Rijiyar Sunnah

Rijiyar Sunnah

Share

To contribute with the little knowledge we have in propagating the islamic religion

22/04/2026

Thank you for being a top contributor and making it onto my weekly engagement list! Masoyin Zatee, Khadijah Yahaya Muhammad, Hudu Umar, Babangida Abubakar Saulawa 🎉 Masoyin Zatee Khadijah Yahaya Muhammad Hudu Umar Babangida Abubakar Saulawa

12/04/2026

🌍🇳🇬🤍 MUSULMAI DA KIRISTOCI… 🕌⛪

BA FA ABOKAN GABA BANE… ABOKAN RAYUWA NE 🤝🌿

---

💭🌙🧠

Wani lokacin…
Abinda muke gani a zahiri ba shi ne gaskiyar da ke ɓoye a ciki ba…

Ana ƙoƙarin raba mu da sunayen addinai…
Ana ƙoƙarin saka mana tsoro da ƙiyayya…

Amma a gaskiya…

👉 dukkan mu muna numfashi iri ɗaya ne
👉 dukkan mu muna jin zafi iri ɗaya ne
👉 dukkan mu muna kuka idan an cutar da mu 😢💔

Humanity first… before identity... 🌍🤍

---

🔥💡🧠

Masu hikima sun ce:

👉 “Idan mutane s**a fahimci abinda ke haɗa su, za su manta da abinda ke raba su...”

Saboda haka…

👉 Ba addini ne matsalar ba… ❌
👉 Ba kabila ce matsalar ba… ❌

👉 Rashin fahimta ne… da rashin adalci… da son zuciya ⚖️💔

---

🌿🤝✨

Ya ku ‘yan uwa…❤️🙏

Lokaci yayi da zamu canza tunani (mindset shift) 💡

👉 Daga “ni da kai”
👉 Zuwa “mu gaba ɗaya” 🤝

Domin ƙasa tana rushewa ne idan mutanenta sun rabu…
Ammah tana ƙarfi ne idan zukata sun haɗu… 🏗️🇳🇬

---

💔🩸😢

Kullum ana rasa rayuka…
ba wai saboda dole ba…

👉 Sai don saboda ƙiyayya da aka gina a zukatan mu

👉 da labaran da aka yarda da su ba tare da bincike ba

👉 Ignorance is expensive… it costs lives. ⚠️💔

---

📖✨

Allah Maɗaukaki Ya ce:

➡️ “Yā ayyuhan-nāsu innā khalaqnākum min dhakarin wa unthā wa ja‘alnākum shu‘ūban wa qabā’ila lita‘ārafū…”
(Al-Ḥujurāt 49:13)

👉 An halicce mu ne domin mu san juna…
ba domin mu cutar da juna ba… 🤝🌿

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

---

🕊️🌙🤍

Mu tambayi kan mu da kan mu…

👉 Idan aka kashe mutum… wane addini ne yayi nasara...? ❓

👉 Idan jini ya zuba… wane bangare ne yayi galaba...? ❓

Amsar ita ce…

👉 Babu wanda yayi nasara… dukkan mu mun yi asara ne... 💔

---

⚖️🧠✨

Saboda haka…

👉 Ka zama mai adalci…
👉 Ka zama mai sauraro…
👉 Ka zama mai fahimta…

Be a bridge… not a barrier... 🌉🤝

---

🤲🌿🇳🇬

ADDU’A:

Ya Allah…

👉 Ka cire ƙiyayya daga zukatanmu… 🤍
👉 Ka ba mu fahimta da hikima… 🧠
👉 Ka dawo mana da zaman lafiya mai dorewa… 🕊️

Domin…

👉 Najeriya gida ɗaya ce… 🇳🇬
👉 Kumah mu ne ginshiƙinta… 🤝✊

---

🌍✨🤍

Idan muka gyara zukatan mu… duniya zata gyaru...💎🌿

Bilalsadasub
Cpt. P'cross Recto

🤝🇳🇬✨

Photos from Rijiyar Sunnah's post 10/04/2026

😥 DAZU MUNJE MAKABARTA… AMMA ABIN DA MUKA JI YA GIRGIZA ZUCIYA!

