Inuwar Marayu Foundation

Inuwar Marayu Foundation

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Inuwar Marayu Foundation, Kano.

07/03/2025

Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu
An umarceni da na sanar daku cewar Inshaa Allah ranar Lahadi me zuwa, 9th Ramadan zaa gabatar da rabon abincin marayu na azumi kamar yadda aka saba. Don haka, ana ga dukkanin wakilan marayu da su sanar da iyayen marayu domin zuwa su amshi sadakar abincin marayunsu
2. Ana kira ga duk masu niyyar bada gudunmuwar su ta wannan aiki dasu bayar da abinda s**ayi niyya na kayan abinci ko kudi a account din qungiya dake Jaiz Bank PLC.
3. Za ayi wannan rabo ne a gidan su welfare officer
+234 803 115 1533⁩ kamar yanda aka saba at 10am.

SIGNED
Lawan Adamu Ismail
08064955053
Secretary General,
Inuwar Marayu Foundation.

08/09/2024

Assalamu alaikum,
Cikin shirye-shiryen komawar yara makarantun boko, ajiya gidauniyar inuwar marayu ta rabawa marayun ƙungiya litattafan karatu(text books)na matakan ajujuwan firamare, da matakan ajujuwan ƙarama da babbar sakandare tare da litattafan rubutu da fensira.
Fatan Allah ya sakawa kowa da alkhairi ya baiwa yaran ilimi mai amfani,amin.

PROII,
Inuwar Marayu Foundation.

05/04/2024

Assalamu Alaykum

Tallafin Ramadan na biyu a 1445H/2024

Ƙungiyar Inuwar Marayu Foundation za ta bawa Iyaye Mata TALLAFIN KUƊI kowaccen su In Sha Allah a madadin kowa na ƙungiya don samun Albarkar wannan wata na Ramadan mai Alfarma da kuma rage musu raɗaɗin hidindimun Azumi da Sallah akan Marayun mu. Za'a yi rabon kamar haka;

• Gida mai Maraya 1: ₦5, 000
• Gida mai Maraya 2 zuwa sama: ₦10, 000
• Rana: Lahadi, 7th April, 2024
• Lokaci: 11:00 am
• Wuri: Gidan su Musa Bobo (Welfare Officer), Dirmi, Kofar Naisa, Gwale LGA, Kano State.

1. Lallai kowacce Mahaifiyar ta zo da kan ta
2. Lallai ban da makara, don wannan karo ba za'a jira ba
3. Lallai a taho da PHOTOCOPY (ba original ba, don Allah) na sakamakon jarrabawar Marayu na Boko da Islamiyyah.

PRO II,
Inuwar Marayu Foundation.

Photos from Inuwar Marayu Foundation's post 10/03/2024

Masha Allah,

Rabon kayan Abinci ga Marayun ƙungiya. An bawa kowanne Maraya Shinkafa Kwano 2 da ₦1,000 Kuɗin Cefane.

Allah Ya sakawa kowa da Alkhairiy.

PRO II,
Inuwar Marayu Foundation.

09/03/2024

Assalamu Alaykum

Ciyarwar Ramadan

Ana gayyatar Marayun ƙungiya zuwa karɓar taimakon ciyarwar Ramadan daga ƙungiya.

• Rana: Lahadi, 10th March, 2024
• Lokaci: 11:00am
• Wuri: Gidan su Musa Bobo (Welfare Officer), Dirmi, Gwale LGA, Kano State.

Allah Ya sakawa duk wanda s**a bada gudunmawa da Alkhairiy Ya karɓa daga garemu baki ɗaya.

PRO II,
Inuwar Marayu Foundation.

28/08/2023

Assalāmu Alaykum,

𝙸𝙽𝚄𝚆𝙰𝚁 𝙼𝙰𝚁𝙰𝚈𝚄 𝙵𝙾𝚄𝙽𝙳𝙰𝚃𝙸𝙾𝙽

• Motto: Looking after Orphans and Vulnerable
• Objectives: Sponsoring, Education, Ramadan Feeding, Vocational Skills, Empowerment, Guidance & Counseling.

Year 1: 2017: 12 Donors
• 12 Male members
• 0 Beneficiaries.

Year 2: 2018: 42 Donors
• 39 Male members
• 3 Female members
• 22 Orphans and Vulnerable.

Year 3: 2019: 135 Donors + 3 Volunteers
• 95 Male members
• 40 Female members
• 63 Orphans and Vulnerable.

Year 4: 2020: 185 Donors + 3 Volunteers
• 112 Male members
• 73 Female members
• 63 Orphans and Vulnerable
• 2 Widows (Monetary assistance).

