28/04/2026
ZUWA GA ƊAUKACIN MA'ABOTA WANNAN CIBIYA TA MUJAMMA'U ASHABILKAHFI WARRAQIM.
Assalamu alaikum.
Sakamakon sauye-sauye da ci gaba da aka samu dangane da shari'ar Maulanah Amirul wa'iziyna Hafizahullah, Malam yayi umarni a ƙara yiwa yan uwa tambihat kamar haka:-
1) Ƙara shagaltuwa da addu'a a kowanne lokaci, domin itace babban makamin da muke dashi, musamman ga lauyan da zai ci gaba da jagorantar 'case' ɗin, Allah yai riƙo da hannayensa ya haskaka ƙirjinsa ya tsayar da diga-digansa zuwa ga abinda yake daidai wanda zai zama silar kubutar Maulanah Amirul wa'iziyna daga wannan hali da ake ciki na zaluntarsa da take hakkokinsa da akai.
2) Da a ƙara kiyaye harshe kan maganganun da za'a dinga furtawa, (mun gani a baya yadda akai amfani da kalmomin wani aka hukunta Malam da abinda bai jiba bai gani ba, akai masa sauyin waje na gaggawa ba tare da shiri ba). Mu sani cewa a yanzu lamarin shari'ar Malam yana wata gaɓa da ba'a buƙatar yawaita maganganu ko yin sharhi kan duk abinda aka gani, b***e kalaman tunzuri ko ƙetare doka.
3) Aci gaba da tsayuwa kan doka da oda kamar yadda aka sanmu. Malam yana ƙara jadda cewa duk wani motsi ko furuci da yake nuni ga karya doka ko tada zaune tsaye ba daga gareshi ba ne, kuma baya goyan baya.
4) Kira na musamman ga mahukunta kan wajabcin tsayar da adalci kan yan ƙasa; Malam ya ja hankalin hukumomi kan su kalli rawar da yake takawa wajen bawa zaman lafiya gudunmawa a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, a duk lokacin da aka sami wani furuci ko motsi wanda ya saɓa da abinda yake kira kai, bai kamata wanda yai laifi daban ba, wanda za'a dorawa hukunci daban ba. Wannan ya saɓa da tsari na adalci.
Daga ƙarshe muna ƙara jaddada kira ga yan uwa, kada ayi sanya ko ƙasa a guiwa wajen ci gaba da yin addu'o'i na musamman bisa wannan lamari, domin kuwa haƙiƙa ana ganin haskensu.
©Majmu'atu Atba'ish Sheikh Abduljabbar Kabara (Hafizahullah).
MASAK 28/04/2026.
25/04/2026
Alhamdulillah!
Malam dai ya hannata case a hannun wannan lauya da Kotu ta bashi shawarar ya hannatawa mutum ne me Amana sai yan makaranta a shagala da ruwan Hasbunallahu wani'imal wakilu da cigaba da kaiwa Allah kuka.
25/04/2026
22/04/2026
GOBE MUHYIDDENI ZAI BAYYANA A KOTU.
Kamar yadda sanarwa ta fito a gidajen jaridu, an dawo da Maulanmu, Amirul Wa’izina, jihar Kano a yau 22/04/2026. Insha Allah, zai halarci zaman kotu a gobe.
Don haka, ana kira ga daukacin dalibai da masoyan Malam da su kasance cikin nutsuwa, su takaita surutai, su kuma shagala da lazumtar:
Hasbunallahu wa ni'imal Wakil
Ya Qahharu, Ya Jabbaru
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya karfafe shi, Ya ba shi nasara da gagarumin rinjaye, kuma Ya karya azzaluman da suke zaluntarsa. Allah Ya karbi koke-kokenmu.
حسبنا الله ونعم الوكيل
يَا قَهَّارُ يَا جَبَّارُ
20/04/2026
RAHOTON ZAMAN KOTU NA YAU LITININ 20/04/2026.
