30/08/2025
SIRRUKAN BISHIYAR GUAVA (Maganin Gargajiya)
بسم الله الرحمن الرحيم
Allah Bai Halicci Wata Bishiya ko ganye a banza ba, kowane bishiya da ya halitta tana da irin sirrukan ta da magunguna da take yi a jiki dda ruhin ɗan Adam.
A yau zamu yi magana akan Bishiyar Guava da amfaninta a magungunan gargajiya:
GANYEN GUAVA:
Ana Tafasa Ganyen Guava A Ruwa, A Sha Shi Kamar Shayi.
Yana Maganin:
1. Zawo (diarrhea)
2. Ciwon Ciki Da Kumburin Ciki
3. Matsalar Narkewar Abinci (indigestion)
Kuma Ana Kurkure Baki Ko Wanke Baki Da Ruwan Ganyen Guava Wanda Aka Tafasa, Yana Maganin Warin Baki Yana Kuma Ƙarfafa Dadashi.
ƳAƳAN GUAVA (Guava Fruit):
1. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Ƙara Ƙarfin Garkuwar Jiki.
2. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Taimakawa Wajen Saukar Da Sugar Ko Rage Sugar Da Yake A Cikin Jini (blood sugar) Ga Masu Ciwon Sukari.
3. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Ƙara Lafiyar Ido Da Fata.
SIRRIN MAGANIN TSORO DA TASHIN HANKALI KO RUƊANI:
Idan Aka Sami Ganyen Guava Sai Ayi Shayi Dashi. Sai A Karanta Ayatul Kursiyyu Kafa 7 A Tofa A Ciki A sha. Yana Magani Na Kariya Daga Tsoro Da Ruɗani (anxiety).
A Jarraba Za A Godewa Ni'imar Allah Kuma Za A Riski Albarkar Da Take Acikin Wannan Bishiya. Ayi Mana Like Da Share Domin Al'ummar Annabi (S.A.W.A) Su Amfana.
“Allah Bai Halicci Wata Cuta Ba Sai Da Ya Halicci Maganinta.”
اللّهُمَّ اجعل في هذا الدواء نوراً وشفاءً وبركة، واحفظنا ببركة محمد وآل محمد
23/08/2025
بسم الله الرحمن الرحيم
إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ ۚ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا
اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ شَجَرَةِ ٱلنُّبُوَّةِ وَمَوضِعِ ٱلرِّسَالَةِ وَمُخْتَلَفِ ٱلْمَلاَئِكَةِ وَمَعْدِنِ ٱلْعِلْمِ وَأَهْلِ بَيْتِ ٱلْوَحْيِ
🌿 Assalamu Alaikum wa Rahmatullah
A baya mun yi muqaddima a wannan shafin namu inda muka gabatar da maqasudin abinda yasa aka buɗe wannan shafi. Yau insha Allahu zamu fara karatu inda zamu fara da kawo muku magungunan gargajiya.
"Kowane tsiro ko bishiya da Allah Ya halitta, lallai Allah ya ajiye fa'idodi masu yawan gaske acikin su, sirruka na samun waraka daga rashin lafiya da samun nutsuwar ruhi" Alhamdulillah
Yau insha Allah, zamu fara da bishiya mai matuƙar amfani wato bishiyar Darbejiya ko Maina (Neem).
✨ Ku karanta, ku jarraba sannan kuma kuyi mana sharing domin wasu su amfana.
🌿 Bishiyar Darbejiya ko Maina (Neem Tree)
Fa'ida daga Bishiyar Darbejiya🌿
🍃 Amfaninta:
Ana tafasa ganyen maina a ruwa, a Sha. Yana maganin maleriya, typhoid, da ciwon jiki.
Yanda ake amfani da ita:
Ka/ki ɗebi cikin hannu daya na ganyen darbejiya danye ko busasshe. Sai ka tafasa shi a ruwa kamar litre 1. A bar shi ya tafasa na minti 10 zuwa 15. Sai a tace.
