29/09/2025
Zauran Sheikh Aliyu Rabiu Kurna
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zauran Sheikh Aliyu Rabiu Kurna, Kano.
29/09/2025
WAKA:
BIN TAFARKIN MANZON ALLAH
SHI KADAI NE DACEWA
14/07/2023
HUKUNCIN ASKE WANI SASHEN SUMA DA BARIN WANI SASHEN
Kamar yadda wasu ƙabilu cikin Fulani ke da al'adar barin toliya ko gegire ko faskara a kansu, haka Larabawa s**a kasance suna yi kafin zuwan Musulunci da kuma farkonsa.
A Musulunci an sami nassoshin da s**a yi tankiya game da wannan al'adar, saboda haka Musulmin farko s**a daina yin ta.
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga sahabi Abdullahi Ɗan Umar (Allah ya ƙara musu yarda) cewa: "Manzon Allah (SAW) ya hana 'qaza'u'. Sai aka tambayi Nafiu cewa mene ne 'qaza'u' sai ya ce shine a aske wani ɓangare na gashin kai jariri a bar wani ɓangaren.
A wata riwaya ta Al-Imam Ahmad da Abu Dawud kuwa cewa aka yi: "Manzon Allah (SAW) ya ga wani yaro ne an aske wani ɓangare na sumar dake kansa an bar sauran. San Manzon Allah (SAW) ya ce: ku daina haka. Ku aske sumar duka, ko ku bar ta duka".
A cikin littafin 'Majmu'u' na Al-Imam Nawawiy yana cewa: "Aske wani ɓangare na suma a bar wani ɓangare abin ƙyama ne".
A wannan zamanin kuwa abu ne a fili cewa wannan al'adar ta sake dawowa, sai dai wannan karon ba ƙananan yara ake yi wa ba. Galibi matasa ne suke yi, musamman ƴan gayu da masu yin sana'o'in da s**a jiɓinci wasannin motsa jiki ko nishaɗantarwa ko makamantansu. Galibin masu yi suna koyi ne da wasu fitattun mawaƙa na gida ko na waje ko sharararrun ƴan wasan ƙwallon kafa ko jaruman fina-finai ko ƴan dambe ko ire-irensu.
To daga nan ne Uthaymeen a cikin 'as-Sharhul Mumti'i' yake cewa aske wani sashen suma da barin sauran da nufin kwaikwayon ka*firai to haramun ne saboda nassoshin da s**a zo masu yawa bisa hani game da koyi da al'adun waɗanda ba musulmi ba.
Allah shine mafi sani.
Assalamualaikum yan uwa musulmai tare da fatan alheri Allah ya bamu sa'a da nasara a rayuwar mu.
Click here to claim your Sponsored Listing.