻴﺮَ ﻓﻴﻬﺎ
ﻣُﺰَﺧْﺮَﻓﺔً ﺗَﺴﻮﻕُ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺸﺮﻭﺭ

ﻗﻤﻴﺼًﺎ ﺛﻢ بِنْطالًا ﻗﺼﻴﺮًﺍ
ﻭﻣﻨﻪ ﺗَﻔﻮﺡُ ﺭﺍﺋﺤﺔُ ﺍﻟﻌﻄﻮﺭ

ﺇﺫﺍ ﺧَﺮَﺟَﺖْ ﻓﺘﺎﺓُ ﺍﻟﻌﺼﺮِ ﻓﻴﻨﺎ
ﻭَﻣَﺮَّﺕْ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺀِ ﺃﻭ ﺍﻟﺒُﻜﻮﺭ

ﺭﺃﻳْﺖَ ﻟﻬﺎ ﻓﻨﻮﻧًﺎ ﻣﻦ ﺳُﻔﻮﺭ
ﻣﺎ ﺷَﻬِﺪَﺕْ ﺑِﻪِ ﻣﺎﺽِ ﺍﻟﻌﺼﻮﺭ

ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻔﺘﻴﻦ ﻗﺪ ﻭﺿﻌﺖ ﺳﻤﻮﻣًﺎ
وﺃﻟﻘﺖ ﺷﻌﺮﻫﺎ ﺧﻠﻒ ﺍﻟﻈﻬﻮﺭ

ﻭَكُحْلًا ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﻮﻥ ﻳﻜﺎﺩ ﻳَﺴْﺒِﻲ
ﻋﻘﻮﻝَ ﺍﻟﻨﺎﻇﺮﻳﻦ ﺑﻼ ﺧﻤﻮﺭ

ﻭﻗﺪ ﻧَﺴِﻴَﺖْ ﺑﺄﻥ ﺍﻟﻤﻮﺕَ ﻳﺄﺗﻲ
ﻭَﺗُﻤْﺴﻲ ﻋﻦ ﻗﺮﻳﺐٍ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ

ﻭَﺗَﻔْﻨَﻰ ﻛﻞُّ ﻟَﺬّﺍﺕِ ﻭَﺗُﺠْﺰَﻯ
ﺑﻤﺎ ﻋَﻤِﻠَﺘْﻪُ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺸﻮﺭ

ﻓﻴﺎ ﺃَﻣَﺔَ ﺍﻹﻟﻪِ ﻫَﻠُﻢَّ ﺗﻮﺑﻲ
ﻭَﻋُﻮﺩِﻱ ﺍﻵﻥَ ﻟﻠﺮﺏِّ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ‏

08/06/2022

Yadda za kuci Nasarar Korar Tsaka Daga Gidan ku

Kasamo tafarnuwa da gishiri saika shafe tafarnuwar da gishiri sai ka jejjefa ta akowanne bangare na gidan.
Da yardar Allah bazata sake dawowa ba.
Ina rokon duk wanda ya karanta don Allah yayi sharing saboda wasu su amfana.

30/03/2022
19/02/2021
05/10/2020

يوم العلماء!!
المعلم المخلص في عمله يشبه الأنبياء، النبي ينير لنا طريقنا إلى الجنة، والمعلم يقودنا في الحياة من ظلمات الجهل الى نور العلم.
جزى الله علماءنا بالخيرات.

30/09/2020

TAIKAITACCEN TARIHIN SHEIKH SANI HASSAN KAFANGA RTA.

Daga Salihu A Adam

Nasabarsa shi ne:-Sheikh Muh'd Sani dan Hassan dan Muh'd Dikko dan Ahmad dan Ahmad mutumin Borno, daga kabilar Kanuri.

Kakansa na uku ya yi hijira tare da iyalansa da 'ya'yansa daga garin Guru daya daga cikin yankunan Masarautar Barno wacce ta yi shura da "Anuzaka" daya daga cikin jihar Yobe a yanzu, yataho zuwa garin Kibiya jihar Kano, ya yada zango a can kuma 'ya'yansa sun auri mutanen garin Kibiya.

