10/10/2025
*Mafita ga Musilmi, Gomnati da Malamai a Jihar Kano akan Lamarin Mal Lawan Triumph da Sheik Abdujjabbar*
Kira/WhatsApp
+2347082858755
[email protected]
`Warware wadannan matsalolin da samar da mafita da waraka me dorewa a jihar kano da Nigeria gaba daya`
Ni Nurse Adamu Alhassan (Liman), ina sanar da Gomnati, Malamai da al umar jihar Kano, cewa Allah ya azurtani da fahimta da gano hanyar warware wannan matsala dama shauran matsalolin dasuke damun musilmin jihar kano dama Nigeria gaba daya.
Ina neman abani jagorancin wannan matsala cikin yardar Allah za awarwareta da samarwa musilmi mafita.
Zan kafa Komiti me wakilai kamar haka.
1. Mutum daya daga Izala/Jibwis
2. Mutum daya daga Tijjaniyya
3. Mutum daya daga Qadiriyya
4. Mutum daya daga Shi'a
5. Mutum daya daga Qur'aniyyun.
- Wakilai (2) daga Majalisar Shura
- Wakilai (2) daga Majalisar Malamai (Mal. Ibrahim khalil + wani).
- Nine Shugaban Komiti
Zamiyi zama (3)
1. Zamu zauna ajunanmu mutattauna akan mas'alar akan adalci ba nuna wariya. (Akalla awa 3 ko sama, musamar da mafita ta yanzu da nan gaba
2. Zamu Zauna da Mal Lawan Triumph
3. Zamu zauna da Sheik Abdujjabbar
Bayan tabbatar da adalci garesu da samar da mafita anan gaba, zamu tabbatar da zartar da doka da zata tabbatar da kiyaye ladabi ga Annabi S.A.W, kiyaye imani da gujewa shirka ko kafirci, hadin kan musilmi, rage rabuwar kai, samar da kauna, soyayya da girmama juna.
Zamu zauna da wakilan kiristoci na wannan jaha don suma abin ya shafesu.
Bayan haka zamuyi kokari muga ragowar jahohi ma sun tabbatar da hakan cikin yardar Allah.
Allah kabamu dacewa, amin.
`Rantsuwa/Tabbatarwa`
Ina me rantsewa da Allah, da gaske nake, babu wasa aciki. Kuma na yarda ina da maslaha akan wannan matsalar da nagano fil-kitab was-sunnah.
Idan ba dagaske nake ba aimin bulala (80) asani agidan yari na shekara daya (1).
*JANHANKALI*
Wani zai mamaki akan maganar nan... Amma duk wanda yasanni sosai ba lalle yayi ba. Duk da cewa babu wanda yasanni Haqiqatan sai Allah. Don haka kada kayi mamaki.
_Allah shi yake halitta kuma yayi zabi acikinta Sur, Qasas, aya 67._
Abinda ake bukata awannan mas'ala shine Ilimi, tsoran Allah/ikhlasi, hankali, adalci, amana da karfin zartar da gaskiya. Ba malami bane ni, kuma banfi malaman sani ba, kuma banfi kowa ba, amma ba kowa yake da karfin adalci da ikon danne son zuciyarsa ba.
Kuma akwai irina da yawa da suke da ikon haka sedai ba asonsu ba, kuma basuda dama.
Don haka nayi imani, in sha Allah, ina da ikon tafiyar da wannan al amari
_Hadisin Saidil khudri, Annabi S.A.W yace "wanda yaga abinki ya gyara/canza shi da hannunsa, idan bashida iko, yayi da harshensa idan bashida iko, yaki da zuciyarsa, amma wannan shine mafi raunin imani", riwayar Muslim_
Banida ikon tabbatar da adalci acikin wannan lamari sedai idan masu iko sun bani dama, nayi imani zan iya. Kuma za'asha mamaki, kowanne bangare se sun yarda cewa anyi adalci in sha Allah babu siyasa, ba bangaranci babu wariya.
Akarshe ina kira ga yan uwa na kowanne bangare, duk me iko da yasanar ko yada wannan sako har zuwa ga masu iko, musamman gomna don nayarda yana son yin adalci, in kayi hakan ka bada gudunmawa wajen yin adalci, hadin kan musilmi da samar da zaman lafiya a tsakanin al umma.
_Nr. Adamu Alhassan (Liman_
_Me rajin samar da hadin kan al ummar Annabi S.A.W._
Kira/WhatsApp
+2347082858755
[email protected]