Mai Tafsiri Kurmawa TV

Mai Tafsiri Kurmawa TV Karatuttukan maulana sayyadi basheer sheikh Ibrahim Mai tafsiri kurmawa kano

Dawowa Karatukan zawiyya Alhamis 1 Oct 2026
26/09/2026

Dawowa Karatukan zawiyya Alhamis 1 Oct 2026

25/09/2026
  Maitafsiri Kurmawa/muna Gayyatar kowa da kowa
22/09/2026

Maitafsiri Kurmawa/muna Gayyatar kowa da kowa

TARIHIN KHALIFA SHEIKH GHALI BN SHEIKH YAHUZA ZARIAKhalifa Sheikh Ghali bn Sheikh Yahuza Zaria an haife shi a Anguwar Li...
17/09/2026

TARIHIN KHALIFA SHEIKH GHALI BN SHEIKH YAHUZA ZARIA

Khalifa Sheikh Ghali bn Sheikh Yahuza Zaria an haife shi a Anguwar Limanci Iya, cikin Birnin Zaria, a shekarar 1926. Ya rayu kusan shekaru 100, kuma ya yi shekaru 43 yana Khalifanci, yana koyar da Tarbiyya ga dubban Muridai da Almajirai.

Shi ne na biyar cikin ’ya’yan Sheikh Yahuza Zaria da s**a zama Khalifofi:

1. Khalifa Sheikh Sani
2. Khalifa Sheikh Salisu
3. Khalifa Sheikh Surajo
4. Khalifa Sheikh Mukhtar
5. Khalifa Sheikh Ghali

KARATUN KHALIFA SHEIKH GHALI DA FARKON TARBİYYARSA

Sheikh Yahuza Zaria ya fara tura Khalifa Sheikh Ghali tare da Sheikh Mahmudu Kubau zuwa makarantar Allo domin karatun Alƙur’ani. A can ne s**a fara koyon Alƙur’ani tare da yin sauka.

Daga baya, tun yana da shekaru 15, Khalifa Sheik Ghali ya haddace Alƙur’ani a wajen Sheik Malam Rabi’u Dantude na Kano, wanda ya kasance aminin Sheikh Yahuza Zaria A wannan makaranta ne ya yi karatun Alƙur’ani tare da abokinsa Khalifa Ishaq Rabi’u Kano.

Bayan sun kammala haɗa Alƙur’ani, Sheik Malam Rabi’u Dantude ya ƙaddamar da shi cikin Darikar Tijjaniyya Daga nan ne tafiyar ilimi da Tarbiyyarsa ta ci gaba.

Khalifa Sheik Ghali ya samu ilimin Addini mai zurfi da Tarbiyya a wajen mahaifinsa, Sheik Yahuza Zaria Ya yi Tarbiyyatul Azkar da sauran ilimin Tarbiyya a wajensa Mahaifisa.

Bayan rasuwar Sheikh Yahuza Zaria a shekarar 1956, Khalifa Sheikh Ghali ya koma ƙarƙashin babban ɗan Sheikh Yahuza, wato Khalifa Sheikh Salisu bn Sheikh Yahuza Zaria, wanda shi ne mahaifin Khalifa na yanzu, Sheikh Sa’adu Salisu Yahuza.

Haka kuma, Khalifa Sheik Ghali ya haɗu da manyan Khalifofi da malamai, inda ya samu ilimi, Tarbiyya da ijazojin karatu, sirruka da izinoni cikin Darikar Tijjaniyya

MAZAN DA S**A BA KHALIFA SHEIKH GHALI IZININ ƘADDAMARWA CIKIN DARIKAR TIJJANIYYA

Khalifa Sheikh Ghali bn Sheikh Yahuza Zaria ya samu izinin ƙaddamar da mutane cikin Darikar Tijjaniyya daga manyan malamai da magabata.

Daga cikin waɗanda s**a ba shi wannan izini akwai:

1. Sheikh Malam Rabi’u Dantude Kano
2. Imam Sheikh Hassan Sise
3. Sheikh Hassan Dim
4. Khalifa Sheikh Mukhtar bn Sheikh Yahuza Zaria

Wannan izini ya ba Khalifa Sheikh Ghali damar ci gaba da hidimar Darikar Tijjaniyya, musamman wajen ƙaddamar da Muridai, koyar da Tarbiyya da Azkar.