Year 5: 2021: 258 Donors + 3 Volunteers:
• 140 Male members
• 118 Female members
• 112 Orphans and Vulnerable
• 10 Widows (Monetary assistance).

Year 6: 2022: 212 Donors + 3 Volunteers:
• 117 Male members
• 95 Female members
• 114 Orphans and Vulnerable
• 10 Widows (To receive pasta or knitting machines as empowerment).

Year 7: 2023: 227 Donors
• 126 Male members
• 101 Female members
• 120 Orphans and Vulnerable
• 10 Widows (Empowered with Pasta machines & Flour).

Social Media:
• Facebook: Inuwar Marayu Foundation: https://www.facebook.com/Inuwar-Marayu-141638113222349
• WhatsApp: Inuwar Marayu Foundation; Inuwar Marayu EXCOs/Shura; Wakilan Inuwar Marayu.

Email: [email protected]

Monthly donations:
• Males: ≥₦500 per month
• Females: ≤₦250 per month.

Monthly/regular donations - Educational services (Buƙatun Makarantun Marāyu)
• Access Bank;
• Inuwar Marayu Foundation
• 0108600525.

Ramadan feeding, Sallah clothing, Health services, Vocational training, Empowerment, etc. (Ƙarfafar Marāyu da Iyayen su Mata)
• Jaiz Bank;
• Inuwar Marayu Foundation
• 0011741163.

JazākumULLĀHU-Khayran.

28th August, 2023,
12nd Safar, 1445H.

Inuwar Marāyu Foundation,
Kano State,
Nigeria.

Photos from Inuwar Marayu Foundation's post 08/04/2023

Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh. Alhamdulillah, Gidauniyar Inuwar Marayu Foundation ta raba tallafin abincin Azumi ga iyayen marayu kamar yadda aka sanar. Allah ya saka da Alkhairi ya karbu ayyukan mu, Amin.

PROII,
Inuwar marayu foundatuon.

02/04/2023

Assalāmu Alaykum,

Tallafin Abincin Ramadan ga Marayun Ƙungiya:

Inuwar Marāyu Foundation za ta rabawa Marāyun ƙungiya tallafin Abinci don ciyarwar Ramadan (wata mai Albarka).

• Rana: Asabar, 8th April 2023 (17th Ramadan 1444H),
• Wuri: Gidan su Musa BawBaw, Dirmi, Diso Quarters,
• Lokaci: 10:00 na Safe.

Ga masu niyyar taimakawa ta kowanne hali (kuɗi, kayan abinci, dss) ƙofa a buɗe take.

Ramadan feeding, Sallah clothing, Health services, Vocational training, Widows empowerment, etc:
• Jaiz Bank;
• Inuwar Marayu Foundation
• 0011741163.

JazakUMULAHU-Khayran.

PRO II,
Inuwar Marayu Foundation.

12/01/2023

Assalamu Alaykum,

Taron Rabawa Iyayen Marāyu Injin Taliya:

Inuwar Marayu Foundation za ta rabawa Iyaye Mata 10 na Marayun ƙungiya Injin Taliya guda 10 don fara sana'a da samun sauƙin kula da Marayun.

• Rana: Lahadi, 15th January 2023
• Wuri: Subulussalam Islamiyya,
• Lokaci: 11:30 na Safe

Rabbi Ya saka wa wanda ya bayar da Alkhairiy Ya karɓa daga garemu baki ɗaya.

Abdulhamid Dahiru Muhammad,
PROII,
Inuwar Marayu foundation.
12/01/2023.

25/12/2022

Assalāmu Alaykum,

Taron Ƙarshen Shekara: End of year meeting:

Rana: Litinin, 26th December 2022
Lokaci: 11am
Wuri: Office ɗin Safīnatul Khair Foundation, Ɗiso Qtrs, Gwale LGA, Kano State.

PROII,
Inuwar Marāyu Foundation

08/05/2022
03/05/2022

InnaLILLAHI_Wa'inna_ILAYHI_Raji'un..!!!

Inuwar Marāyu Foundation ta rasa ɗaya daga mutanen ta a Yau bayan ciwon ciki.

Allah Yai masa Rahama Ya sa ya huta. Kuma Insha-Allah ƙungiya za ta ɗau nauyin karatun Yaran sa guda 2 da ya bari (wancan satin akai masa haihuwa ta biyu ma).

Inuwar Marāyu Foundation has lost a member. May Allah grant him Jannatul Firdaus.

🤲🏼🤲🏼😢💐

PRO II,
Inuwar marayu foundation.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Culinary Team

Attire

Telephone

Website

Address

Kano