08/04/2024
DOGARO DA ILIMIN FALAKI WAJEN TABBATAR DA GANIN WATA.
Babban Malamin nan Ash-Shaikh Bakar Abdullah Abu Zaid Allah Ya yi masa Rahama, cikin kyakykyawan littafin nan na sa wanda ya ke magana a kan sababbin mas'aloli a Addini, wato (فقه النوازل) Ya yi bayanai masu kyau, bayanai na ilimi, bayanai gamsassu, a kan sha'anin aminta da dogara da maganar masana ilimin falaki (Astronomy) wajen tabbatar da ganin Wata.
Malamin ya kai matuka wajen bayanin wannan mas'ala yadda ya kamata. A cikin bayanansa a wanann Littafi ya kawo misalai na irin yadda sau da yawa ake samun tasgaro da cikas da rashin tabbaci cikin bayanan masu wannan ilimi, inda ya nuna cewa maganganun masu ilimin falaki wajen tabbatar da ganin wata ba wasu maganganu ba ne tabbatattu yanke! Kuma Shari'ar Musulunci ba ta yi Umarni da a dogara a kansu kacokam ba! Ta yadda idan sun fadi abu, to shike nan ya zauna daram dam!!! Ya tabbata. Ya ce sau da yawa suna kore yiyuwar ganin wata, amma kuma sai a samu an gan shi a wasu kasashe daban-daban, ta hanyar amintattun mutane masu yawa. Wanda hakan ke nuna maganarsu ba Yakini ba ce, kuma za su iya fad'a a samu sabanin abin da s**a fad'a, sannan ba za a karyata amintattu ba a kan kawai bincikensu wanda zai iya zama daidai, zai iya zama kuskure, ko za a iya samun chanji daga bayan binciken na su.
Hakika yadda wannan Bajimin Malamin Duniya Shaikh Bakar Abu Zaid ya yi bayanin wannan mas'ala filla-filla ya kayatar da ni, maganganunsa akwai bincike da zurfin ilimi da nufatar daidai, Kuma wannan shi ne abin da ya kamata a rike a a matsayin abin lura a cikin wannan mas'ala.
Domin kuwa da ma wannan ita ce Matsayar daukacin malaman musulunci tun a baya, da kuma a yanzu, ba a zallar dogaro da maganar masana ilimin Falaki wajen lissafin ayyukan Ibada.
Kafin Sheikh Bakar Abu Zaid, shi ma Shaikhul Islam Ibn Taimiyya ya yi bayani mai fad'i a kan wannan mas'ala cikin "Majmu'ul Fatawa" Juz'insa na (25) haka nan Alhafiz Ibn Hajar a cikin "Fat'hul Bari" da kuma sauran ma'abota ilimi tun a zamunan baya.
Don haka cin fuska ne, azarbabi ne wani masanin ilimin Falaki (Astronomer) ya fito yana hakikance cewa dole Azumi (30) za a yi, yana mai jazami da tabbatar da cewa ala dole tilas ba zai tab'a yiyuwa a ga jinjirin watan Shawwal a ranar (29) ga Ramadan ba, duk wanda ya ganshi Karya ya ke! Duk wadanda s**a gan shi s**a yi Sallar Idi a washegari sun sha Azumin Ramadan, sun afka Zunubi! Wannan ba daidai ba ne! Kuma ba Yakini ba ne!
Asali a Shari'ar Musulunci shi ne duba na ido, kamar yadda Ayar Alkur'ani da Hadisan Annabi (S.A.W) s**a tabbatar. Don haka in dai amintattu s**a tabbatar da ganin wata, babu Hujjar da za ta sa a kore ganinsu ko a musanta shi saboda binciken wasu wanda ba Yakini ba ne. Lissafi ne, zai iya zama gaskiya, zai iya zama da kuskure a cikinsa. Haka nan idan aka biyewa wannan Kofa, to ana nan ma za a rufe batun gani da ido din kacokam! A koma kawai ga yan ilimin Hai'ah wajen duba wata.
Karin Bayani: Hikimar wannan Rubutu shi ne haskakawa domin komawa wadannan littafai da na ambata a ga mai malamai s**a yi bayani a kan wannan batu, sannan kuma a gurguje a wanke zukatan wasu daga rudanin da wadancan masanan ilimin falakin ke jefawa al'umma duk Shekara.
A karshe, muna tare da abin da Sarkin Musulmi ya yi umarni, muna bisa abin da sanarwarsa ta hukunta, kuma mu sani Sarkim Musulmi bai dogara da maganganun wadancan mutane ba kacokam! Domin idan da ya biye ta tasu, ya dogara da su, to ba ma za a umarci mutane su duba wata ba a yau Litinin (29) Ga Ramadan, kai tsaye za a fitar da sanarwa ne cewa Azumi (30) za a yi, yin Sallar Idi sai ranar Laraba kawai. Amma ga shi an fitar da sanarwar cewa al'umma su duba watansu a yau (29) ga Ramadan, daga nan kuma sai a bi matakai na tantancewa yadda aka saba. Allah Ya sa mu dace, Ya dora mu a kan abin da ya ke shi ne daidai.
Mai Rubutu:
Musa Muhammad Dankwano
29-Ramadan-1445
07/04/2024
30/10/2023