TAFIYAR SHEIKH YAHUZA ZARIA ZUWA KHAULAHA

A shekarar 1948, Sheikh Yahuza Zaria ya tafi Khaulaha wajen Sheikh Ibrahim Inyass, tare da ’ya’yansa guda huɗu.

Manyan ’ya’yansa biyu su ne Sheikh Muhammad Sani, Khalifa na farko, da Sheikh Yusuf.

Ƙananan ’ya’yansa biyu kuma su ne Khalifa Sheikh Ghali da Sheikh Mujitafa bn Sheikh Yahuza Zaria.

Sheikh Yahuza Zaria ya yi kwanaki 101 a Khaulaha.

An ruwaito cewa Sheikh Yahuza Zaria ya samu wani irin kashafi, inda ya fahimci cewa manyan ’ya’yansa biyu ba za su yi tsawon rai ba, yayin da ƙananan ’ya’yansa biyu, Khalifa Sheikh Ghali da Sheikh Mujitafa, za su yi tsawon rai.

Bayan Sheikh Yahuza ya shiga Tarbiyya a wajen Shehu Ibrahim Inyass, Shehu ya wakilta Sayyadi Aliyu Sise domin ya kula da shi.

An ruwaito cewa Sayyadi Aliyu Sise ya ce:

«“Da ba don Sheikh Yahuza ya yi Tarbiyya a hannun Shehu Ibrahim Inyass ba, irin wannan yanayin da aka shiga, da babu wanda zai iya dawo da shi.”»

SHEIKH IBRAHIM INYASS YA BA KHALIFA SHEIKH GHALI DA SHEIKH MUJITAFA DARIKAR TIJJANIYYA A KHAULAHA

A shekarar 1948, Khalifa Sheikh Ghali da ɗan uwansa Sheikh Mujitafa bn Sheikh Yahuza Zaria sun je wajen Shehu Ibrahim Inyass tare da mahaifinsu, Sheikh Yahuza Zaria, domin a ba su Darikar Tijjaniyya.

Sai Shehu Ibrahim Inyass ya ce su dawo bayan kwana uku, domin shi da kansa zai ba su Darikar.

Bayan kwana uku s**a dawo. Bayan an kammala Wazifa, Shehu Ibrahim Inyass ya tambaya:

“Ina ɗan yayana na Zaria?”

Sai Shehu ya bayyana cewa dalilin da ya sa bai ba su Darikar a ranar da s**a zo shi ne, Sheikh Tijjani ne zai ba su da kansa.

Sai aka bayyana cewa a daren da ya gabata, Sheikh Tijjani ya zo wa Shehu Ibrahim Inyass, ya ba shi izinin ya ba su Darikar, daga Manzon Allah ﷺ.

KHALIFANCIN SHEIKH GHALI

Khalifa Sheikh Ghali ya yi shekaru 43 yana Khalifanci, yana koyar da Tarbiyya ga dubban Muridai da Almajirai, tare da ci gaba da hidima ga Darikar Tijjaniyya da koyar da abin da ya gada daga malamansa da magabatansa.

Ya kasance cikin ’ya’yan Sheikh Yahuza Zaria waɗanda s**a ɗauki nauyin ci gaba da ilimi, Tarbiyya da hidimar Muridai bayan rasuwar mahaifinsu.

Allah Ya jiƙan Sheikh Yahuza Zaria da Khalifa Sheikh Ghali. Allah Ya ƙara ɗaukaka darajar malamai da magabata, Ya sa mu amfana da iliminsu. Amin.

13/09/2026

Maulidin mai babban suna

07/09/2026

Kaitsaye daga kankarofi kano diwanin maulidi

03/09/2026

Kamar yadda aka bukata Gashi nan Allah yamaimaitamana yakara wa khalifa lafiya Alfarmar shehu Tijjani R'a

01/09/2026

Address

Kano
Kano
700101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mai Tafsiri Kurmawa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share