21/02/2025
📢 Muhimmiyar Sanarwa! Karatun Halqa (Tsarin Haddar Al-Kur’ani A Karshen Mako) Ya Dawo!
Zuwa ga Iyaye Da Jama’ar Gari,
Mu na farin cikin sanar da ku cewa Karatun Halqa zai ci gaba bayan kammala cikakkun shirye-shirye ta hanyar inganta manhajin karatu, da gyara ajujuwa da dakunan kwana da kuma sabon shiri na musamman domin ingataccen koyo da koyarwa! 🌟📖
Ita Halqa wata kwarya-kwaryar makarantar kwana ce ta dalibai yan shekaru 10 zuwa 16 da aka tsara ta don haddar Al-Kur’ani. Tsarinta ya na ba dalibai damar zuwa makarantun boko a kwanakin sati sannan su karkata kacokam zuwa ga haddar Al-Kur’ani a karshen sati tare da mu. 🌙
📅 Tsarin Lokuta:
🕑 Lokacin Zuwa: Juma’a, da misalin karfe 2:00 n. r.
🏡 Lokacin Tafiya Gida: Lahadi, da misalin karfe 6:00 n. y.
📢 Tini an fara yin rijista! Iyaye za su iya samun fom din neman shiga a makarantar Zamzam Islamic College, Kano.
🎯 Zai yi kyau a hanzarta wajen cin ribar watan Ramadan! Ku sa yaranku domin su ci moriyar wannan babbar damar kuma a cikin wannan watan mai alfarma.
📥 Don neman karin bayani, ku sauke daftarin tsare-tsarenmu ta nan:
https://drive.google.com/file/d/1cElAbsbtlUpgWDlAWLc4MoVm9USydcHG/view?usp=drive_link
Email: [email protected]
📞 Kira/WhatsApp: 08065736302, 08039244754, 08038504436
Ku zo mu hada hannu wajen gina Hafizai da Malaman gobe! 🏫✨
Jazakumullahu Khairan! 🙌