Muryar Tsangayun Kano State

Muryar Tsangayun Kano State

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muryar Tsangayun Kano State, Educational Research Center, Kano.

27/02/2026

Madina tayi kira

Shatiman Mahaddata Alqur'ani na Nigeria
Goni misbahu Aliyu baba Gwani Allah yasaukeku lafiya ayimana ziyara

03/02/2026

Gayyata ta musamman

31/01/2026

Alhamdu lillahi Yau Asabar 31/1/2026/

Majalisar qoli ta Mahaddata Alqur'ani ta Nigeria
Ta tabbatar da nadin Gwani Abdurrahman Dan Alaramma A matsayin Turakin Mahaddata Alqur'ani na Abuja Domin qoqarinsa da jajircewa Dakuma qara zaburar da Matasa kan Alqur'ani Kuma Allah yatashi riqo.

Sidil Furuk Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na Kano

DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA

07/01/2026

Tunda ake S A Tsangaya a jihar Kano ba a taba S A Tsangaya me kishin Tsangaya da yan Tsangaya irin wannan bawan Allahn Gwani Musa Falaki ba, wasu Gwamnatocin ma ba a san sunan waye ya rike irin wannan muƙamin ba, bare an san aikin da su ka yi, bare kuma korafi a kan sun yi kaza ba su yi kaza ba.

Idan aka buɗe zuciya za a gane shi aikin sa bayar da shawara ne ba zartarwa ba, kuma ba Hukuma ce da shi da ake ware mata wani kaso domin yin wani aiki ba, aikin bayar da shawara, idan ya bayar an dauka Shikenan idan ba a ɗauka ba, shi dai ya yi nashi aikin.

Wannan bawan Allah ta karkashin ofishin sa ya saka wasu daga cikin yan'uwa ƴan Tsangaya cikin farin sau babu adadi. Ba za iya yi wa kowa komai ba, k**ar inda ko Gwamnatin tarayya bata isa ta yi wa kowa komai ba, duk abin da za a yi a gwamnati ko ta jaha ko ta Tarayya ko ta Local Government sai kana da rabo za ka samu.

Jahilci da hassda da son zuciya da rashin sanin ya tsarin gwamnati yake, shi ne zai sa idan ba a yi tsari da kai ba ka ce ba a yi, ko ka ce ba a yi daidai ba, idan kuma an yi da kai ka ce an yi daidai, wannan ya zama banbaɗanci na siyasa, idan kuwa haka ne k**ata ya yi mutum ya fito fili ya k**a siyasa haikan domin cimma burin sa.

Idan mutum yana son gaskiya kuma yana son kawo ci gaba a wani tsari, to Gwamnati ake ƙalu balan ta ba wai wani wanda yake da wani muƙami ba, domin wanda ya bayar da wannan muƙamin ya fika sanin wa ya bawa mukami, ya fika sanin iya hurumin aikin sa, idan wanda ya bawa aiki baya yin abin da Yak**ata to ya fika sani, tunda shi ya bashi aikin.

Wannan bawan Allah Ya yi Abubuwan alkhaiiri da yawa a Tsangaya wanda tun zamanin Malam Ibrahim Shekarau ba a yi su ba.

Muna yi masa fatan alkhaiiri da fatan samun nasara a wannan aiki da aka bashi da fatan samun kujerar zartarwa da tafi ta bayar da shawara domin kawo ci gaba ga Alarammomi.

Allah ya shiga Lamarin sa Amin

Yasir Gwani Badamasi

06/01/2026

Yanzu Mun Ransar Da Gidan Gwamnatin Kano
Saura Villa In Sha Allah

Mai Bawa Gwamna Shawara Wato S.A Tsangaya GWANI MUSA FALAKI. yayi abun ayaba Dama yasaba Da qoqari Akan Yan Tsangaya Allah yayi Masa Jagora Allah yakareshi Daga Sharin Maqiya

03/12/2025

ALHAMDU LILLAH
GA GWAMNAN MAHADDATA ALQUR'ANI YOBE STATE
WANNAN TAFIYACE TA HADINKAN MATASAN
DA QARA ZABURARWA AKAN ALQUR'ANI.
DAYA BAYAN DAYAN ZASU BIYO IN SHA ALLAH.

