Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano

Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano Jami'u Ahlus Sunnah (Izala Head Quarter Kano State).

29/09/2026

RADDIN MALAM GA YAN TAMORE.
Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph

Idan dai za ka faɗi gaskiya, sai ka yi rigima da mutane, musamman ’yan siyasa.Sheikh Yaqub Musa Yaqub 24/09/2026
24/09/2026

Idan dai za ka faɗi gaskiya, sai ka yi rigima da mutane, musamman ’yan siyasa.

Sheikh Yaqub Musa Yaqub
24/09/2026

23/09/2026

ABIN MAMAKI: Digirinsa na uku akan Inyass ya yi.

SHUGABAN Jibwis Nigeria NA KASA YA KAURACEWA TALLATA TINUBU A KARO NA BIYU.Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙauracewa tallar...
21/09/2026

SHUGABAN Jibwis Nigeria NA KASA YA KAURACEWA TALLATA TINUBU A KARO NA BIYU.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙauracewa tallar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu;

Inda Ya bayyana cewa: Al'umma ta na fama da matsalar tsaro, yunwa, matsin lambar rayuwa, rashin aikin yi, da mummunan talauci.

Saboda haka a samarwa al'umma mafita.

Lokacin da DG Na Shugaba Tunubu ABDUL AZIZ YARI ya Kawo wata Ziyara Ga Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah na Duniya a Kaduna Domin Yaɗa Manufar Tunubu

Shi Kuma Shugaba ya Waske da Fito masa da Abinda Ya Damu Al'umma na Kashe-Kashe da Sace Mutane da Sauransu

Muna Addu'a Allah Ya Kara Kare Mana Wannan Shugaba namu Mai Daraja
Sauran Malaman Suma Muna Addu'a Allah Ya Ganar dasu

Copied

Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano
21/09/2026

"Kar ka sake ka kira wanin Allah wannan Wanda bazai iya amfanar da kai ba Kuma bazai iya cutar da kai ba, in kuwa kai ha...
20/09/2026

"Kar ka sake ka kira wanin Allah wannan Wanda bazai iya amfanar da kai ba Kuma bazai iya cutar da kai ba, in kuwa kai hakan to lallai kana daga cikin azzalumai"
yunus 106.

Allah ka tabbatar damu akan Tauhidi har karshen rayuwarmu Kuma ka tashemu da shi a ranar Alkiyama.

Ashmar.

Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano
20/09/2026

🕌 RAHOTON TATTARA FATUN LAYYA NA JIBWIS NIGERIA – SHEKARAR 2026💰 JIBWIS Ta Tattara Kusan Naira Miliyan 190 Daga Fatun La...
18/09/2026

🕌 RAHOTON TATTARA FATUN LAYYA NA JIBWIS NIGERIA – SHEKARAR 2026

💰 JIBWIS Ta Tattara Kusan Naira Miliyan 190 Daga Fatun Layya

Shugaban Ƙungiyar JIBWIS ta Ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya karɓi rahoton tattara kuɗaɗen fatun layya na shekarar 2026 daga Kwamitin Tattara Fatun Layya na Ƙasa.

Shugaban kwamitin, Malam Lamara Azare, tare da sauran mambobin kwamitin ne s**a miƙa rahoton a wani taro da aka gudanar a Kaduna.

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yaba wa kwamitin bisa jajircewa, gaskiya da riƙon amana da s**a nuna wajen gudanar da wannan aiki. Haka kuma ya yaba wa jihohin JIBWIS a faɗin ƙasar nan bisa gudummawar da s**a bayar, tare da addu’ar Allah Ya saka musu da mafificin alheri.

