26/10/2025
UWAR MIJI
"Ramatu! Ke Ramatu! Wai ina Ramatun take ne?"
Ina jin ta, na yi mirsisi kamar ban ji ba, har sai da Salele cikin ɓacin rai ya ce mini, "kina ji fa Inna na kiran ki, amma kika yi banza da ita."
Na tashi na fice daga ɗakin, ina gunaguni, na nufi inda surukata ke kira na. Na same ta tsaye a ƙofar ɗakinta. Ta dube ni ta ce, "ashe kina gidan nake ta ƙwala miki kira kika ƙyale ni."
Sannan ta dubi tulin sharar da ke ƙofar ɗakinta ta ce, "yanzu saboda Allah, Ramatu, ƙofar ɗakina ta zama bola ne da har za ki tattaro sharar gidan nan ki jibge man? Idan har ƙofar ɗakina bai samu mutuncin da za a share shi ba, ai kuwa bai kamata a tara mini shara ba. Ɗan kaciya in bai ci kaza ba, ai ba ya yi bara ba ko?"
Na amsa mata, "haba Inna, yanzu duk iskar nan da ake balbalawa ba ki ga laifinta ba a kan tara miki shara sai ni? Saboda kawai an mayar da ni karkatacciyar kuka mai daɗin hawa. Da ma ita akuya mai farin baki, ai ko ba ta ci gari ba sai a ce ta ci." Na buga tsaki na koma ɗakina. Na bar ta nan tsaye tana mamaki.
Ban san dalilin da ya sa tsohuwar nan ta ɗauki karan tsana ta aza mini ba. Kusan wata uku ke nan da aurenmu da Salele, amma zama ya ƙi daɗi tsakanina da mahaifiyarsa. Kullum rigimar safe daban, ta rana daban, ta dare daban, sai ka ce kishiyoyi. To wai me ya yi zafi ne, an mutu kai na motsi? Da na ga abin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, sai na yanke wata shawara a cikin raina.
Na tafi wajen kakana da yake sayar da magungunan gargajiya, na kwashe duk abin da ke faruwa tsakanina da uwar mijina na faɗa masa, na roƙe shi da ya taimake ni da wani maganin da zan zuba mata a abinci, ta ci ta mutu kowa ya huta.
Ya yi shiru yana tunani, can ya ce mini, "wannan abu ne mai sauƙi, zan ba ki maganin da zai kashe ta. Amma fa ki sani, idan ta mutu yanzu ba wanda zai hana a tuhume ki da kisan ta, tun da kowa ya san babu ga maciji a tsakaninku. Abin da za ki yi yanzu shi ne, ki yi ƙoƙari ki canja halayenki zuwa gare ta. Ki riƙa yi mata ladabi da biyayya iyakar iyawarki har mutane su gane babu wata gaba tsakaninku. Zan ba ki maganin da za ki riƙa sanya mata cikin abinci kullum, maganin ba zai kashe ta ba sai nan da wasu 'yan watanni, kin ga idan ta mutu a lokacin, babu wanda zai zarge ki." Ya kawo magani ya ba ni.
Tun daga ranar na fara lallaɓa 'yar tsohuwar nan, hatta tufafinta da Salele ke wanke mata a da, sai na karɓe, ya kasance ni ke wanke mata yanzu, in share mata ɗakinta da ƙofar ɗakin duka. Da na ga na ciwo kanta, sai na fara zuba mata maganin nan a abinci kullum.
Wata ɗaya, wata biyu, wata uku, har aka yi wata biyar ina barbaɗa mata magani. Tsawon wannan lokaci, gaba ɗaya zamanmu ya canja salo, sai ya kasance babu wadda uwar mijina ke so kamar ni, ta ɗauke ni kamar 'yar da ta haifa, ta cikinta. Sannu a hankali sai na ji duk ƙiyayyar da nake yi mata a da, yanzu ta kau, da ma baƙin halina ne tun farko ya sanya muka yi ta rigima da juna kamar kaji.
Na koma wurin kakana domin ya ba ni makarin maganin da ya ba ni a baya, yanzu kam ba ni so ta mutu. Sai ya yi dariya ya ce, "ai da ma ba wani magani na ba ki ba, yaji ne haɗe da magi kawai k**e barbaɗa mata a abinci.
Na gode wa Allah na kuma gode wa kakana da wannan dabara. Da a ce wajen wani mugun boka na tafi, da tuni labari ya sha banban. Na zauna da surukata cikin aminci da jin daɗi. Tun daga lokacin na fahimci, ashe dai uwar miji ba kishiya ba ce, uwa ce.
Bukar Mada
20/10/2025
25/10/2025
25/10/2025
09/04/2025
29/03/2025
15/03/2025