05/01/2026
Bayan kammala Addu’o’in da muka gudanar na Saukar Al-Qur’ani Mai Girma guda 21, mun ci gaba da gudanar da Addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, ci gaba da albarka ga ƙasarmu Najeriya, jiharmu Kano, da Maimartaba Sarkin Gaya da Kuma Masarautarmu, sannan da dukkan masoyanmu da al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Haka nan, a wannan lokaci mai albarka, mun ƙara kebance addu’a ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, shugaba nagari, mai kishin al’umma, kuma jagora mai hangen nesa. Mun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya shige masa gaba a dukkan al’amuransa, Ya ƙara masa hikima, juriyar shugabanci, da ikon gudanar da al’amuran jama’a bisa gaskiya da adalci.
Mun kuma yi masa addu’ar cewa Allah Ya ƙara taimakonsa, Ya ƙarfafa masa guiwa, Ya tsare shi daga sharrin ma hassada tare da roƙon Allah Ya maimaita masa wannan kujerar, domin mu ci gaba da amfana da nagartaccen shugabancinsa, ayyukansa na alheri, da manufofinsa na bunƙasa rayuwar al’umma wanda Mu Yan Gaya ganau ne.
Muna roƙon Allah Ya sanya mulkinsa ya zamo na albarka, ya kasance ginshiƙin zaman lafiya, ci gaba da haɗin kai, kuma ya bar tarihi na alheri da za a riƙa tunawa da shi har bayan mulkinsa.
Allah Ya kare Kano, Ya ɗaukaka shugabanninmu nagari, Ya kuma sanya mu a cikin masu yi wa ƙasa addu’a da aiki na gaskiya. Ameen.
Sarkin Malaman Gaya.