🏆 Jihohi 10 na farko a tattara fatun layya:

1️⃣ Kaduna — ₦25,866,300.00
2️⃣ Kebbi — ₦25,830,950.00
3️⃣ Sokoto — ₦19,412,490.00
4️⃣ Bauchi — ₦17,595,583.00
5️⃣ Niger — ₦12,110,500.00
6️⃣ Katsina — ₦10,957,850.00
7️⃣ Zamfara — ₦10,901,250.00
8️⃣ Adamawa — ₦9,186,400.00
9️⃣ Taraba — ₦8,431,400.00
🔟 Jigawa — ₦6,547,500.00

📊 Sauran Jihohi:

11. Kano — ₦6,385,850.00
12. Gombe — ₦5,838,700.00
13. Abuja (FCT) — ₦5,370,400.00
14. Nasarawa — ₦4,239,300.00
15. Lagos — ₦3,728,555.00
16. Kogi — ₦3,162,150.00
17. Borno — ₦2,890,900.00
18. Benue — ₦1,986,500.00
19. Yobe — ₦1,854,550.00
20. Kwara — ₦1,656,150.00
21. Plateau — ₦1,634,850.00
22. Oyo — ₦1,194,672.00
23. Ogun — ₦624,903.58
24. Osun — ₦486,272.00
25. Rivers — ₦385,500.00
26. Enugu — ₦380,000.00
27. Delta — ₦335,600.00
28. Ondo — ₦202,202.42
29. Edo — ₦145,500.00
30. Bayelsa — ₦135,000.00
31. Imo — ₦110,000.00
32. Akwa Ibom — ₦87,000.00
33. Anambra — ₦76,650.00
34. Ekiti — ₦69,495.00
35. Ebonyi — ₦67,200.00
36. Cross River — ₦50,300.00
37. Abia — ₦24,000.00

💰 JIMLAR KUƊAƊEN DA AKA TATTARA

📖 Kuɗin Fatun Layya: ₦179,771,140.00

🧾 Kuɗin Rasit: ₦10,191,283.00

✅ Jimla Gaba Ɗaya: ₦189,962,423.00

Allah Ta’ala Ya ce:

﴿ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ ﴾

"Ya ku waɗanda kuka yi imani! Idan kuka taimaki addinin Allah, Allah zai taimake ku kuma Ya tabbatar da dugaduganku." (Suratul Muhammad: 7)

Annabi ﷺ ya ce:

"Allah yana taimakon bawa matuƙar bawan yana taimakon ɗan’uwansa." (Sahih Muslim)

A ƙarshe, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi addu’ar Allah Ya saka wa dukkan masu bayar da gudummawa da mafificin alheri, Ya karɓi ibadun layya, Ya ƙara wa JIBWIS albarka da ci gaba.

🤲 Allah Ya saka da alheri.

🕌 Jibwis Nigeria

DODON MUSHRIKAI. Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph Kano Hafizahullah. SUNNAH SAK.
17/09/2026

DODON MUSHRIKAI.
Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph Kano Hafizahullah.

SUNNAH SAK.

ALHAMDULILLAH. MALAM YA DAWO KARATUSheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan. 📖 KARATUN LITTAFIN SHU’ABUL IMANAlhamdulillah, an da...
16/09/2026

ALHAMDULILLAH.

MALAM YA DAWO KARATU
Sheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan.

📖 KARATUN LITTAFIN SHU’ABUL IMAN

Alhamdulillah, an dawo karatun Littafin Shu’abul Iman, tare da Sheikh Abdurrazak Yahaya Haifan Hafizahullah, a Masallacin FCDA Area II, Garki, Abuja.

Allah Ya bamu ilimi mai amfani, Ya sa mu amfana da abin da muke koya, kuma Ya taimake mu wajen aiki da shi.

Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano.
16/09/2026

DATTIJON SUNNAH. Prof. Mansur Sokoto, mni
14/09/2026

DATTIJON SUNNAH.

Prof. Mansur Sokoto, mni

SANARWAR KARASA KARATUWanda Sheikh Yaqub Musa Yaqub Sautus Sunnah Kano ya fara gabatarwa a Masallacin Juma'a na Dantamas...
04/09/2026

SANARWAR KARASA KARATU

Wanda Sheikh Yaqub Musa Yaqub Sautus Sunnah Kano ya fara gabatarwa a Masallacin Juma'a na Dantamashe dake Karamar Hukumar Ungogo.

Address

Tudun Murtala
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Tudun Murtala Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share