04/07/2024
SHIEKH IBRAHIM INYASS (RA) MATSAYINSA A DUNIYAR MUSULMI
An san Shaihu Ibrahim (RA) a matsayin mutum mai ilimin a duk fadin duniyar musulmi. Ya samu karramawa da girmamawa a dukkanin kasashen musulmi, kuma ya ziyarci kusan dukkaninsu, da kuma ziyarar al'ummar musulmi a wasu kasashen. Ya gana da malaman musulmi na zamaninsa, kuma ya yi alaka mai amfani da juna da su.
Daya daga cikin kasashen da ya fi ziyarta ita ce kasar Saudiyya, inda ya yi aikin hajjin dakin Allah mai alfarma sau da dama. Ya kuma ziyarci Alkahira sau goma. Yana da alaka mai karfi da shuwagabannin jami'ar Al-Azhar, irinsu Shaykh Mahmoud Shaltut da Shaykh Dr. Abd al-Halim Mahmud, dukkansu tsoffin shugabannin jami'ar Al-Azhar ne. Malaman Azhar sun karrama shi ta hanyar ba shi lakabin "Shaikhul Islam". An ce Shaikh Shaltut ne ya ba shi wannan mukami.
Kuma sun karrama shi a wani lokaci ta hanyar bukatarsa da ya jagoranci sallar Juma’a a cikin watan Safar, shekara ta 1381 bayan hijira (21 ga Yuli, 1961), kuma shi ne bakar fata na farko da ya samu wannan daraja. Bayan kammala sallar, Shaikh Muhammad al-Ghazali ya yi tsokaci a kan khudubar Shaihu Ibrahim da cewa: “Muna da tabbacin makomar al’ummar Musulmi a duniya matukar dai akwai irinsu fitaccen bakonmu Shaikhul Islam Shaihu Ibrahim a cikin Musulmi.