09/01/2026
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ*
*السَّلاَمُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ*
Yan'uwa masu albarka, a madadin wannan cibiyar me albarka ta *Ma'an Nahwan Najah Youths Awareness Development*, muna farin cikin sanar da ku cewa a yau, cikin ikon Allah (SWT), mun samu damar gudanar da *yaye dalibanmu a karo na biyu*, waɗanda muka horas da su kan *sana’ar mayafai*.
Allah ya azurta wannan cibiya da *jajirtattun malamai* masu ilimi da hangen nesa, waɗanda ke da buri na sawa matasanmu ’yan mata dabarun sana’a, domin samun ’yanci daga dogaro da rokon samari da buƙatun rayuwa.
Alhamdulillah, malamanmu sun gudanar da aikin koyarwa cikin kwarewa, sun koya wa dalibai yadda ake mayafai masu kyau da inganci, a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci.
*Daliban kuwa, sun nuna cikakken haɗin kai da sha’awar koyo*, har ta kai ga cewa malamai suna yaba musu bisa ƙoƙari da himma, lamarin da ya ƙara musu ƙarfin guiwa da kwarin gwiwa — domin manufar mu itace
*"A gudu tare, a tsira tare."*
Babu abin da zamu ce face *Alhamdulillah!*
*Mun gode da goyon bayanku da haɗin kai. Allah ya saka da alheri.*
Sing
Chairlady
*HALIMA SHUAIBU BAKANO*
Alma'arij females foundation
Ummu Musab Khairat