01/12/2023
As-salam Alaikum!!!
Akaro na biyu muna so Alumma su fahimci cewa, bawai muna kalubalantar wadda s**ai Wannan post bane, ko kuma nasarar da dalibanmu s**a samu bane, hasalima zamufi kowa farin ciki da wannan abun Alkairi,
Amma mu sani cewa wasu na ci da buguzun da sunan kungiyar dalibaine, domin lokacin da'aka kawo wannan form na wannan tsari, bamu sani ba, yawanci mutane basu sani ba, aka raba, agefe guda kuma wasu na zargin munyi yadda muke so, mu kuma alhalin ba mu sani ba,
Wannan tasa muka magantu, muke bada gyra cewa bamu san wannan al'amari ba,
Amma koma menene, wannan aikinmu ne aka taimaka mana wajen sanar da alumma, kawai rashin fahimatar da'akai mana shine ba wai muna kalubalantar ku bane, korafinmu anan shine, kawai anyi amfani da sunan NAGS ne batare da saninta ba wannan shine kawai,
Daga karshe muna masu bawa junanmu hakuri cewa rashin fahimta ne, da kuma kokarinmu na kaucewa zargin masu zargi ckn wannan al'amari,
NAGS akoda yaushe fatan mu shine samun kyakkyawan yanayi ga dalibai yan asalin karamar hukumar gaya, kuma ashirye muke da hada hannu da kowanne mutum ko kungiya wajen ganin anyi aiki tare don cigaban garinmu,
Allah ya taimaki daliban gaya, da kungiyar daliban ta gaya, gaya, jihar kano, da kasarmu baki daya,
Naku rabiu lukman,
Jami'n hulda da jama'a na kungiyar dalibai ta gaya NAGS national body.
Rabiu luqman Gaya
PRO I