Kakansa Muh'd Dikko ya tawo karamar hukumar Kano Municipal tare da 'ya'yansa a ciki a kwai fasihin malami wato Malam Hassan tare da Sayyada A'isha, wato Mahaifan Sheikh Sani Kafanga da niyar zama sun zauna a unguwar Tudun Wada kusa da Jakara a wani wuri da aka fi sani da Kafanga. Sunan wata rijiya ne da ta rushe sai aka yi gini a kanta kuma ake kiran bigirenta da kusa da ita da wannan suna Kafanga.

Haihuwarsa: An Sheikh Sani Kafanga a shekarar 1330 AH daidai da 1912 A.D. A unguwar Kafanga kuma a gidan Mahaifinsa.

Tasowarsa da neman Iliminsa: Shehu ya taso akan tsananin kwadayi da riko da sunnar Manzon Allah (S.A.W.) da kaucewa hanyar shaidan da son zuciya, ya likewa zaman masallaci da jiran sallah. Ya shagala da neman Ilimi da Ilimantarwa, bai taba tsoron fadin gaskiya akan kowa ba, farko malaminsa shi ne Mahaifinsa wato Malam Hassan dan Malam Dikko inda ya fara da karatun Rashada har zuwa kan Lawwali tare da karatun Alqur'ani har ya sauke duk a gurin Mahaifinsa ya kai shi gurin Sheikh Rabiu Dan Tinki Mahaifin Khalifa Isiyaqa Rabiu inda karayin karatun Alqur'ani da tajwidi da Nahawu a gurinsa.

Daga nan Shehu ya ci gaba da mai da hankali wajen neman Ilimi da fahimtarsa, inda ya hadu da babban Shehi Sheikh Abubakar Mijinyawa Bakin Ruwa da Sheikh Muhammad Salga wanda gurin sa ne ya karbi darikar Tijjaniya. Sheikh Sani Kafanga ya yi tarbiyatul azkar a gurin Shehul Islam Sheikh Ibrahim Niass RTA.

Gudunmawarsa a musulunci : Shehu bai yi ta rago ba ya mike tsaye kyam da ruhinsa da jikansa da kafarsa don daukaka addinin Allah da dasa shi a cikin zukatan matasa ta hanyar wa'azi da rubuce-rubuce kai har ma da yawon musulantarwa.

Sheikh Sani Kafanga ya rubuta litattafai kusan tamanin (80) guda arba'in nasa ne na kansa (40) Arba'in kuma wadanda ya yi musu sharhi ne, daga cikin mafi shurarsu :
(1)Mir'tusshabban (2)Mir'atul Ikwan (3)Mir'atul haqqi (4)Gayatul amani (5)Kitabuttaisiri (6)Nainul amani (7)Sabilarrashadi (7)Minahul Hanidah. Daidai sauransu.

Wasu daga cikin Almajiransa : Sheikh Nuhu Sallau Dausayi, Sheikh Aminu Sanda, Sheikh Ahmadu Gabari (Malamin Dare), Sheikh Musa Ali Gabari, Sheikh Abubakar Hanga, Sheikh Ibrahim Warure, Sheikh Ibrahim Akwa, Alhaji Abdulyasari mai littafi. Daidai sauransu.

Wafatinsa : Sheikh Sani Kafanga ya yi wafati cikin ranar Litinin 25 ga watan shawwal 1409 A.H daidai da 29, May 1989 A.D yana shekara 79. An binne shi a makabatar Mai Kargo dake Goron Dutse. Allah ya ya yi masa rahama, ya ba mu albarkarsa. Amin.

Allah ya karawa Khalifa Hassan Kafanga lafiya da 'yan uwa musulmi baki daya.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address

Tofa Town, Tofa Local Government
Kano
KANO