Abu Albany MMR
we aim to spread *authentic Islamic teachings*, inspiring , and practical guidance about pious Deen
13/12/2025
Karatun Kur'ani yana amfani don saboda ranar Kiyama zai yi ceto ga ma'abotan sa.
Muna da Sana'a
AlhamdulilLah
Babu wanda ya kamata a rayuwar duniyar nan ka kulla alaka dasu me karfi sama da yan uwanka, domin kuwa sune abokan rayuwa na dindindin wanda Allah ya kulla wannan zumunci tsakanin ka dasu, dukkan wata dangantaka da take tsakanin ka da wani ko wata zabi ce a gare ka, amma banda dangantakar da take tsakanin ka da yan uwanka wannan itace kadai alakar da Allah ya hadata kai tsaye, wannan itama wata Ni'ima ce a gare ka. Shiyasa akaso sufi kowa kusanci dakai fiye da matarka, abokanka dama sauran mutane, domin su yan uwa suna tsayawa tare dakai tun daga farkon rayuwa har zuwa karshe, akasin wasu basu ba wanda za suzo daga baya kuma su iya tafiya kafin karshe. Allah ka barmu da masoyan mu, Ina sonku saboda Allah.
Alaramma Abdurrahim Mansur Yelwa
Capacity to the core
29/07/2025
Wani daga cikin magabata ya kira yayansa lokacin da yake gargarar mutuwa yace musu kowanne ya samo Assiwak guda daya, bayan sun samo sai yace su hadasu waje daya sannan ya bawa babban dansa yace ya karya wannan asuwakin, yayi iya yinsa amma ya kasa, sai ya dauki guda daya ya bawa karamin ciki yace ya karya shi, yana bashi nan take ya balla shi.
Sai wannan bawan Allah yace musu haka misalin hadin kai yake, idan kuka hada kanku ba wanda ya isa ya balla ku komai karfin sa, haka kuma idan kuka rarrabu kowanne zai iya karya ku duk raunin sa. So nake ko bayan raina karku sake ku raba kanku domin idan kukayi haka babu abinda zaku cimma.
03/07/2025
Allah ka rufa mn asiri duniya da lahira
23/06/2025
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum yace:[mutum ne yana da kamfanin shinkafa sai yace da manager ya bawa wancan buhu 5, ka bawa baban ka buhu 3, kanin ka buhu 1,sai wannan manager ya aikata abinda mai kamfanin nan yayi masa umarni dashi, shin wannan manager yana da asara?, to haka misalin wanda Allah ta'ala ya bashi arziki da horewa kenan, don haka masu kudi ku bayar daga cikin dukiyoyin ku, domin Allah ne ya wakilta ka akan dukiyar amma ba taka bace, kayi amfani da wannan damar domin a koda yaushe zaka iya rasa wannan damar. Allah kayi mn arziki, Allah ya taimake mu 🤲 😊.
05/06/2025
Allahu Akbar
*MAFI ALKHAIRIN ADDU'A ADDU'AR RANAR ARAFAH*
-
Addu'ar ranar Arfa ita ce mafi alherin addu'o'i.
Manzon Allah (SAW) Yace: "Mafi alherin addu'a ita ce addu'ar
ranar Arfa, kuma mafi alherin abinda na fada ni da Annabawan dake
gabani na shine...
LA ILAHA ILLALLAHU
WAHDAHU LA SHAREEKA LAHU,
LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADEER."
Tirmizy
_Zaku iya biyomu a_
TELEGRAM CHANNEL 👇
https://t.me/QAIMATUL_UQALA_islamic_reminder
FACEBOOK 👇
https://www.facebook.com/share/18iRJyHxdA/
INSTAGRAM 👇
https://www.instagram.com/qa_imatu_uqala?igsh=dzJreWpxMm9xcTRz
WHATSAPP CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VapBzDFG8l5Fbj6pDU13
26/05/2025
GOMAN FARKON DHUL-HIJJAH.
-
"Dukkanin wani mutumin kirki na ƙwarai wanda yake neman kusanci ga ubangijinsa Allah maɗaukakin sarki, yakan yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya ribaci waɗannan kwanukan ta hanyar aikata kyawawan aiyuka nagari, da kuma kamewa daga munanan aiyuka na banza, lallai yin hakan yana samarwa da bawa yardar ubangijinsa da kuma amincinsa"
-
"Kayi ƙoƙarin ribatarsu kaima, ta yadda zaka kasance masu yin ƙoƙari wajen neman yardar Allah buwayi da ƙara kusanci zuwa gareshi"
-
"Haƙiƙa Sa'eed Bin Jubair Allah ya ƙara masa yarda, ya kasance idan kwanaki goman farkon watan zul-hijjah s**a shiga, yana yin jihadi jihadi mai tsanani (wajen bautar Allah da biyayya gareshi da dukkanin dangogin aiyukan ɗa'a ga Allah acikinsu) hatta ma har irin abinda ya kasance baya iya yin irinsa, (hatta irin abinda yake gagararsa aikata shi, to ya kasance yana aikata shi acikin waɗannan kwanakin koda kuwa cikin wahala ne domin neman kusanci da Allah mahaliccinsa)"
سنن الدارمي: (41
23/05/2025
Saura kiris
GOMAN FARKON DHUL HIJJAH
-
"Kwanaki goman farko na zul hijja kwanaki ne masu matuƙar falala da daraja a gurin Allah madaukakin sarki, wanda Allah ta'ala yake son aiyukan bayinsa a cikinsu kuma yake basu lada mai matuƙar yawa"
-
"Kada kayi wasa da waɗannan kwanakin, domin haƙiƙa kwanaki ne da babu irinsu, yawaita ambaton Allah a cikinsu yana ɗaukaka darajar bawa"
_Zaku iya biyomu a_
TELEGRAM CHANNEL 👇
https://t.me/QAIMATUL_UQALA_islamic_reminder
FACEBOOK 👇
https://www.facebook.com/share/18iRJyHxdA/
INSTAGRAM 👇
https://www.instagram.com/qa_imatu_uqala?igsh=dzJreWpxMm9xcTRz
WHATSAPP CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VapBzDFG8l5Fbj6pDU13
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Kano