28/07/2024
Ƙanwata! NI MA NAMIJI in gaya miki babu addu'ar da na fi yi a kwanakin nan irin Allah ya azurta ni da mace tagari, wacce za ta zame min sanyin idaniya (ni ma namiji kenan). Ina ga ke?
Ƙanwata! Kada ki yi wasa da addu'a Allah ya ba ki miji magari. Ki yi da gaske! Ki rabu da masu cewa kina zuwa sallar 'tarawih' da 'tahajjud' don neman miji, eh! Ai a wajen Allah k**e nema, ba a wajen kowa ba.
Ƙanwata! Akwai wata nasiha da mahaifiyyata ta taɓa yi min kan neman matar aure, ta ce, "ka ƙaddara Allah ya yi za ka shekara 70 a duniya, idan ka yi aure kana da shekara 30, zaɓar macen da za ku rayuwa tamkar zaɓar yadda za ka ƙare shekarunka 40 ne a duniya. Idan ka auri 'yar bala'i ka shiga bala'i, ka haɗu da hawan jini da 'depression'. Idan ka samu salaha asirinka ya rufu". To! Ina ga ke mace za ki dogara ki zauna a ƙarƙashin wani?
Ƙanwata! Idan ma kina da wani buri a 'future' bai wuce aure ba. Burin karatu ko aiki a wajenki ke mace duk suna bayan aure. To laifi ne don kin roƙi Allah 'future'rki', Allah ya baki miji nagari?
Ƙanwata! Muma maza muna roƙon 'future', mu roƙi nasibi, aiki mai kyau, rufin asiri, ke kuma mece ce taki 'future'? Ki roƙi tsarin Allah daga namijin da zai sa kina 'HIDE MY ID'.
Ƙanwata! Duk lokacin da za ki yi addu'a, ki roƙi Allah ya ba ki miji nagari, aure shi ne burin 'ya mace. A gidan aure za ki huta ko ki shiga bala'i, ki roƙi alheri.
28/07/2024
Duk lokacin da ka kalli "Tsoffi", za ka ga iya maƙurar komai game da mutane. Za ka ga kwaɗayinka. Za ka ga sha'awarka. Za ka ga ƙarfinka. Za ka ga ƙarfin jin daɗin rayuwa. Za ka gansu, duk sun gushe.
A gabanka, zaka ga yanda komai suke tsayawa, su zama ba komai ba. Duk yanda aka so a rayu, an yi rayuwar, amma gashi anzo wata gaɓa wacce babu wani abu mai nuna cewa an yi wata rayuwa. Komai yayi rauni, wasu abubuwan jikin ma sun bar aiki. Morewar gangan jiki ta rasa ma'anarta.
Tsoffi ayoyi ne a garemu akan rayuwa; na mu rage ɗaukar al'amura da tsanani da makanta, k**ar ba za'a zo wata gaɓa da duk waɗannan abubuwa ba zasu zama basuda wata ma'ana ba. Waɗannan tsoffi sune dai masu ƙarfin nan a baya. Wannan tsohon shine mai kuɗi, mai mataye, mai morewa. Wannan tsohuwa ita ce yarinya mai kyau, wacce take ji da kanta, wacce maza suke tururuwa akanta.
Babban abinda zai kashe maka jiki shine: Zaka ga yanda muke wuce irin waɗannan tsoffi k**ar ba su cikin rayayyu. A gefen hanya, suna zaune, sun gaji. A cikin unguwanni, suna zaune a kofofin gidaje. Mutane suna wucesu, ko kallonsu ba a yi. A cikin Masallatai, suna zaune cikin gajiya da nutsuwa. Ga su nan, sun rayu, amma yau sun koma yan kallon rayuwa. Tafiya a hankali. Tashi a hankali. Motsi a hankali cikin gajiyawa.
Haka nan, idan ka sauraremu muna hira, zaka ji yanda muke magana dangane tsoffi k**ar basu da rai. Babu su a gabanmu, muna ji k**ar basu da komai yanzu da zasu iya yi mana. Amma mutane ne suma k**armu a wasu lokuta a baya, amma a yau sun zama k**ar basu rayu k**ar yanda muke ba a yau. Hasalima, su a karan kansu suna jin sun tashi a aiki, rayuwarsu ta zama abar lallaɓawa, komai suna binsa a hankali. Dolensu! Domin ko sun so su bi abubuwa da tsanani ko da gudu, ba zasu iya ba.
A cikin rayuwar tsoffi, akwai darussa a garemu. Kuma, matukar da rai da rayuwa, mu ma zamu tsufa. Watarana, mu ma zamu zama darussa ga wasu a bayanmu.
Allah SWT ya bamu rayuwa mai kyau.
18/07/2022
Haɗuwata da Umar Ibn Kattab.
Na tambayi Umar shin ko akwai wani misalin da zaka ƙara min na baiwar 'Firasar' da Allah ya baka?
