26/09/2025
KA JI RABO: Kano Muna Fama Da Matsalar Yan Daba Da Rashin tsaro, Muna Kira Ga Gwamnatin Kano kada ta gayyato wata rigimar Daban wato Ta Addini.
Son a k**a Malam Lawan Triumph da wasu ke yi ba abu ne mai kyau ba, wannan sa'insar tsakanin mu da yan Darika da yan Bidia ba yau muka fara.
Abu ne wanda dama can ana yi dan haka muke fadawa Gwamnati datai kokari ta cire hannun ta kan wannan magana idan abu yazo na Addini a bari hujja tai aiki.
Bama so Gwamnati ta janyo wata fitinar bayan wacce muke ciki, shi isa muke rokon Gwamnatin Kano ta janye hannun ta kan lamarin Malam Lawan Triumph
~ inji Sheikh Abdallah Gadon Kaya
26/09/2025
Duk wani mai cikakken hankali yasan cewa,Allah bai taba halittar wani abu mai daraja da matsayi k**ar Annabi Muhammad SAW ba, shugaban halittun Allah, macecin alโumma a ranar alkiyama.
Haka nan babu wata halittar Allah data daidaitu wajen kyau da tsarin halitta k**arsa, Amincin Allah a gareshi da ahalinsa da masu binsa da biyayya har ranar sak**ako, wannan bama malamin addini ba, ko jahilin da biyi karatu ba yasan haka.
Matsalar Kano ta Kungiyanci ne, tare da banbancin akidu, Gami da banbancin malamai da kuma siyasa, wacce takeson game kowanne fanni na rayuwar yau da kullum.
Tabbas karatuka kowa da irin fahimtarsa, don haka maganar kace wai a hada kai hmmm wannan zancen banza ne, tunda can ada kai bai hadu ba sai yanzu?, kuma akan Wacce akida kake so a hada kan?, ba Gwamna ko menene matsayin mutum bazai samar da wannan hadin kan ba wallahi.
Abu daya ne zaiyi wannan abu, shi ne a koma kan karantarwar Allah da Manzonsa, abar maganar kowanne mutum a dauki ta Allah da manzonsa, abar fahimtar kowa a dauki ayoyin Allah da hadisan manzonsa ingantattu, daga wannan lokaci hadin kai zai samu.
Baโa addini da alโada ko hasashen wani, ana addini ne tsantsa da fadar Allah da umarninsa, kuma sakon Allah daya ne tunda aka kafa duniya ๐๐ป ููููููุฏู ุจูุนูุซูููุง ููู ููููู ุฃูู
ููุฉู ุฑููุณููููุง ุฃููู ุงุนูุจูุฏููุง ุงูููููู ููุงุฌูุชูููุจููุง ุงูุทููุงุบููุชู
Amma tayaya zaโabar mutane sakaka, kowa yana magana akan addini, wanda suke da ilimi da jahilai, mawaka jahilai marasa kan gado masu amfani da kalmomin kafirci sun cika alโumma, Malamai marasa hikima da azanci kowa ya hau munbari ko asaka masa Camera ya hau bada fatawa, kowa yaci ya koshi sai ya hau media yayi magana akan addini, batare da sun sanya littafi gaban malamai ba.
Wani ma Quotes zai kwafo a google saiya dora tambihinsa kai kace yasan inganci abinda ya karanta, lallai yak**ata a samar โSHURAโ committee marasa son zuciya su dunga duba ga lamarin kowa.
Amma wallahi idan akace zaโa zura idanu kowa ya fadi magana akan Allah, ko akan Annabinsa ko sahabbansa ko wannan addinin da muke tak**a, to tabbas watarana fitina zata bulla irin wadda bazamu iya kareta ba.
Bazance nafi kowa sani ko nafi kowa hankali ba, amma gaskiya magana anan itace abinda ke hada kan mutane shi ne ayi riko da igiyar Allah. ููุงุนูุชูุตูู
ููุง ุจูุญูุจููู ุงูููููู ุฌูู
ููุนูุง ููููุง ุชูููุฑููููู
Idan akai riko da cikakken Tauhidi da biyayya ga manzon Allah wallahi zaโa samu hadin kai tsakanin musulmi, amma duk hadin kan daba akan Tauhidi akayi shi ba, wallahi shirmen banza ne kawai da bata lokaciโฆ
Mugayawa kanmu gaskiya, duk wani son zuciya da banbancin akida mu ajiye shi mubi Allah da Annabin daya aiko mana, domin su kadai ne abinda zaโa tambayemu a kiyama..
Babu mai tambayarka malaminka, ko shehunka, ko wani waliyinka, ko akidar da suke akai..
Malaminka, waliyinka, shehunka, zai maka amfani ne idan ya doraka akan tafarkin Allah na gaskiya, sabanin haka kuwa babu abinda zai amfana maka a lahira.
ููููู
ู ููุง ูููููุนู ู
ูุงูู ููููุง ุจูููููู
ุฅููููุง ู
ููู ุฃูุชูู ุงูููููู ุจูููููุจู ุณููููู
ู
26/09/2025
KAJI RABO: Shekara 15 Baya fa Kasurgumin ฦan Bidi,a ne Allah Ne ya ganar dani Gaskiya ta Hanyar Sauraron Karatutukan Sheikh Jaafar mahamud Adam da yanzu Kodai nazama Boka ko babban mushriki -cewar Muhd King Cash
Me zaku ce?
Kana Son Duba Sahihan Labarai Shigo Jaridar ๐ Wakiliya ๐ Yanzu Yi Following Karku Bari Komai Ya Wuceku
05/06/2025
Ya Allah duk wanda yake da burin zuwa wannan wuri Allah Ka kai shi. Wadanda s**a je kuma Allah Ka mayar da su. Wadanda suke can a yanzu haka kuma Allah Ka karbi ibadarsu, da tamu baki daya.