21/05/2026
GADIR KHUM: Ranar da aka kammala Addinin Musulunci (na 1/14)
Bayan kammala Hajjin Bankwana wato (Hajjatul Wada'), na Manzon Allah (SAW) sai ya jagoranci ayarin Musulmi wajen komawa Madina. Yana tare da mutane sama da dubu ɗari (100,000+) a tare da shi – kuma wannan shi ne mafi yawan taron Musulmi da ya taɓa jagoranta.
A lokacin da s**a isa wani wuri da ake kira Ghadir Khum– wani tafki kusa da mahaɗar hanyoyi huɗu wato (Madina, Misira, Iraƙi, Sham da Najdu) – sai aka saukar da umurnin Allah ga Annabi (SAW) wato.
Ayar Tabligh (isar da saƙo) (Al-Ma'ida: 67) ta zo:
Ya Manzon Allah! Ka isar da bayanin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka,idan kuwa ba ka aikata ba, to fa k**ar ba ka isar da saƙon annabtar taka ba ne kwata-kwata! Idan kana tsro ne to Allah zai kare ka daga sharrin mutanen, Allah ba ya shiryar da kafirai masu ƙin aikata umarnin Allah!
Wannan ayar tana daga ayoyi masu zafi ba aya ce irin ta yau da kullum ba. Allah yana cewa: idan baka isar da wannan saƙo ba, to dukkan saƙonka bai isa ba!!! Wannan ya nuna cewa abin da zai faɗa yana da matuƙar muhimmanci – yana daidai da dukkan risalar Annabcinsa (sawa).
Nan take sai Annabi (SAW) ya umurci ayarin: na gaba su tsaya, na baya su hanzarto. Ya sa aka share wuri, aka haɗa kayan raƙuma ya zama mumbari. Sai ya hau, ya kalli taron, bayan ya yi godiya da Allah ya yi huɗuba sai kuma ya ɗaga hannun Imam Ali (AS) har mutane na hango fararen hammatansa, sannan ya faɗa musu cwa: Man kuntu mawlahu, fa hadha Aliyyun mawlahu.
Duk wanda na kasance shugabansa, to wannan Ali ne shugabansa ne.
Bayan haka ya ƙara da addu'ar cewa:
Allahumma waali man waalahu, wa aadi man aadaahu, wa anṣur man naṣarahu, wa akh dhul man khadhalahu, wa adir al-ḥaqqa ma'ahu ḥaythu dara.
Wato: Ya Allah, Ka taimake wanda ya taimake shi, Ka tozarta wanda ya tozarta shi, Ka sanya gaskiya ta bi shi duk inda ya juya.
Wannan ba ƙaramar magana ce ba. Kuma ba ƙaramin saƙo ne ba, wanda Annabi ya isar zuwa ga al'umma gaba ɗaya.
TO SHIN:
1. Idan har Allah Ya ce wa Annabi (sawa) "Idan baka isar da wannan saƙon ba, to k**ar baka isar da komai ba" shin me yake nufi game da muhimmancin wannan saƙon?
2. Shin akwai wani sahabi da Annabi (SAW) ya taɓa tsayar da dukan ayarin musulmi irin wannan, ya ɗaga hannunsa, ya ce wa mutane "Wannan shi ne shugabanku a cikin tarihin musulunci"?
3. Mene ne ra'ayinku a kan kalmar "mawla" shin tana nufin aboki ne kawai ko shugaba mai cikakken iko bayan manzon Allah (sawa)?
Ku biyo ni domin jin
Dalilin saukar Ayar Tabligh dalla-dalla da ra'ayoyin malaman Ahlus Sunna game da ita.
Ku biyo ni don ku ga hujjoji masu ƙarfi daga Alqur'ani, Sahihain, da littattafan malaman Sunni, inshaAllah.
Naku Mansur Yahya Bargi
18/05/2026
06/05/2026
22/12/2025
10/12/2025
08/12/2025
13/07/2025
13/07/2025
11/07/2025
10/07/2025