Tabbas akwai:
Wata rana anzo da wani mutum waje na da tuhumar laifin sata, sai nace da shi hukuncinka shi ne za'a yanke maka hannu, ba makawa kuma sai an zartar don shi haddi ana kawar da shi ne da SHUBUHA kawai kai kuma ga shi baka da wata hujja da zata hana a yanke hannunka!
Sai mutumin ya ce da Ni: ina haɗaka da Allah ya Sarkin muminai ka yi min afuwa wannan ne karon farko da na taɓa yin sata.
Umar: sam ƙarya kake ba wannan ne karon farko ba!
Shi: shin ka san gaibu ne ya Umar?
Umar: ba san gaibu ba amma nasan Allah ba ya taɓa tona asirin bawansa da zunubinsa a karon farko.
Ni: To ya kayi da mutumin?
Umar: Umarni na bayar aka yanke hannunsa.
Lokacin Aliyu Ibn abi ɗalib(RA) yana wajan, da ganin haka sai ya bi bayan wannan mutumin ya tambaye shi, ina haɗaka da Allah ka faɗa min gaskiya shin da gaske wannan ce satarka ta farko ba k**ar yadda Umar ya zata ba?
Shi: Wannan ne karo na 21 ana biyun aka k**a ni.
Sai Aliyu(RA) ya ce: Umar ya yi gaskiya da yace "Ni ba mayaudari ba ne, haka mayaudari ba zai taɓa yaudara ta ba"
"لست بالخب ولا الخب يخدعني"
عندما التقيتُ عمر بن الخطاب📚 أدهم شرقاوي.
17/07/2022
https://www.farinsako.com.ng/2022/07/yadda-zaku-toshe-kafofin-batsa-daga.html
Yadda zaku toshe kafofin batsa daga wayoyinku dana yaranku
Yadda zaku toshe kafofin batsa daga wayoyinku dana yaranku. Kamar yadda kafar sadarwar zamani(internet) take da abubuwan amfani masu yawa...
07/07/2022
“Mafi falalar azumi bayan na Ramadan shi ne azumin ranar arafa, Allah yana yafe zunuban shekara biyu ga wanda ya azumce shi,mafi falalar ayyuka a ranar arafa sune azumi kabarbari(ambaton Allah) da addu'a tare da yawaita istigfari”
Allah ya karɓi ibadunmu, ya amshi addu'oinmu.
06/07/2022
ALIYU BIN ABI TALIF OLD STUDENTS ASSOCIATION.🎓🎓🎓🎓🎓
TARO ! TARO !! TARO !!!
Amadadin Committee Gudanar Da Taron Sallah Na Duk Shekara Na Wannan Makaranta Mai Albarka, Committee Yana Sanar Da Duk Wani Dalibi Namiji Dayayi Wannan Makaranta Gagarumin Taron Sallah Na Bana Wanda Za'ai Kamar Haka:
Ranar : Litinin 11-07-2022.
Lokachi : 04:00pm Na Yamma.
Wurin Taro : Madarasatul Aliyu Bin Abi talif Dake Rijiyar lemo Kusa da Masallachin Gawo .
Allah Ya Bada Ikon Halartar Allah Yasa Muyi taro Lafiya Mugama Lafiya.
30/06/2022
1 Zulhijja.
Yazo a Hadisin da Imamul Bukhari ya fitar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa “Babu wasu kwanaki da ayyukan Alkhairi s**a fi soyiwa a wajan Allah sama da waɗannan kwanaki goma na watan Zulhijja Sahabbai s**a ce ko da Jihadi ya Rasulullah? Annabi s.a.w yace ko da Jihadi sai Mutumin da ya fita yaƙi da ransa da dukiyarsa bai dawo da ɗaya daga cikinsu ba.
Lallai ne mu yawaita ambaton Ubangiji a cikin waɗannan kwanaki tare da gode masa bisa ni'imar rayuwa da ganin waɗannan kwanaki masu albarka, wasu sun ga na bara amma ba da su za'ayi wannan ba wasu kuma sun riski wannan ɗin ba lallai su riski na gaba ba, lallai mu amfani lokacinmu muyi sadaka mu yi azumi muyi karatun Alkur'ani mu kyautatawa iyaye mu yi addu'ar zaman lafiya da yalwar arziki ga ƙasashanmu da sauran ƙasashen musulmi, mu yi addu'ar samun shuwagabanni na gari masu tausayinmu masu amana, mu guji saɓo domin suna hana gafarar Ubangiji a irin waɗannan lokuta.
17/06/2022
Jun 17
A mak**anciyar wannan ranar a shekara ta 714 aka Haifi
«أبو جعفر المنصور»
Khalifa na biyu a daular Abbasiyya, masana tarihi suna ganin shi ne wanda ya gina daular Abbasiyya ta tsaya a kan ƙafafunta.