Babba zai iya shan dan qarami kofi ko babban cokali ×2 (15ml × 2) sau biyu a rana (safe da yamma)
Yaro kuma qaramin cokali ×2 (5ml × 2) sau biyu a rana (safe da yamma).
A Sha tsawon sati daya kawai
Ana iya saka zuma aciki domin kashe ɗacin ta.
Insha Allahu acikin satin za a sami waraka.
Tana maganin maleriya, typhoid da ciwon jiki da zazzaɓi.
NB: Mata masu juna biyu su kiyaye amfani dashi.
Man Darbejiya (neem oil)
Amfani da man darbejiya yana maganin ciwon fata, ƙaiƙayi da kuraje.
Haka ma Yin wanka da ruwan ganyen neem yana maganin kurajen jiki da kaikayi.
👉 A jarraba wannan magani na gargajiya. Za aji dadi za a godewa Allah kuma za a riski albarkar da ke cikin wannan itace.
“Allah bai halicci wata cuta ba sai da ya halicci maganinta.”
🤲 اللّهُمَّ اجعل في هذا الدواء نوراً وشفاءً وبركة، واحفظنا ببركة محمد وآل محمد
23/08/2025
إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ ۚ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا
عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا
اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا حَمَلَ وَحْيَك وَبَلَّغَ رِسَالاَتِكَ وَصَلِّ
عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا أَحَلَّ حَلاَلَكَ وَحَرَّمَ حَرَامَكَ وَعَلَّمَ كِتَابَكَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا أَقَامَ ٱلصَّلاَةَ وَآتَىٰ ٱلزَّكَاةَ وَدَعَا إِلَىٰ دِينِكَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا صَدَّقَ بِوَعْدِكَ وَأَشْفَقَ مِنْ وَعِيدِكَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا غَفَرْتَ بِهِ ٱلذُّنُوبَ وَسَتَرْتَ بِهِ ٱلْعُيُوبَ وَفَرَّجْتَ بِهِ ٱلْكُرُوبَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا دَفَعْتَ بِهِ ٱلشَّقَاءَ وَكَشَفْتَ بِهِ ٱلْغَمَّاءَ وَأَجَبْتَ بِهِ ٱلدُّعَاءَ وَنَجَّيْتَ بِهِ مِنَ ٱلْبَلاَءِ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا رَحِمْتَ بِهِ ٱلْعِبَادَ وَأَحْيَيْتَ بِهِ ٱلْبِلاَدَ وَقَصَمْتَ بِهِ ٱلْجَبَابِرَةَ وَأَهْلَكْتَ بِهِ ٱلْفَرَاعِنَةَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا أَضْعَفْتَ بِهِ ٱلأَمْوَالَ وَأَحْرَزْتَ بِهِ مِنَ ٱلأَهْوَالِ وَكَسَرْتَ بِهِ ٱلأَصْنَامَ وَرَحِمْتَ بِهِ ٱلأَنَامَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ كَمَا بَعَثْتَهُ بِخَيْرِ ٱلأَدْيَانِ وَأَعْزَزْتَ بِهِ ٱلإِيمَانَ وَتَبَّرْتَ بِهِ ٱلأَوْثَانَ وَعَظَّمْتَ بِهِ ٱلْبَيْتَ ٱلْحَرَامَ وَصَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَأَهْلِ بَيْتِهِ ٱلطَّاهِرِينَ ٱلأَخْيَارِ وَسَلِّمْ تَسْلِيماً
19/08/2025
In the Name of Allah, the Most Merciful, the Most Compassionate
Peace be upon you all 🙏.
We hope this page will serve as a path of goodness and healing for everyone who follows.
We created this page, WARAKA DAGA AHLULBAYTI, to share with you:
Traditional remedies that bring physical healing
Prayers and spiritual invocations from the Ahlulbayt (AS) for protection and inner healing
Wisdom and lessons from their blessed lives to improve our hearts and daily living
🌿 True healing is not only for the body, but also for the soul and spirit.
