24/04/2026
Ahbabu Rasulullah Kumbotso
Gida ne Domin Tsantsar Masoya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Munayin Mauludi kuma Rera Yabo
24/04/2026
14/04/2026
Kamar yadda bazaka iya kamo rana da hannunka ba, haka nima bazaka iya kamo ni a Soyayyar Manzon Allah ba.
~Shiekh Ibrahim Inyass.
13/04/2026
Kaunar Annabi Alaihissalam idan muka sakata agaba duk abinda ya damemu Allah sai ya warware mana.
~Prof. Umar Sani Fagge.
13/04/2026
Duk wanda zai sawa dansa suna Muhammad sai ya kula wajen fadar sunan saboda sunan akwai daraja.
~Prof. Umar Sani Fagge
12/04/2026
Duk yadda kake da zafi kan akidarka, ka tsaya ka fahimci wannan karatun, kada malamanka su kai ka ga halaka.
Wasu sukan yi ƙarya su ce Shehu ya yi iƙirarin matsayin da ya wuce na ɗan adam ko kuma ya sanya kansa a matsayin da ya saba wa koyarwar Musulunci.
Akwai masu yi masa sharri suna cewa dukkan koyarwarsa bidi’a ce, alhali tushenta Alƙur’ani ne da Sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Sukan ɗauki sashen maganarsa su yanke ta yadda za ta ba da ma’ana mara kyau, domin kawai su ɓata masa suna a idon duniya.
Wasu sukan ƙirƙiri maganganu su jingina su gare shi, suna cewa daga littattafansa ne, alhali bai taɓa faɗar hakan ba, kuma ba ya cikin sahihan rubuce-rubucensa.
Wasu kuma sukan yi zargin cewa ya zo ne don raba kan Musulmi, alhali tarihin rayuwarsa duka kira ne zuwa ga haɗin kai da ƙaunar juna.
Suna ƙoƙarin siffanta shi da abubuwan ƙarya domin rage darajarsa a zukatan matasa da masu tasowa.
An yi masa ƙage kan matsayinsa, ba mu yafe ba.
An yanke maganganunsa domin a ɓata masa suna, Allah zai bi mana haƙƙinmu.
An ƙirƙiri ƙaryar cewa koyarwarsa bidi’a ce, alhali duka Sunna ce.
An jingina masa littattafan da bai rubuta ba domin a yaudari mutane.
An siffanta shi da raba kan al’umma, alhali shi jagoran haɗin kai ne.
Duk wanda ya ce zai toshe hasken Shehu da bakinsa, Allah zai kunyata shi.
11/04/2026
Duk wanda zai sawa dansa suna Muhammad sai ya kula wajen faɗar sunan saboda sunan akwai Daraja.
11/04/2026
Duk abin da mutum yake so a duniya, akwai ranar da zai rabu da shi. Amma soyayyar Manzon Allah (S.A.W) ita ce kaɗai jarabtar da take kai mutum ga babban rabo a duniya da lahira.
Kamar yadda Shehu (R.A) ya faɗa, kowa da abin da aka jarabce shi da so. Shin kai mene ne naka babban burin a rayuwa?
اللهم انك عفو تحب العفو فعف عنا
27/12/2025
Ga mutanenfa sun dakko karatu
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Kano