13/08/2026
Wani tsohon wakilin Najeriya a Musabaqar Malik Abdulaziz ta Duniya, Dr. Gwani Ibrahim Siraj, ya bayyana yadda aka samu manyan sauye-sauye a Musabaqar Qur’ani ta Saudiyya tun lokacin da ya wakilci Najeriya a shekarar 2002 zuwa yanzu.
A cewarsa, a shekarar 2002 ana gudanar da gasar ne a Intercontinental Hotel da ke Makkah, yayin da a yanzu ake gudanar da ita a faɗaɗin Masallacin Harami na Makkah.
Ya bayyana cewa a wancan lokaci ’yan takara ba su da yawa, kuma babu matakin tantancewa na farko, abin da ke bai wa alƙalai damar kammala zaman karatu cikin gajeren lokaci. Yanzu kuwa yawan ’yan takara ya ƙaru, tare da wasu sababbin matakai da s**a sa gasar ta fi tsauri.
Dr. Ibrahim ya kuma bayyana cewa a baya Najeriya na iya zuwa da ’yan takara da yawa, amma daga baya aka rage adadin zuwa mutum biyu. Sai dai a shekarar 2026 adadin ya ƙaru zuwa maza biyu da mata biyu, sakamakon fara shiga mata a gasar.
Ya ce fara Musabaqar Mata na daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu, domin hakan zai ƙara ƙarfafa mata wajen haddar Alƙur’ani, karatu da fahimtar ma’anoninsa.
Haka kuma, ya bayyana cewa kyaututtukan gasar sun ƙaru sosai. Ya ce a lokacin da ya shiga gasar a 2002, wanda ya zo na ɗaya a babban ajin Tafsiri yana samun kusan Riyal 75,000, yayin da a yanzu kyautar babban matsayi a wasu rukunan gasar ta kai daruruwan dubban Riyal.
Dr. Ibrahim ya ƙara da cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin karatun Alƙur’ani, inda a yau ake samun ƙwararrun masu karatu daga sassa daban-daban na duniya, ba kamar a baya ba da wasu ƙasashe kaɗan ne s**a fi shahara.
Ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Musabaqar ta duniya ci gaba, tare da bai wa ’yan takarar Najeriya nasara a gasar da ke gudana a Saudiyya.
Allah Ya taimake su, Ya dawo da su gida cikin nasara. 🤲🏽