Dazu munje makabarta domin binne matar kawuna… 💔(wadda ta rasu sanadiyar haihuwa😭


Amma a cikin wannan yanayi… sai wani abu ya faru.

Mai kula da makabartar malam AUDI ya kalle mu, cikin damuwa ya ce:

> “Yan siyasa na ta rabon kyaututtuka… amma mu da muke hidimar ƙarshe ga al’umma, ba wanda ya taɓa tunawa da mu… Ina yan media su ɗaukemu muma su watsa…”

😳 WALLAHI magana ta tsaya min a rai!

👉 Ka tsaya ka yi tunani:
Waɗanne mutane ne suke yi mana hidima ba tare da hayaniya ba?

✔️ Su ne suke haƙa kabari… ko da dare ne 🌙
✔️ Ko da ruwan sama na zuba 🌧️
✔️ Ko da babu kowa, su suke nan suna aiki
✔️ Su ke tsaftace makabarta, su cire ciyawa 🌿
✔️ Su ke tabbatar da an binne mutum cikin mutunci

❗ Amma su fa?
Waye yake tuna su?

Ba su da wata jam’iyya
Ba su da wani ɗan siyasa da zai tallata su
Ba sa zuwa wajen neman alfarma

💔 Sun sadaukar da rayuwarsu… amma ana kallon su kamar ba komai bane.

👉 Abin da ya fi bani tausayi ma…
na san dai kungiyar “Come To Sabon Gari” ta taɓa karrama su 👏
Wannan yana nuna cewa akwai masu ganin ƙimarsu… amma har yanzu ba a kai ga inda ya kamata ba!

👉 A wasu wurare ma, wallahi ana biyansu albashi na wata-wata!
Amma a wasu guraren… babu komai sai juriya da hakuri 😢

🙄 Shin don ba ‘yan siyasa bane yasa ba a ganin darajarsu?

🔥 SAKON ZUCIYA:

Ya kamata daga kansila Zubairu Lawal zuwa ciyaman Albany Jameel Abubakar
zuwa ɗan majalisa Sadiq Ango Abdullahi
Dana jaha nasiru idi kano
su duba wannan al’amari.

📢 Ku daina rabon abin duniya ga waɗanda zasu kaɗa kuri’a kawai…
Ku fara tuna waɗanda ke yi wa al’umma hidima har bayan mutuwa!

❓ TAMBAYA:

Shin a ganinka… waɗannan mutane basu cancanci kulawa da tallafi daga gwamnati da ‘yan siyasa ba?

Ko sai lokacin da aka binne mutum naka ne zaka gane darajarsu?


BabaSadiq dan Allah atayamu Mika sakonnan

07/04/2026

🌑⚰️😭 RAYUWAR KABARI – ⚰️🌑😭

---

⚰️🌌💀 RAMIN KABARI… 💀🌌⚰️

Rami ne mai duhu… 🌑
Rami ne mai tsananin matsi… 🤯
Rami ne mai firgici… 😨
Rami ne da babu wata mafaka sai rahamar Allah… 🤲😭

A nan ne za'a rufe ka… ⚰️
A nan ne za'a barka daga kai sai halin ka… 😢
A nan ne zaka fara sabuwar rayuwa… 🌌😭

Ba tare da:
❌ gado
❌ katifa
❌ haske
❌ dangi koh
❌ aboki ba

Sai kai kadai… da ayyukanka… 💔⚖️😭

---

🔥💭 KA TUNA… 💭🔥

Wanda ka raka jiya… ⚰️
Da wanda ka raka yau… 😭
Ta yuwu Gobe… kai ne za'a raka… 😰

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” 🤲💔

---

🌑🐍🔥 AZABAR DA KE CIKI… 🔥🐍🌑

Akwai duhu mai tsanani… 🌑
Akwai matsi da zai matse ƙasusuwanka… 💀
Akwai mala’ikun azaba… 😡👼
Akwai macizai… 🐍🔥
Akwai kunamai… 🦂🔥

