Dawwama akan aikin alkhairi kashi na farko (1)
------------------------------------
Dukkan wanda Allah (S.W.T.) yai masa damkatar dayi masa biyayya da kuma aikata ayyukan alkhairi acikin wataran Ramadan haƙiƙa Allah ya datar dashi da mafi girman falala. Sai dai babban ƙakuban shi ne dawwama akan aikin.
Mutane da yawa su kanyi himma da zage damtse wajen ganin sun kyautata alaƙarsu da mahaliccinsu a watan Ramadan, amma da zarar watan ya wuce sai kaga sun koma gidan jiya, wasu su koma aikin ɓarna, wasu kuma su tsaya da aikata aikin alkahairan da s**a kasance suna aikata a Ramadan.
Annabi (S.A.W.) ya kasance yana koyar da sahabbansa tabbata da tsayuwa tsayin daka akan aikin alkhairi. Ya tabbata a hadisi, watarana Sufyan ibn Abdullah Assaƙafiy ya tambayi Annabi (S.A.W.) ya faɗa masa wani abu wanda zai zama ya tattara komai a sha'anin addini ta yadda ba zai ƙara tambayar wani bayan manzon Allah ba, sai Annabi (S.A.W.) ya ce masa: "Kayi imani da Allah, sannan ka dai-dai ta".
Abdullahi ibn Abbas (R.A.) ya kasance yana fassara faɗin Allah (S.W.T.) acikin Suratul Fussilãt (30).
إن الذين الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا تتنزل عليهم الملائكة ألا تخافوا ولا تحزنوا وأبشروا بالجنة التي كنتم توعدون.()
Cewa Ma'anar ayar, s**a tsaya tsayin daka wajen yiwa Allah biyayya.
Alhasan -Allah yai masa rahama - ya kasance duk lokacin daya karanta ayar yana kance:
"اللهم فأنت ربنا فارزقنا الاستقامة"
Ya kasance daga cikin addu'oin Annabi (S.A.W.) k**ar yadda Imam Attairmithi, da Nasa'i s**a fitar:
"اللهم إني أسألك الثبات في الأمر ، والعزيمة على الرشد"
Dan haka yana daga cikin muhimmin abu maida hankali wajen aikin alkhairi bayan Ramadan, tare da dagewa da roƙon Allah akan ya tabbatar damu akan hakan, k**ar yadda aka samu magabata suna aikatawa.
Zulyadaini Auwal Abdullahi
3/Shawwal/1445H
Zulyadaini Auwal R/lemo
Teacher, reader, typist, reciter and journalist
Goni Nura Yahya Salihu Director na Al'anwar Babban baƙonmu a Shirinmu na Goron Sallah.
Lokaci: 4:00 na yamma
98.9 B.U.K. FM
Ramadaniyyat shi ne shiri na farko gobe from 98.9 B.U.K.
FM. Zamu kasance da Prof. Ahmad Murtala da kuma Dr. Umar Ibrahim Indabawa
By 7:00am-8:00am
Munyi magana wasu suna ganin abun k**ar wasa, wallahi duk mutumin da yake barin matarsa tana yawon zuwa kasuwa musamman a lokutan da ake cin kasuwar sallah To "Dayyusi" ne, anan fa za kaga suna bawa yaro Mama, suci abinci a shagon da aka sakar musu fuska a gaban mutane da azumi. (Aikin banza aikin wofi)
Ɗazu na je shagon wani mai gida ɗakko wasu kaya, kawai wata mata ta kira mai pure water ta fasa ta shanye, bance komai ba, kawai ta tuɓe Hijab, nace Hajiya wai yaya dai?! Ta ce: Wallahi ta gaji banga ma ta karya azuminta ba yanzu!. A raina nace wannan babbar kai ce, ta fi ƙarfi na. ( Na ɗau kayana na wuce).
Ƴan mata kuwa, ba a maganar rashin kunya da fitsari. Rannan wani ya mari wata a shagonsa, da aka bi ba'asi, ashe wai idan zata tambaye shi farashi sai ta taɓa masa kafaɗa. Dan Allah ya ya sunan wannan-?
Akwai Hajiyoyi da ƴan mata da ba sai Sallah suke zuwa kasuwa ba, irin waɗannan sun san me suke matuƙa, kuma suna kare mutuncin kansu. Bayansu kuma akwai matan aure da ƴan mata da suke zuwa cikin mutunci su tafi cikin mutunci abunsu, ba kasafai zaka ga suna dogon tayi ba.
