Yawan lazumtar abu alama ce ta ƙaunarsa da ba shi muhimmanci da fifita shi a kan waninsa.
Abin da ka fi lazumta da kasancewa tare da shi ko da yaushe ba tare da ka ƙosa da shi ba shine abin da ka fi so a rayuwarka ko shakka babu.
Sai ka auna ka gani 👇
- Tsakanin neman duniya da neman lahira wanne ka fi lazumta ba tare da gajiya ba?
- Tsakanin karatun Alkur'ani da litattafan addini da kuma yawo cikin shafukan sada zumunta a wayarka wanne ka fi lazumta ba tare da ƙosawa ba?
- Tsakanin zama cikin iyalinka da da ba su tarbiyya da kuma zaman majalisar hirar Ball ko Siyasa wanne ka fi lazumta ba tare da sarewa ba?
- Tsakanin sauraron karatuttukan malaman addini da sauraron waƙoƙin soyayya da siyasa wanne ka fi jin daɗi ba tare da ya gimshe ka ba?
- Tsakanin kallon tashoshin addini irin su Wisal Hausa TV / SUNNA TV / AFRIKA TV3 / MANARA TV / ALBANY TV ... da sauransu, da kuma kallon tashoshin shiriritar wasanni da finafinan Hausa ko ma har na larabcin wanne ka fi kulawa ba tare da gajiyawa ba?
Tsakanin da tsakanin....
Tsakanin da tsakanin....
Yi wa kanka hisabi kafin mai ƙididdigar ƙwaƙwaf ya yi maka hisabi.
✍️ AllemawyMuhammad Auwal Nuhu Allemawy
itz_muhammad_mahabub
اللهم صلى على. محمد وعلى آل محمد كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم إنك حميد مجيد ا
01/11/2022
Mtswwww😒😒😒
Alhamdulillah ❤️💯
Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Kano