SunnahOnline24

SunnahOnline24 Shafi Na Ilimi Da Wa’azi
Al-Qur’ani • Hadisi • Tunatarwa
Kano, Nigeria
Domin Yaɗa Sunnah Ka Follow domin samun fa’ida kullum.”

“Barka da zuwa SunnahOnline24 �
Shafi na musamman domin yada sahihin ilimin Musulunci, wa’azi, tunatarwa da karatun malamai cikin sauƙi da fahimta.

Abu Khaldatal Basary R.A yace :  Na sami mutane wadanda suke aiki ba tare da yawan magana ba, amma mutanan yau magana ka...
09/08/2026

Abu Khaldatal Basary R.A yace : Na sami mutane wadanda suke aiki ba tare da yawan magana ba, amma mutanan yau magana kawai suke yi ba tare da yin aiki ba.

Idan wannan saƙo ya amfane ka, ka taimaka wajen yaɗa shi domin wasu ma su amfana.
✅ Like • Comment • Share • Follow shafinmu.

09/08/2026
09/08/2026

Kada a manta, idan za'a kwanta bacci a dare a karanta:
1. Subhanallah - 33
2. Alhamdulillah - 33
3. Allahu Akbar - 34

Alhamdulillah! A jiya Asabar Baban Malamin Mu Sheikh Abubakar Salisu  Sharfadi ya kammala karantar da littafin Hakokin M...
09/08/2026

Alhamdulillah!

A jiya Asabar Baban Malamin Mu Sheikh Abubakar Salisu Sharfadi ya kammala karantar da littafin Hakokin Mata Akan Maza, wanda yake gabatarwa duk ranar Asabar bayan Sallar Magariba zuwa Isha’i a Masallacin Sheikh Ja’afar M Adam, Sharada. A cikin darussa 28.

Darasi ne mai matuƙar amfani kan haƙƙoƙin mata, kyakkyawar mu’amala tsakanin ma’aurata, soyayya, rahama, haƙuri, kyawawan ɗabi’u da yadda ya kamata musulmi ya gina gidansa bisa shiriyar Al-Qur’ani da Sunnah. Littafin ya kuma nuna mana cewa gyaran gida da zaman lafiya tsakanin ma’aurata na daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen gyaran al’umma.

Manufar marubucin littafin ita ce ya taimaka wajen gyaran rayuwar aure da dawo da kyakkyawar mu’amala da koyarwar Annabi ﷺ a cikin gidajen Musulmi

Allah Ya sa abin da aka karanta ya zama sanadin gyaran gidajenmu da kyautata zamantakewarmu.
Insha Allah, daga Asabar mai zuwa za'a ci gaba da wani muhimmin littafi:التحصينات الإيمانية من المداخل الشيطانية na Sheikh Wahid bin Abdul-Salam Bali. Wannan littafi yana magana ne kan hanyoyin da shaidan yake bi wajen karkatar da mutum, da kuma irin kariyar imani da musulmi yake bukata domin kare kansa daga waswasin shaidan da dabarunsa. An riga an fara wannan littafi, kuma an gabatar da darussa 10 kafin a dakata; yanzu kuma lokaci ya yi da za a dawo a ci gaba daga inda aka tsaya.

Don haka, ɗalibai da masu kishin ilimi kada ku rasa wannan cigaba! Littafin ya shafi wani muhimmin al’amari da kowane musulmi yake bukatar fahimta, domin sanin makircin maƙiyi shi ne mataki na farko wajen kare kai daga cutarsa.

Mu kasance tare da Malam daga Asabar mai zuwa, domin mu ci gaba da neman ilimin da zai ƙara ƙarfafa imanimmu, ya gyara rayuwarmu, kuma ya taimaka mana wajen kare kanmu daga hanyoyin shaidan. Allah Ya sa mu amfana da ilimin da muke koya, Ya ba Malam lafiya da ikon ci gaba da wannan aiki na alheri. Amin.

Ishaq Shuaibu Ibrahim
SunnahOnline24

09/08/2026

Azumi Gobe Litinin Ga Wanda Allah Yabashi Iko

08/08/2026

Darasi Na Karshe

Cikin Littafin Lambunan Soyayya da Rahama daga Koyarwar Annabi ﷺ tare da Mata

Mai Taken Hakokin Mata Akan Maza

Tare Da Sheikh Abubakar Salisu Sharfadi

08/08/2026

Tsira da Amincin Allah Sukara Tabbata ga Fiyayen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasalam ♥️♥️

08/08/2026

Shin Ya Halatta Malaman Addini Su Shiga Siyasa?

Ku Ziyarci Shafin Mu Na YouTube Domin Kallon Cikakkiyar Khudubar 👇

youtu.be/Ajq4wnPMF14

07/08/2026

Kada ka taba yanke tsammani, ka koma ga Allah da gaskiya, zaka same shi mai yawan yafiya, Ko mai yawan zunubanka.

Address

Sharada
Kano
700211

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SunnahOnline24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to SunnahOnline24:

Shortcuts

Share