📖 Allah Ya ce:
➡️ “Wanda ya bijire wa ambatona, to rayuwarsa za ta kasance cikin tsanani.”
(📚 Surah Taha 20:124)

💥 Wannan tsananim ba'a duniya kawai yake ba… har cikin ramin kabari… 😭

---

⚰️😨 LOKACIN DA ZA'A BINNE KA… 😨⚰️

Za'a sauke ka cikin rami… ⚰️
Za'a lullube ka da ƙasa… 🪨
Za'a rufe ka gaba ɗaya… 🌑

Kana jin sautin tafiyar mutane suna barinka… 👣💔😭

A nan ne zaka gane cewa…
👉 Ka shiga wani stage da babu dawowa… 🚫

---

🕊️📖 MANZON ALLAH ﷺ YA CE:

➡️ “Kabari ko dai lambu ne daga cikin lambunan Aljannah, ko kuma rami ne daga cikin ramukan wuta.”
(📚 Tirmidhi)

😨🔥 Dole zai kasance lambun al-jannah gare ka… koh kumah ramin azaba…

Babu tsaka-tsakiya… ❗

---

💀⚖️ TAMBAYAR DA ZA'A YI MAKA… ⚖️💀

Mala’iku za su zo gare ka… 😨👼

Su tambaye ka:
❓ Wanene Ubangijinka?
❓ Menene addininka?
❓ Wanene Annabinka?

Idan ka kasa… 😭
Sai azaba ta fara… 🔥

---

😢💭 A WANNAN LOKACIN… 💭😢

❌ Uwa bazata iyaetaimakon ka ba
❌ Uba ba zai iya kare ka ba
❌ Kudi baza su ceci ka ba
❌ Abokai ba za su zo ba

👉 Kai kaɗai ne… da aikinka… ⚖️

---

🔥💔 FIRGICI MAI TSANANI… 💔🔥

Wasu za su yi ihu a kabari… 😭
Wasu za su nemi dawowa duniya… 😢
Wasu za su yi nadama mai tsanani… 💔

📖 Allah Ya ce:
➡️ 'Yan wuta zasu ce ya Ubangijina!
Ka dawo da ni duniya domin in aikata alheri…”
(📚 Surah Al-Mu’minun 23:99-100)

❌ Amma bazasu taba dawowa ba… ❗
😭 Sun tafi kenan na har abada 😭

---

🌿✨ AMMA GA MASU IMANI… ✨🌿

Kabari zai zama:
🌸 haske
🌸 natsuwa
🌸 lambu daga Aljannah

Mala’iku za su yi musu bushara… 🕊️

📖 Allah Ya ce:
➡️ “Lallai waɗanda s**a ce Ubangijinmu Allah ne sannan s**a tsaya tsayin daka, mala’iku suna sauka gare su…”
(📚 Fussilat 41:30)

---

💔🔥😭 YA KU FALLOWERS DINA… 🔥💔😭

Ku shirya… ⏳
Ku gyara ayyukanku… 🧎
Ku tuba kafin lokaci ya kure… 😭

Domin:
👉 Kabari ba wasa bane
👉 Kabari gaskiya ne
👉 Kabari makoma ce

---

🤲🌙 ADDU’A… 🌙🤲

Ya Allah… 🤲
Ka sa kabarinmu ya zama haske… ✨
Ka kare mu daga azabar kabari… 🔥
Ka yalwata mana kabarinmu… 🌿
Ka sa mu shiga Aljannah cikin sauki… 🕊️

Albarkacin Manzon Allah ﷺ 🤍

---

⚰️💭 KARSHE… 💭⚰️

Duk wanda ya san wannan gaskiyar…
kuma ya shirya mata…
👉 ya ci nasara… 🌿

Wanda ya yi sakaci…
👉 nadama ce kawai zata biyo baya… 💔

---

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
╭━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━╮
🔔🔥 TASHAR WHATSAPP DON FAƊAKARWA 🔥🔔
╰━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━╯

🌿✨ DA’AWAH • ILIMI • HIKIMA ✨🌿
📚💡 Ilimi • 🧠✨ Hikima
⏳⚰️ Tunatarwar Lahira • 🕌🌙 Sunnah

📌👉 Bimu anan kai tsaye.