DAGA DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA
3/12/2025

27/11/2025

TA'AZIYYA GA IYALAN SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI
A madadin Dukkan Mahaddatan Alƙur'ani na Kano da Kewaye

A madadin dukkan Mahadda Alƙur'ani na Jihar Kano da kewaye, Gwani Sidil Faruk, Gwamnan Mahadda na Kano State (Da Kuri Da Maimai), yana mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan marigayi Sheikh Dr. Dahiru Usman Bauchi (Rahimahullah), musamman ɗansa *Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi (Khadimul Faidha)*, da kuma ɗalibansa da mabiya a ko’ina.

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga al’umma gaba ɗaya, musamman bangaren ilimi, tasawwuf, da tarbiyyar al'umma bisa tsantsar koyarwar Qur’ani da Sunnah. Rayuwarsa ta kasance abar koyi wajen shimfiɗa zaman lafiya, karfafa ɗa’a da gina al’umma masu tsoron Allah da biyayya ga Annabi Muhammadu (SAW).

Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya ɗaukaka darajarsa a Aljannah, Ya sa Alƙur’anin da ya koyar da shi da miliyoyin mutane s**a haddace ya zama hujja a kansa. Allah Ya ba iyalansa, dalibansa da mabiya, musamman Sheikh Khadimul Faidha haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Allah Ya jikan Sheikh Dahiru Usman Bauchi da rahma ya b iyalansa da mabiya haƙuri

26/10/2025

Gayyata ta musamman
Daga Gwarzon Shekara na Tsangaya na 2025
Gwani Saminu Barden Tilawa Vice president na Matasa na QASA

sanarwa Daga Gwani Sidil Furuk Alhamzawy
Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na kano da kewaye (DAKURI DA MAIMAI)

DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA

19/10/2025

Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na kano da kewaye Gwani Sidil Furuk Alhamzawy
(DAKURI Damaimai)

13/06/2025

قل اللهم ملک الملک توت الملک من تشاء

In Sha Allahu zamucigaba yin nadanade A arewacin Nigeria Domin qarfafawa Matasan Mahaddata quwiwa Akan sha'anin Alqur'ani Dakuma tajdidi Ga Wanda suke da Muqami Domin qarin hadinkai.
واعتصموابحبل الله جمیعا ولا تفرقوا

Ba qungiyaba. Qarqashin group namu na Matasan DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA

Muna Taya Dan uwa Murna Gwani Aminu Garkuwa Matasan Alarammomin zazzau Kaduna State
Allah yariqamasa.

Sidil Faruk Alhamzawy
Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na jahar Kano

13/6/2025
Da'irar Musaffa TV

12/06/2025

قل اللهم ملک الملک توت الملک من تشاء

In Sha Allahu zamucigaba yin nadanade A arewacin Nigeria Domin qarfafawa Matasan Mahaddata quwiwa Akan sha'anin Alqur'ani

Ba qungiyaba. Qarqashin group namu na Matasan DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA

Muna Taya Dan uwa Gwani sh*tu Dan mama murna Allah yariqamasa.

Sidil Faruk Alhamzawy
Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na jahar Kano

Da'irar Musaffa TV

21/03/2025

Saqon Matasan Mahaddata Alqur'ani na jahar Kano
Suna Addu'a Allah yasa dalilin wannan nadin da akayiwa Mai girma Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf. Allah yasa yazama yafi kowane Gwamna a Arewacin Nigeria Gina Tsangayu da Yan Tsangaya albarkacin Alqur'ani
Domin bai taba fadar mummunar magana akan almajirai ba sedai tallafamusu da yakeyi da abinci tuqatuqa kayan karatu da shauransu.

sabanin Gwamnatin Baya da tadinga k**asu cikin Azumi a cikin tsangayunsu tana kullewa abayan gari sabod zalunci ta tarwatsa Tsangayu. Wannan zancene na gaskiya ba na siyasaba.

Kuma muna qara Jinjina ga S.A Tsangaya Gwani musa Falaki Allah yaqara jagora qudirin da yake shigarwa Allah yasa azartar dasu Amin.

Muryar Tsangayun Kano state

21/3/2025

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Kano