Bana mantawa, wajen Shekara uku kenan yanzu, akwai wata mata data taɓa zuwa kasuwa ta siyi takalmanta dana yaranta, da taga yadda ake ballagazanci a kasuwa, har yau bata ƙara zuwa ba, sai dai tayi magana a tura mata samples ta zaɓa, sai a tura mai delivery ya kai mata. (Kai Ni har mun saba, ni nake kai mata da kaina).
Idan ka saki matarka ta tafi kasuwa, to kasan inda ka tura ta, Sai ka shirya amsoshin tambayoyin da Allah zai yi maka. Akwai wanda shi a ransa ya san matarsa bata can-canci taje kasuwa ba, saboda kullum idan ya dawo sai yayi karo da ita tane leƙe, which means, neman hanyar yaro take.
Allah ya kyauta!
Mata masu zuwa kasuwa gaskiya kuna cin amanar Allah da mazajenku, harma da ƴaƴanku. Kuma wallahi sai Allah ya tambaye ku akan irin abubuwan da kuke yi😭😭😭
Ba wuya abun, har mun iso👇
قال الملأ الذين استكبروا من قومه (الأعراف: 88)
Allah ka bamu sa a🤲
La ilāha illalAllah! Da naga reminder ɗin iftar ɗin da aminina kuma mai gidana a Jami'a Mal. Ibn-katheer Al'arabee suke haɗa mana duk shekara a unguwa uku, sai kawai sai na tuna da abokina Umar Sadi Umar, wanda duk shekara tare muke dawowa dashi, amma ba tare muke tafiya, saboda ni daga kasuwar Sabon Gari nake wucewa, shi kuma daga kasuwa ƴan katako R/lemo. wannan shekarar labari ya canza, saboda yana Uganda yana karatun degree na biyu. -Allah ya bada sa'a. Nesa da mutumin kirki akwai ɗaci, indai zamu haɗu to zai kirani koni na kirasa akan na tawo masa da littafin da zai karanta ko shi ya tawo mun dashi.
Hakazalika, nayi missing ɗin Aliyu Bello (Aba gimba), shima kusan tunda na shiga Jami'a na maƙale masa, ba yadda za a yi ace bamu haɗu a sati sau Huɗu ba. Aliyu bashi da shiga cikin mutane kuma bashi da damuwa da cuɗanya da al'ummah, amma saboda ina ƙaunarsa agefe na har gurin aiki na na jashi saboda ina son ganinsa a tare dani. Shima idan aka ce yau Lahadi ko Talata da Laraba nakanji wani iri idan na tuna baza mu haɗu ba saboda shima ya tafi neman degree ɗinsa na biyu (Amma waya a Whatsapp bata yanke mana).
Allah ya baku abinda kuka tafi nema, ya kuma sa al'ummar Musulmi suci gaba da amfana daku idan kun dawo.
Asha ruwa lafiya!
Idan ka samu iyaye na gari, Masu gida na gari, mata ta gari, ka more.
Allah ka bamu ka kawo lamba ukun da alkahairi 🤲
Kada ka ɓata kanka da son abun hannun mutane, kwadayi, Sa rai, Jira a baka, dss. Ka nema a gurin Allah, ka dogara daShi kana mai yaƙini zai baka.
Ramadaniyyat 4rm B.U.K. FM 98.9
Baƙon yau shi ne Prof. Taufiq Abubakar .
6:00 na yamma dai-dai.
Rayuwar Jami'a:
الحياة الجامعية: آلام وآمال.
Rubuta ne zanyi shi episode 5 dogaye, na Hausansa zaizo a wannan sahar. Na Larabcin kuma zan wallafasa, tare da neman ɗaya daga cikin abokaina especially marubucin jaridar nan Aliyu Idrees Ali domin ya fassara sa zuwa harshen Turanci.
Zanyi shi ne, saboda dalilai guda Biyu:
(1) Tunasar da kaina game da irin rayuwar da muka yi a Jami'a tsawon shekaru 6.
(2) Nusantar da ƴan uwa na masu shirin fara karatun Boko abubuwan da suke ciki; domin su k**a da kyau.
Rubutun zai taɓa Kowanne ɓangare in Sha Allah.
BarakAllahu Feekum.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Rijiyar Lemo, Sabon Titin Ɗan Rimi, Kano-Nigeria
Kano