24/05/2025
*Ilimi* : _Makullin Cigaba a Rayuwa_
Karku bari a kashe muku guiwa ko a yaudare ku har ku daina taimakawa kanku da wasu. Ilimi shi ne makullin buɗe ƙofar cigaba a rayuwa. Wannan magana gaskiya ce, har birnin Sin.
_Idan wani ya ce maka ilimi ba shi da amfani, ka tambaye shi:_ me ya sa ƙasashen da s**a fi samun ci gaba a duniya su ne waɗanda s**a fi yalwata da ilimi? Ka bincika, za ka gano cewa ƙasashe irin su Amurka, Japan, da Jamus sune manyan ƙasashe a fannin tattalin arziki – kuma babu ɗaya daga cikinsu da bai gina kansa akan ilimi ba.
*Wane ne ke tafiyar da duniya a yau?* Technologists, engineers, da scientists. Idan kana magana kan masu kudi da ba su je makaranta ba, ka tambayi kanka: nawa ne adadin su? Kuma yawancin su, sai sun nemi masu ilimi su taimaka musu wajen tafiyar da kasuwanci.
Watakila kana koyi da wasu – 'yan siyasa, 'yan kasuwa, 'yan kwallo ko wasu – amma ko waye ke burge ka, bincika, zaka ga yana da ilimi ko ilimin ne ke taimaka masa.
*Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:
"طَلَبُ الْعِلْمِ فَرِيضَةٌ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ"
"Neman ilimi wajibi ne akan kowanne Musulmi."*
To wane zai ce ilimi ba shi da amfani?
*Ka nemi ilimi don ilimi kansa – domin ilimi ya fi jahilci.* Ba sai domin aiki ba. Idan kana da ilimi, ka fi wanda ba shi da shi damar samun aiki, daraja, da dama a ko'ina.
Akwai waɗanda ke cewa ba a samun aiki bayan karatu – amma waɗannan su kansu ba su yi karatun ba, ko kuma ‘ya’yansu ba sa yin karatu. Ka tambayi kanka: a wane ƙasa ‘ya’yan Abba Kabir Yusuf ko Ganduje ko Tinubu ke karatu? Su sun san mahimmancin ilimi, amma wasu na kokarin karkatar da ku daga neman ilimi.
Idan ka kalli duniya yau, ka ga muna kusantar wani zamani da idan baka da ilimi, sai ka zame kaya.
A baya, sana’o’i irin su duƙe da noma suna ba da riba – amma a yanzu, saboda rashin ilimi, yawancin su sun dusashe. Ilimi ne ya gano amfanin wake na kwana arba’in, masara mai sau uku a damina, da mangwaro mai yawaita tun yana ƙarami.
Har al’amura k**ar sauya lambobin waya daga tsohuwar waya zuwa sabuwa, wasu sai sun biya kudi saboda ba su da ilimin fasaha. Wannan ai ƙaramin abu ne!
Mafi yawan matasan da s**a fada cikin 'yan mining ko s**a yi asara ko sun samu riba, yawancin su rashin fahimtar bayanai ne ya jefa su cikin matsala. Idan akwai yawaitar ilimi, da an fi cin gajiyar damar zamani.
Yanzu ana maganar *Crypto* da *Digital Economy –* duniya tana tafiya zuwa duniyar dijital. Mai ilimi ne kadai zai iya morewa wannan zamanin.
*Allah ya tsaresu daga kashedin da ya sa wasu s**a daina ƙoƙari. Allah ya bamu ikon jurewa da sadaukarwa don cimma burikanmu na zama " *changer* " – waɗanda ke kawo canji. Allah ya bamu ikon taimakawa al’umma da ƙarfinmu. Allah ya mana jagora wajen ciyar da wannan yanki gaba. Allah ya tabbatar mana da imani kuma ya bamu kyakkyawan ƙarshe.
Ameen.
*ENGR. NASIR ABDULRAZAQ BELLO, GNSE*
*