18/05/2026
KORAFIN ‘YAN TSANGAYA A JAHAR JIGAWA: Ana Kira Ga Gwamnati Ta Duba Ayyukan Tsangaya Board
Daga Murya Ta Gaskiya TV
Wasu daga cikin ‘yan tsangaya da alarammomi a jihar Jigawa sun bayyana damuwa tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta sake duba yadda ake tafiyar da harkokin Tsangaya Board, musamman dangane da shugabancin Executive Secretary na hukumar.
A cewar bayanan da s**a fito daga wasu masu ruwa da tsaki a harkokin tsangaya, akwai koke-koke kan yadda ake gudanar da ayyukan hukumar ƙarƙashin jagorancin Abubakar Maje Hamisu, wanda ke kula da harkokin tsangaya a jihar ƙarƙashin gwamnatin Mai Girma Gwamna Malam Umar Namadi.
Masu korafin sun bayyana cewa, tun bayan hawansa kan muƙamin, ba a ga wasu manyan ayyuka masu tasiri ga cigaban harkokin tsangaya ba, lamarin da ya haifar da tambayoyi daga wasu ‘yan tsangaya da malamai.
Haka kuma, an bayyana cewa akwai buƙatar ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar da ƙungiyoyin mahaddata Alƙur’ani da malamai domin tattauna matsaloli da samar da hanyoyin ci gaba ga harkokin tsangaya a jihar.
Bugu da ƙari, wasu daga cikin masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan abin da s**a kira ƙarancin halartar wasu muhimman lamura da s**a shafi malamai da harkokin addini, ciki har da ziyara, jajantawa da tarukan da s**a shafi tsangaya.
Sai dai masu korafin sun ce manufarsu ba zargi ko s**a kawai ba ce, illa kira ga gwamnati domin sake duba tsarin shugabanci da tabbatar da an samu jagoranci mai kusanci da jama’a, wanda zai saurari koke-koken ‘yan tsangaya tare da fifita ci gaban ilimi da addini.
A nasu ɓangaren, shugabancin Tsangaya Media Network of Nigeria, ƙarƙashin Amb Alaramma Sani Musa Nuhu, tare da kafatanin alarammomi musamman na reshen jihar Jigawa, sun buƙaci gwamnatin Mai Girma Gwamna Malam Umar Namadi da ta yi nazari cikin adalci tare da ɗaukar matakin da ya dace domin inganta harkokin tsangaya a jihar.
Murya Ta Gaskiya TV na ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da bai wa kowane ɓangare damar bayyana matsayinsa domin tabbatar da adalci da gaskiya a rahotanni.