RAHOTON ZAMAN KOTU - SHARI’AR SHEIKH ABDULJABBAR
RANA: 20 ga Afrilu, 2026
WURI: Court of Appeal, Kano Division, Audu Bako Secretariat
TAƘAITACCEN BAYANI:
A ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026, kotu ta ci gaba da sauraron shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara kamar yadda aka tsara. Zaman ya ƙunshi muhimman matakai na shari’a, umarni daga kotu, da kuma bayyana damuwar kotu kan yadda ɓangaren Gwamnatin Jihar Kano (ofishin Kwamishinan Shari’ah) suke jan ƙafa wajen tafiyar da wannan shari’a.
MUHIMMAN ABUBUWAN DA S**A FARU:
1. Fara Zaman Kotu da Gabatar da Takarda
Da aka kira shari’ar: Usman Malam Hussaini ya miƙe a madadin kwamitin Shari’ar Sheikh Abduljabbar, wanda ya ƙunshi mutane 14, inda ya gabatar da wata takarda wacce Sheikh Abduljabbar Kabara ne ya rubuta domin a miƙa wa kotu.
Mai Jagorantar Shari’a (Presiding Justice) ya tambayi halin da mai appeal (Appellant) yake ciki da kuma inda yake. Hussaini ya bayyana masa cewa yana tsare a Gidan Gyaran Hali na Kuje kuma yana cikin ƙoshin lafiya.
2. Karɓar Takardar da Kotu Ta Yi:
Kotu ta amince da karɓar takardar domin nazari, tana mai nuna cewa saƙon na da muhimmanci ga shari’ar.
3. Kiran Shugaban Sashen Shari’a (HOD Litigation):
Ɗaya daga cikin alkalai (Presiding Justice) ya bayar da umarnin a kira Ibrahim, shugaban sashen shari’a (HOD Litigation) .
Bayan zuwansa, ya tabbatar wa kotu cewa an karɓi takardar Malam Abduljabbar kuma an yi mata rajista (filing). Sai dai ya kuma tabbatar da cewa ba a kawo wanda ake ƙara kotu ba.
4. Umarnin Kotu ga Ma’aikatar Shari’a:
Bisa wannan yanayi, kotu ta bayar da umarni a kira Darakta daga Ofishin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano domin ba da bayani.
5. Bayanin Abin da Takardar Ta Ƙunsa:
Kotu ta nemi a yi taƙaitaccen bayani kan abin da takardar ta ƙunsa. Hussaini ya miƙa wannan aikin ga Jilani Makwarari, wanda ya yi bayani a takaice cikin harshen Hausa.
6. Nazarin Takardar da Alƙalai S**a Yi:
Alƙalai sun ɗauki kusan mintuna biyar suna nazarin kwafin takardar da ke hannunsu. Bayan haka, sun umarci Hussaini da ya koma ya zauna, suna mai nuna cewa sun wadatu da kwafin da suke da shi.
7. Ɗan Dakatar da Shari’ar (Case Down):
Mai Jagorantar Shari’a ya bayyana cewa an “sauke” shari’ar na ɗan lokaci (the case is down), wato za a dakatar da ita na ɗan lokaci kafin a sake kiranta.
8. Sake Kiran Shari’ar:
Bayan kimanin awa biyu, kotu ta sake kiran shari’ar a matsayin ta takwas cikin jerin shari’o’in ranar.
Zahraddeen Kofar Mata daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ya miƙe, inda ya nemi afuwar kotu bisa jinkirin zuwansu. Ya kuma sanar da kotu cewa an miƙa shari’ar ga wani lauya mai zaman kansa (Private Lawyer).
9. Gargadin Kotu:
Mai Jagorantar Shari’a ya nuna rashin jin daɗi matuƙa kan yadda ake tafiyar da shari’ar, yana mai jaddada cewa wannan ba shari’a ce ta yau da kullum ba, don haka bai kamata a yi sakaci da ita ba.
10. Ƙin Amincewa da Buƙatar Ɗagawa:
Lokacin da aka tambaye shi abin da zai ce, wakilin Ma’aikatar Shari’a ya nemi a ɗaga shari’ar na tsawon mako guda. Nan take kotu ta ƙi wannan buƙata, tana mai nuna cewa an riga an samu jinkiri mai yawa.