Abu Ja'afar al-mansur mutam ne mai tsanani kwarai da gaske ya yadda da maganar Alexander da yake cewa " k**ar yadda ba zai yiwu a samu rana guda biyu a sama ba haka bai k**ata a samu shugaba biyu ga daula ɗaya ba" shi yasa al-mansur ya dinga kauda duk mutanan da yayi zaton zasu kawo masa tsauko ga mulkinsa daga cikin su akwai abu musulim Alkurasani wanda shi ne mutumin da ya dinga bi lungu da saƙo yana naimawa al-mansur mubaya'a, amma da al-mansur ya fahimci k**ar abu musulim yana yi masa katse landan a mulkinsa sai ya kawar da shi.
In muka bar batun mulki abu Ja'afar al-mansur mutum ne mai saukin hali bashi da almubazzaranci, tsananinsa bai hana shi tsaida adalci ba.
Wata rana ɗaya daga cikin gwamnoninsa ya kwacewa wani mutum gonarsa, sai mutumin ya kawo ƙara wajan al-mansur yace da shi ya amiral mu'uminin in faɗa maka matsalar da ta kawo Ni ko in ɗan baka wani misali?
Sai al-mansur yace: a'a kayi min misali.
Sai Mutumin nan yace:
A duk lokacin da wani abun cutarwa ya tunkari ƙaramin yaro gudu yake yaje wajan mahaifiyarsa,saboda a tuaninsa babu wanda zai taimake shi sai ita, idan ya ƙara girma sai ya dinga zuwa gurin mahaifinsa idan ya ƙara girma sai ya dinga kai ƙara wajan hakimi idan ya ƙara fahimtar rayuwa sai ya dinga kai ƙara wajan Khalifa idan Khalifa bai yi masa adalci ba sai ya kai kukansa wajan Ubangiji.
To yau nima wata matsala ta same ni bani da wanda zai iya kwatar min haƙƙina sai kai sai Allah, idan kayi min adalci shikenan in baka yi min ba sai in Kai ƙara na zuwa ga Allah in dangana!
Da al-mansur yaji haka sai yace a'a zamu yi maka adalci dai sai ya rubuta takadda guda biyu ɗaya aka rubuta an mayarwa da wannan mutumin gonarsa a ɗayar takaddar kuma aka rubuta cewa an tsige wannan gwamna.
وتلك الأيام
أدهم شرقاوي
16/06/2022
JUN 16
A mak**anciyar wannan ranar a shekara ta 778 miladiyya sahabin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama
«سعيد بن العاص رضي الله عنه»
Ya yi wafati, Sa'id yana cikin Sahabbai masu ƙananun shekaru Annabi s.a.w yayi wafati yana ɗan shekara 9 ya rawaici Hadith daga Nana A'isha Da Sayyiduna Umar.
Yana cikin Sahabbai attajirai mutum ne mai kyauta da karamci ga kyakkyawan mu'amala.
Wani mutum da ake kira أبو الجهم العدوي makwabcib Sa'id ne wata rana ya siyar da gidansa, darhami dubu ɗari bayan mai siyan ya biya shi kuɗin gidan sai kuma yace masa sauran kuɗin makwabci na da zan bar maka.
Sai mai siya yace wane kudin makwabci kuma dama an taɓa siyan makwaftaka?
Sai mai gidan yace makwabci na shi ne sa'id Ibn A's don haka ka siya makwabtakarsa in ba haka ba na fasa siyar maka.
Don ba zan bar maka makwabtakarsa a banza ba, don mutum ne da idan yaga baya ganina yake tambayar ina na shiga, idan ya ganni yayi maraba da gani na cikin kyautatawa in bana nan sam baya cin amana ta in na tambaye shi wata buqata yawa sauri yake ya biya min, kai ko ban tambaya ba yi min yake!
Da labari Ya jewa Sa'id sai ya turawa makwabcin nan nasa da Dirhami dubu goma yace ya bar gidansa ba sai ya siyar ba.
In akwai wani darasi da zamu koya a wannan kissar shi ne, makwabtanmu da waɗanda muke tare da su su s**a fi cancantar su fadi halinmu.
Makwabcinka shi zai faɗi wane irin makwabci ne kai.
Iyayanka su zasu faɗi wane irin ɗa kake a wajansu.
Matarka ita ce zata faɗi wane irin miji ka kasance a wajanta.
"Yayanka sune zasu faɗi wane irin Uba ka kasance a wajansu.
وتلك الأيام.
15/06/2022
Jun 15
A mak**anciyar wannan ranar a shekara ta 674 miladiyya sahabin Annabi s.a.w
«سعد ابن أبي وقاص»
Ya yi wafati, yana cikin mutane na farko-farko da s**a shiga addinin Musulunci. Shi ne Musulmi na farko da ya fara harba Mashi saboda ɗaukaka addinin Musulunci ranar yaƙin Badar.
Shi ne mutumin da Annabi s.a.w yace da shi “ Harba mashinka ya sa'ad Iyaye na fansa gare ka"
Ya jagoranci Yaƙoƙi masu yawa a musulunci shi ne wanda ya jagoranci buɗe ƙadisiyya a zamanin Umar Ibn Kattab.
وتلك الأيام.