17/02/2026
🕌 DA DUMI-DUMI 🕌
An tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan 1447H a Saudi Arabia.
Hukumar kula da harkokin shari’a da ganin wata ta sanar da cewa, za a fara azumin watan Ramadan daga daren yau, wanda ya yi daidai da shekarar 2026 Miladiyya.
Ramadan wata ne na rahama, gafara da kubuta daga wuta. Wata ne da Al-Qur’ani ya sauka, kuma lokaci ne na ƙara kusanci da Allah ta hanyar azumi, sallah (Qiyamul-Layl), sadaqa da sauran ibadu.
Muna roƙon Allah ﷻ Ya karɓi azuminmu, tsayuwar darenmu da addu’o’inmu, Ya sa mu dace da cin moriyar wannan wata mai albarka
16/02/2026
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da sabuwar hula da take nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu yayin da za a yi bikin karɓar sa zuwa jam'iyyar APC a yau a jihar Kano.
16/02/2026
Hadin gwiwar jami’an tsaro sun lalata manyan sansanonin ’yan bindiga uku a Jihar Kogi tare da kubutar da wasu mutanen da aka yi garkuwa da su a wuraren.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labara na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar a ranar Lahadi 15 ga Fabrairu 2026.
Sanarwar ta ce hadin gwiwar ofishin Mai ba Shugaban kasa shawara kan Tsaro, rundunar Sojin ƙasar nan ta 12, rundunar ruwa, rundunar sama, ’yan sanda, jami’an DSS da kuma kungiyoyin sa kai da mafarauta ne s**a kai farmakin.
Sanarwar ta kara da cewa an lalata sansanonin gaba daya tare da kubutar da mutanen da aka tsare a wuraren, yayin da wasu da ake zargi s**a rasa rayukansu a yayin artabun.
Kazalika, Gwamnatin Jihar Kogi ta kai wadanda aka kubutar cibiyoyin lafiya domin kula da su, sannan daga baya za a mayar da su ga iyalansu.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da aiki da hukumomin tsaro domin dakile ayyukan ’yan bindiga a fadin jihar.
- Arewa Updates
16/02/2026
Gobarar dai ta ɓarke ne daga ranar Asabar inda ta ci har zuwa Lahadi a wasu rukunin shaguna da ake yi wa laƙabi da Gidan Gilas, inda aka yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.
Hotuna da bidiyo da aka yaɗa sun nuna yadda hayaƙi s**a turnuƙe saman kasuwar, yayin da shaguna s**a k**a da wuta tare da ƙonewar kayayyakin masarufi masu ɗumbin yawa.
13/02/2026
Zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin kan kowa-Ministan Tsaro CG Musa
Babban Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa ana iya cimma zaman lafiya mai ɗorewa ne kawai idan aka haɗa ƙoƙarin tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi, daidaiton zamantakewa, da ci gaban ɗan Adam.
Ya ce yaƙi da matsalar tsaro da ƙauracewar jama’a daga gidajensu ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, ya na buƙatar haɗin gwiwar duka sassan gwamnati, al’umma da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taron kan ilimi da zaman lafiya da aka gudanar a birnin Legas.
A cewarsa, farfaɗo da rayuwar jama’a, gina al’ummomi, da ƙarfafa zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa dole ne su kasance tare da ayyukan tsaro. Ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin ci gaba da na farar hula.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar magance waɗannan ƙalubale ta hanyar sabbin dabaru masu haɗa kai da ɗorewa, domin kare jama’a, tabbatar da tsaro, da gina ƙasa mai wadata ga kowa.
12/02/2026
Jami’an tsaro sun kwace fasfon El-Rufai bayan yunkurin k**a shi ya ci tura – Muyiwa
An yi yunkurin k**a tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis.
Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya bayyana hakan ta cikin jerin sakonni da bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Ya ce El-Rufai na dawowa ne daga birnin Cairo na kasar Masar lokacin da jami’an tsaro s**a tare shi.
Adekeye ya ce jami’an sun nufi tsohon gwamnan ne da zarar ya sauka daga jirginsa, inda s**a nemi su tafi da shi domin tsare shi.
A cewarsa, tsohon gwamnan ya ki bin su, yana mai jaddada cewa ba zai amince da bukatar ba sai an gabatar masa da gayyata ta hukuma.
Sakon ya ce: “Jami’an tsaro a yau sun yi yunkurin k**a Malam Nasir El-Rufai yayin da ya iso daga Cairo. Malam El-Rufai ya ki bin su ba tare da gayyata ta hukuma ba.”
Adekeye ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaron sun kwace fasfon tsohon gwamnan yayin da lamarin ke faruwa.
“Duk da haka, sun kwace fasfonsa daga hannun wani mataimaki,” in ji shi.
12/02/2026
Alhamdulillah!
Cikin yardar Allah, mun ƙaddamar da sabon page mai suna:⬇️⬇️⬇️
Ayzan Islamic Channel ✅✅✅
Manufarmu:
Yada ilimi da fadakarwar Musulunci, tare da kawo muku:
• Tarihin rayuwar magabata da yadda s**a gudanar da bautar Allah 🌿
• Guraren da Annabawa da Sahabbai s**a rayu 🏛️
• Karatuttuka na musamman, musamman Watan Azumi 📖✨
• Tafsirai da karatuttuka domin ƙarfafa imani da ilimi
• Nasiha da fadakarwa ga al’umma domin inganta rayuwar Musulmi
Ku biyo mu yanzu, ku yi sharing domin yaduwar ilimi da hidimar addini ga sauran ‘yan uwa Musulmi!
Allah Ya datar damu Ya dawwamar damu Bisa Tafarkin addinin Musulunci 🤲