MUNEERATO VOICE OF AREWA 🌟🖋️
⭐🧭 Jagoran Hikima • 💡✨ Tauraron Haske • 😊❤️ Farin Zuciya ⭐
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

07/04/2026

HADISIN MU NA YAU

Manzon Allah {ﷺ} ya ce: “Abubuwa uku, (3) idan mutum ya yi su da gaske gaskiya ne; kuma idan ya yi su da wasa gaskiya ne: Aure, saki, da dawo da mace (bayan saki).

[ƘARIN HASKE]
1. Ma’anar “جدُّهنّ جدٌّ، وهزلهنّ جدٌّ”:Wato, waɗannan abubuwa ba wasa ake yi da su ba, domin suna da hukunci na shari’a mai tsanani. Idan mutum ya faɗi su da wasa, to hukuncin shari’a zai tabbata.

2. (1) An-nikāḥ (Aure): Idan mutum ya kasance ya yi maganar aure tare da sharuddan shari’ah (waliyyi, shaidu, amincewa), ko da fa wasa ne, to aure ya tabbata. Ba a cewa “ina wasa kawai nake” bayan ya yi lafazin aure.

3. (2) At-ṭalāq (Saki): Idan mutum ya ce wa matarsa “na sake ki”, ko da wasa yake yi, saki ya tabbata.

4. (3) Ar-raj‘ah (Dawo da mace bayan saki):Idan mutum ya saki matarsa saki ɗaya ko biyu, Kuma sannan a lokacin iddarta ya ce “na dawo da ke”, ko da wasa yake, dawowa ta tabbata.

5. Manufar hadith ɗin:Musulmi ya kasance mai natsuwa da hankali wajen amfani da kalmomi da s**a shafi auratayya da saki, domin su na da matuƙar muhimmanci a shari’a. Wasanni, barkwanci, ko motsin rai ba su canza hukunci a cikin waɗannan abubuwa ba.

Ga darasin da za a ɗauka daga hadith ɗin biyu:
(1): Addu’ar farkon salla tana koyar da tsarkake kai da tawali‘u gaban Allah. (2): Aure, saki da dawo da mace ba wasa ake yi da su ba, domin suna da sakamako mai girma a shari’a. (3): Annabi 💓{ﷺ}💓 ya koyar da cewa kalma tana da nauyi, don haka fa musulmi ya kiyaye harshensa.

ALLAH YA DATAR DA MU DA FALALARSA
Yar Hajiya ✍️✍️

06/04/2026

HADISIN MU NA YAU

MANZON ALLAH {ﷺ} YACE:-- HAQIQA ALLAH YANA FUSHI DA AL'FASHA DA KUMA MAI BAIYANA ITA KANTA AL'FASHAR.

[QARIN HASKE]
WANNAN HADITH DIN YANA KARANTAR DA MU HARAMCIN AL'FASHA DA BAIYANA ITA ITA KAN TA AL'FASHAR A CIKIN SHARI'AR MU TA MUSULUNCI, TARE DA NUNI GA YADDA ALLAH YAKE FUSHI DA MAI BAIYANA AL'FASHAR DIN.

AL'FASHA SHINE YA QUNSHI AIKI NA BARNA WANDA YAKE HARAMTACCE A CIKIN SHARI'A
TA MUSULUNCI, TA HANYAR FURTA KALMAI NA BATSA, DA QAZAFI, SHAN GIYA, ZINA, DA KISAN KAI, DA SAURAN NAU'UKAN MIYAGUN AYYUKA WADANDA SUKE QAZANTATTU!!

