17/12/2025
LABARAI CIKIN HOTUNA
MARYAM MUHAMMAD TA KAMMALA KARATUN AL-QUR’ANI CIKIN NASARA A MANBA’UL FAWA’ID ISLAMIC ACADEMY – KANO!
Cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, Manba’ul Fawa’id Islamic Academy, Kano, ta gudanar da Bikin Saukar Karatun Al-Qur’ani na ɗaya daga cikin ɗalibanta, MARYAM MUHAMMAD (FARSHA), a ranar Litinin 24 ga Jumadal Ākhirah, 1447 AH, wanda ya yi daidai da15 ga Disamba, 2025.
Taron ya gudana cikin tsari, annashuwa da cike da falala, inda aka shaida kammala karatun Al-Qur’ani da ɗalibar ta yi bayan jajircewa da tsayin daka a tafarkin neman ilimi. Taron ya samu halartar malamai, iyaye da al’umma, lamarin da ya ƙara wa bikin armashi da muhimmanci.
Masu jawabi a wajen taron sun jaddada muhimmancin koyar da Al-Qur’ani tun daga ƙuruciya tare da tarbiyyar yara bisa koyarwar addinin Musulunci, tare da yin addu’ar Allah Ya sanya Al-Qur’ani ya zamo haske da jagora ga rayuwar ɗalibar.
A ƙarshe, makarantar ta nuna godiyarta ga Allah Maɗaukakin Sarki, sannan ta yaba da gudummawar malamai, iyaye da dukkan masu fatan alheri da s**a bayar da tasu gudummawa wajen ganin wannan rana ta kasance abin tarihi da tunawa.
Allah Ya karɓa, Ya sanya Al-Qur’ani ya zama hujja a gare mu, ba hujja a kanmu ba. Āmīn.
Manba’ul Fawa’id Islamic Academy, Kano
Center for Moral and Academic Excellence