🌸 Join us on this journey of healing through the blessings of the Ahlulbayt (AS), so we may find wellness, peace, and purification.
> Follow us, share this page, and let others benefit — for whoever shares in goodness receives a portion of its blessings.
May Allah make this page a source of healing and blessings for everyone 🤲.
19/08/2025
WARAKA DAGA AHLULBAYTI is a center of knowledge dedicated to sharing traditional remedies, spiritual secrets, and teachings from the Ahlulbayt (AS).
Here you will find:
🪷 Traditional herbal medicine and natural healing methods
🔮 Spiritual guidance, prayers, and protections
📖 Teachings and wisdom from Ahlulbayt (AS)
🌿 A bridge between tradition and modern understanding
Our mission:
👉 To bring healing for the body and the soul
👉 To purify the heart and strengthen faith
👉 To spread the wisdom of the chosen household of the Prophet (Ahlulbayt) (AS)
"Knowledge is the root of healing, and Ahlulbayt (AS) are the fountain of knowledge."
19/08/2025
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل محمد
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah
Alhamdulillah, da fatan shafin nan zai kasance alheri gare ku da mu gaba ɗaya. An buɗe wannan shafi “WARAKA DAGA AHLULBAYTI” domin:
Haska wasu hanyoyin magani na gargajiya da s**a dace da al’ada da addini.
Kawo asrar da addu'o'i domin kariya da samun waraka.
Ilmantar da mutane da hikimomin Ahlulbayti (AS) – zuriyar Manzon Allah ﷺ, waɗanda suke haske ne ga al’umma.
👉 Wannan shafi ba na kasuwanci ba ne, ba kuma na nishaɗi bane – shafi ne na ilimi, magani da kuwa ilimin ruhaniya.
Za mu kasance masu rubutu a kan:
Maganin gargajiya da yadda ake sarrafa su.
Addu’o’i da zikiri da s**a fito daga Ahlulbayti.
Ibtali, Dafa'i, Jalabi da adduo'i daga cikin Qurani domin samun waraka
Hanyoyin kare kai daga aljanu, hasada, sharrin mutane da sauran abubuwan rayuwa.
Ku kasance tare da mu, ku yi following shafin nan domin kasancewa damu a yayin da zamu shiga cikin gidan Ahlulbayti domin neman waraka.
Allah ya sanya alheri a cikin wannan tafiya.
اللهم صل على محمد وآل محمد
18/08/2025
WARAKA DAGA AHLULBAYTI shafi ne na musamman da aka ƙirƙira domin bayar da gudummawa ta hanyoyi uku:
1️⃣ Magungunan Gargajiya: Bincike da amfani da tsantsar hanyoyin gargajiya na Hausawa da sauran al’ummomi wajen maganin cututtuka, lafiya da samun natsuwar jiki.
2️⃣ Asrar da Ruhaniya (Spiritual Teachings): Ilimin ruhi, addu’o’i, hizb, da litattafan hikima domin samun kariya, arziki, nutsuwa da tsira daga dukkan sharrori.
3️⃣ Koyarwar Ahlulbayti (AS): Tsantsar ilimi da koyarwa daga zuriyar Manzon Allah ﷺ – wato Ahlulbayti, waɗanda Allah ya tsarkake su daga kowanne ƙazanta (Qur’an 33:33).
Shafin nan zai kasance cibiyar waraka da hikima, domin haɗa al’adunmu na gargajiya da kuma darussan Ahlulbayti, cikin tsabta da gaskiya.
👉 Burinmu shine: “Waraka ta jiki, waraka ta zuciya, waraka ta ruhu” – domin mutum ya rayu da lafiya da natsuwa, ya yi ibada cikin kwanciyar hankali.
18/08/2025
"بِالصِّحَّةِ تُسْتَكْمَلُ اللَّذَّة"
"With good health, enjoyment is complete"
"Da cikakkiyar lafiya, rayuwa take samun wanzuwar jin dadi da kwanciyar hankali"
Imam Ali (A.S)
Ghurar Al-Hakim