HUKUNCI DA UMARNIN KOTU:
Bayan cikakken nazari, Mai Jagorantar Shari’a ya yanke hukunci kamar haka:
a) An ɗage shari’ar zuwa ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
b) Kotu ta umarci Lauyan Gwamnati ya halarci zama na gaba ba tare da ƙin halarta ba.
c) Kotu ta bayar da umarni ga Hukumar Gidan Ajiya da Gyaran Hali (Correctional Center) da su tabbatar an kawo Appellant, wato Sheikh Abduljabbar Kabara gaban wannan kotu a zama na gaba.
d) Kotu ta bayyana cewa Appellant shi ne zai gabatar Shari’arsa da kansa, kasancewar ba shi da lauya.
KAMMALAWA:
Zaman kotu na wannan rana ya nuna tsayin daka daga bangaren kotu wajen tabbatar da bin doka da tsari, da kuma kauce wa ƙarin jinkiri. Umarnin da aka bayar sun nuna ƙudurin kotu na ganin an tafiyar da shari’ar cikin gaskiya, da kuma tabbatar da halartar mai ƙara - Sheikh Abduljabbar (Appellant) domin ci gaba da shari’ar ba tare da tsaiko ba.
Wanda Ya Rubuta Rahoton:
Ɗan Jarida na Shari’a
20 ga Afrilu, 2026
20/04/2026
Yau kotun ɗaukaka kara zata zauna sauraren case din Sheikh Abduljabbar kabara (H).
13/04/2026
13/04/2026
TAKARDAR TUNI AKAN TAKARDA ME TAKEN "LETTER OF FURTHER COMPLAINT REGARDING THE APPEAL NO. CA/KN/01/2025. SUIT NO. K/93CA/2022. BETWEEN ABDULJABBAR SHEIKH NASIR KABARA— APPELLANT AND KANO STATE GOVERNMENT — RESPONDENT"
~Maulana Ameerul Wa'izeena (H)
13/04/2026
13/04/2026
A REMINDER CONCERNING THE LETTER ENTITLED "LETTER OF FURTHER COMPLAINT REGARDING THE APPEAL NO. CA/KN/01/2025. SUIT NO. K/93CA/2022. BETWEEN ABDULJABBAR SHEIKH NASIR — APPELLANT AND KANO STATE GOVERNMENT — RESPONDENT"
~Maulana Ameerul Wa'izeena (H)
07/04/2026
TAKARDAR KORAFI WADDA SHEIKH ABDULJABBAR KABARA YA RUBUTAWA 'COURT OF APPEAL KANO DIVISION' SAKAMAKON SAKON DA KOTUN TA BAYAR IZUWA GARESHI A WAYAR TARHO, TA BAKIN H.O.D NA KOTUN RANAR 31-03-2026.
KWAMATIN SHAIDU YA ISAR DA WANNAN TAKARDA A YAU TALATA 07-04-2026.
GA TAKARDAR KAMAR HAKA:-
04/04/2026
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un
Da izinin Maulana Amirul wa'izina muna mika ta'aziyya na rashin ɗaya daga zakakuran yan media na Ashabul-khafi wato Malam Sabi'u Saisabana Aljabbary ga uwa da iyalansa muna addu'ar Allah ya jikansa ya kyautata makoma ya bamu hakurin wannan rashi.
Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraqeem Nigeria.
4/4/2026.
27/03/2026
KARASHEN TAKARDAR ƊAUKAKA KORAFIN MAULANA AMEERUL WA'IZEENA (H), ZUWAGA CHIEF JUSTICE OF NIGERIA. PART (2).
https://www.facebook.com/share/p/18NSLjmpki/
27/03/2026
KARASHEN TAKARDAR ƊAUKAKA KORAFIN MAULANA AMEERUL WA'IZEENA (H), ZUWAGA CHIEF JUSTICE OF NIGERIA. PART (1).
https://www.facebook.com/share/p/18NSLjmpki/