DUK WANDA YAKE/TAKE BAIYANA SU A FILI TOH BABU SHAKKA WANNAN MUTUMIN SHI FASIQI NE IDAN MACE CE TOH ITA FASIQA CE SHINE HUKUNCIN SU A SHARI'AR MUSULUNCI
KUMA YA HALASTA A NISANCI ZAMA DA SU.

DUK WANDA YAKE BAIYANA AL'FASHA A FILI TOH IDAN NAMIJI NE BAI HALASTA MACE TA AURE SHI BA, IDAN MACE CE TAKE BAIYANA
AL'FASHA A FILI ITAMA BAI HALASTA A AURE TA BA, IDAN KUMA MUSULMI KO MUSULMA S**A YI WATSI DA HAKAN TOH SUN AIKATA
LAIFI A CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI.

SABODA HAKA YAKU ƴAN'UWANA MUSULMAI MAZA DA MATA MU NISANCI AIKATA WATAU DUKKAN NAU'IN SABON ALLAH WANDA YA YI HANI DA MU AIKATA, KIYAYE HAKAN SHINE SAMUN ZAMAN LAFIYA A DUNIYA DA LAHIRA,
AKASIN HAKAN TOH SHINE TASHIN HANKALI A CIKIN RAYUWAR MU TA DUNIYA DA LAHIRA!

ALLAH YA BAMU IKON KIYAYEWA, ALLAH YA DATAR DA MU DA FALALAR SA.

Yar Hajiya ✍️✍️

06/04/2026

Ina rantsema da Allah. Idan kazo da Gaskiya, sai mutane sun kira ka mayaudari,
Kai Har dukan manzon Allah anyi akan Gsky ﷺ 😔🙏

Photos from Rijiyar Sunnah's post 06/04/2026

Ƙungiyar Musulmi ta Jâma'atu Nasr!l Islam ta yi jana'izar membobin ta da aka kâ$he a harin Anguwan Rukuba dake Jos ta Arewa.

06/04/2026

Shin baka tunanin duk wanda ya karanta
zaka samu lada? Yaya kake tsammani idan kayi liking kayi comment sannan kayi sharing saboda Allah? to ga wannan Addu'an gareka, Allah ya yaɗa sunanka a Aljannah maɗaukakiya tare damu baki ɗaya.

06/11/2025

SHIN ZAN IYA YIN SALLAH DA TUFAFI MAI JANABA?

TAMBAYA TA 3140
********************
Assalamu alaikum. Mallam Inna da Tambaya, bayan na Samu janabah koma nayi taimama shin da'iya yin sallah da da tufafin da janabah ya sameni, ko sai na chanja, tufafin Kafin nayi sallah. Daga zaidu suleiman Maihakuri.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatulLah.

Da farko dai ya kamata ka san cewa ita dai taimama din nan ba fa ko yaushe mutum yake yinta idan yaga dama ba. A'a dole sai da dalili mai karfi wanda shari'a ta yarda dashi.

Daga cikin manyan dalilan dake halasta yin taimama akwai :

1. TSANANIN RASHIN RUWA : Ya zamto ka nemi ruwan iyakar kokarinka amma baka samu ba. Ko kuma kana da ruwan amma ka'dan ne. Idan kayi wanka ko alwala dashi ba zaka sami wanda zaka sha ba. Kuma babu wani ruwan awajen da kake.

2. TSORON FARUWAR JINYA : Idan ya zamto akwai ruwan amma ba zaka iya amfani dashi ba, saboda tsoron idan har kayi amfani dashi zaka iya kamuwa da wata jinya. Koda kuwa mura ce. Musamman idan ruwan mai tsananin sanyibne, kuma ana tsakiyar sanyin hunturu, kuma babu abin dumama ruwa awajenka, kuma kafin ka nemo abin dumamawar lokacin sallar zai iya ficewa.

