18/09/2026
Idan Annabi Alaihissalam yana son abu, ya zama wajibi kuma hujja kowane musulmi ya so wannan abun, ko yau huɗubar da liman yayi kenan a masallacin Madina.
Ya faɗi cewa an haifi Annabi Alaihissalam a Makkah, saboda haka Makkah babban waje ne a wajen Allah, sannan anan Allah ya sanya farkon ɗaki wato Ka’abah, haka nan waje ne mai aminci ga duk wanda yaje ko mutum ko dabba.
Madinah kuma nan Annabi Alaihissalam yayi Hijrah, anan kuma ya rayu har yayi wafati, sannan anan Maƙam (ƘabarinSa) yake har zuwa a tashi ƙiyama. Sannan Annabi Alaihissalam ya faɗa cewa “wanda duk ya tsorata mutan Madinah da zalinci, shi ma Allah ya tsorata shi, kuma kada Allah ya karɓi farillarsa ko nafilarsa, sannan kuma tsinuwar Allah data mutane da tavmala’iku ta tabbata akansa”
Shi ya sa abinda Hutiyawa sukayi (baifi kwana 3 ba) na kaiwa Makkah hari; laifi ne babba a wajen Allah, saboda Annabi Alaihissalam yana son Makkah da Madinah, ƙari wallahi bai taɓa zama a wani gari ba duk duniya yayi rayuwa sai iya Makkah da Madinah.
Allah ya h**e mana ganin girman duk abinda ya shafi Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.