3. TSORON QARUWAR WATA JINYAR DAKE TARE DAKAI KO MOTSAWARTA : Wanda je fama da wata jinyar dake da alaqahbda sanyi ko numfashi, misali kamar Pneumonia, Asthma, Sickle-cell Anemia, da duk wani ciwon dake da alaqah da numfashi kamar mura mai tsanani ko ciwon tari da makamantansu, idan janaba ta sameshi awajen da babu ruwan dumi, ko kuma akwai ruwan dumin amma duk da haka yana tsoron amfani dashi saboda yiwuwar motsawar wannan jonyar dake tare dashi, ko Qaruwarta ko jinkirin warkewarta, to ya halatta gareshi yayi taimama.

4. KUREWAR LOKACI : Kurewar lokaci tare da rashin ruwa shima dalili ne. Misali wanda ya farka a kurarren lokaci, kuma ya duba ya tabbatar da crwa gidansa babu ruwan da zai iya yin alwala ko wankan janaba, kuma kafin yaje ya samo ruwan har rana zata iya fitowa, to ya halatta gareshi yayi taimama yayi sallah.

5. TSORON WANI AZZLUMI : idan ka wayi gari da janaba kuma gudanka babu ruwa, kuma kana tsoron zuwa wajen da zaka samo ruwan saboda wasu azzaluman dake zaune awajen zasu iya chutar dakai, to ya halatta gareka kayi taimama kayi sallah.

Saboda wasu daga cikin dalilan nan shi yasa Malamai s**a ce, duk mutumin da yasan yana dauke da jinyar da bazai iya taba ruwan sanyi ba, to bai halatta gareshi ya sadu da iyalinsa ba, har sai ya tanadi ruwan dumi ko abinda za'a dumama ruwan dashi.

Ita taimama ana yinta ne adaidai wajen da za'ayi sallar. Ba'a matsawa daga wajen da aka yita koda da taku guda ne.. Wannan ita ce mash-huriyar magana a mazhabah. Kuma ba'a sallatar sallolin farilla biyu da taimama guda.

Eh zaka iya yin sallah da tufafin da janabar ta sameka acikinsu, mutukar dai kana da tabbacinka wanke wuraren da maniyyi ya ta'ba. Tunda akwai sabanin Malamai game da shin maniyyi najasa ne, ko juwa ba najasa bane?

To gara dai ka wanke duk wajen da maniyyin ya ta'ba domin fitar da kanka daga kokwanto.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (05/05/1446 06/11/2024).

EMAIL ADDRESS : [email protected]

30/08/2025

AZKAR GUDA BAKWAI (7) MAFI TSADAN GASKE GA RAYUWAR MUSULMI.

Sadakatul Jariya Lada Mai Gudana.

1- Mafificin ambaton Allah.

_Laa ilaha illallaahu wahdahu lā shariyka lahu lahul-mulku wa lahul hamdu wa huwa alā kulli shay'en Qadiyr_

2- Mafificin tasbihi

_Subhanallaahi wabihamdihi, adada khalQihi, waridā nafsihi, wazinata arshihi, wa midāda kalimatihi_

3- Mafificyar Addu'a

Rabbana ātina fiy-dduniyā hasanatan -wafil akhirati Hasanah, waQinā azabanNār_

4- Mafificin Istigfari

Allaahumma anta rabbiy lā ilaha illā anta khalaQ-taniy, wa'ana abduka, wa ana alā aHdika, wa-wa' dika masta-'da at, a-uzubika min sharri ma sana'atu, abū Ulaka bini'-matika ãlayya, wa-abu'u bizambiy, Fagfirliy fa-innahu Lā yagfiruz-Zunuba illa ant_

5- Mafificin neman kariya da tsari

Bismillaahilladziy Lā yadurru ma-asmihi shay'un fiyl-ardhi walā fiys-Samā' , wa huwas samiy'un alaiym_

6- Mafificin zikirin neman yaye damuwa da bakin ciki

Lā ilaHa illa anta subhānaka inniy kuntu minaz-Zālimiyn_

7- Mafi zikirin dogaro ga Allah da sallamawa a gareshi

Lā haula wala Quwwata Illa billaahil aliyyil aziym_

Allah ya sa mu dace

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Kano City
Kano