18/07/2026
RATAYA AYA KO SURAR ALQUR'ANI A BANGO BID'AH NE
(Fatwar Sheikh Ibnu Uthaymeen – Allah Ya yi masa rahama)
-Daure ka karanta maganarsa gaba ɗaya saboda yawan amfanin da take ƙunshe da shi-
Jiya Juma'ah muka ga wani Ɗan Media ya yaɗa hoton Malam Kabiru Gombe da Ɗansa, ajikin hotunan sai aka hango Suratu Yasin an rataye ta a bango, shine muke tura wannan a matsayin nasiha ga kanmu da Malam da kuma duk wanda saƙon yaje masa.
Acikin Fatāwā Nūr 'Alā Ad-Darb Al-Imam Ibnu Al-Uthaimin (Allah ya jikansa) yace:
"Rataya ayoyin Alƙur'ani a bango, ko ƙofofin masallatai, da makamantan wurare, yana daga cikin sabbin abubuwan da aka ƙirƙira a addini (bid'o'i),
Waɗanda ba a san su ba a zamanin magabata na ƙwarai (Salafus Ṣāliḥ), waɗanda su ne mafificin al'ummomi.
Annabi ﷺ ya tabbatar da haka inda ya ce:
"Mafificin mutane su ne mutanen ƙarnina, sannan waɗanda suke bayansu, sannan waɗanda suke bayansu."
Da ace wannan abu yana daga cikin abubuwan da Allah Maɗaukaki yake so, da Allah Ya shar'anta shi ta bakin Manzonsa ﷺ.
Domin duk abin da yake amfanar mutane a cikin addininsu da duniyarsu, to Manzon Allah ﷺ ya bayyana shi ya kuma shar'anta shi.
Da wannan abu alheri ne, da Salafus Ṣāliḥ sun riga mu aikata shi.
Sannan ya ce:
Muna tambayar waɗanda suke rataye waɗannan ayoyi:
Me kuke nufi da wannan ratayawar?
Idan s**a ce: Muna nufin girmama Kalaman Allah.
Sai mu ce: Wallahi! Ba mu fi Sahabban Manzon Allah ﷺ girmama Littafin Allah ba. Duk da haka ba su rataye komai daga cikin ayoyin Allah a bangon gidajensu ko bangon masallatansu ba.
Idan kuma s**a ce: Muna son tunatarwa da wa'azi.
Sai mu ce: Mu dubi abin da yake faruwa a zahiri. Shin mutanen da suke ganin waɗannan ayoyin suna wa'azantuwa da su?
Wataƙila hakan yana faruwa, amma yana da matuƙar wuya.
Mafi yawanci abin da yake jan hankalin mutane shi ne kyawun rubutun ayoyin, ko frame ɗin da aka sa musu, ko adon da aka yi musu, da makamancin haka.
Yana da wuya ƙwarai mutum ya ɗaga kansa ya karanta su domin ya yi wa'azi da abin da suke ƙunshe da shi.
Idan kuma s**a ce: Muna neman albarka da su.
Sai mu ce: Wannan ba ita ce hanyar neman albarka ba.
Alƙur'ani gaba ɗayansa mai albarka ne, amma albarkarsa tana samuwa ne ta hanyar karanta shi, fahimtar ma'anoninsa da aiki da shi; ba ta hanyar rataye shi a bango ya zama kamar kayan tarihi da ake kallo ba.
Idan kuma s**a ce: Mun rataye su ne domin kariya da tsari,
Sai mu ce: Wannan ma ba ita ce hanyar kariya ko tsari ba.
Domin azkar da ayoyin Alƙur'ani suke amfani ne ga wanda ya karanta su.
Kamar yadda Annabi ﷺ ya ce game da wanda ya karanta Āyatul Kursiyyu da dare:
"Za a ci gaba da kasancewa yana da mai tsaro daga Allah, kuma shaiɗan ba zai kusance shi ba har ya waye."
Duk da haka, wasu majalisu – ko ma da yawa daga cikinsu – da ake rataye waɗannan ayoyi, ana samun surutu marar amfani a cikinsu.
Har ma ana iya samun maganganu haram, ko waƙoƙin haram. Wannan kuwa yana ɗauke da wani nau'i na wulaƙanta Alƙur'ani ta fuskar ma'ana, abin da yake a bayyane.
Bayan haka kuma, akwai wulaƙantarwa ta zahiri da mai tambaya ya ambata, wato waɗannan takardun suna iya faɗuwa kasuwanni ko wuraren datti, a taka su da ƙafafu. Wannan ma wani abu ne da ya wajaba a tsarkake Kalaman Allah daga gare shi"
Sannan sai Al-Imam ya kammala da cewa:
"Taƙaitawa: Rataye waɗannan ayoyi ya fi kusantar zama sanadin zunubi fiye da samun lada.
Bin hanyar tsira da kauce wa wannan shi ne mafi dacewa kuma mafi cancanta ga muminai.
Bugu da ƙari, na ga wasu mutane suna rubuta ayoyin Alƙur'ani da haruffa masu matuƙar ado, har na ga wasu suna tsara wasu ayoyi cikin sifar tsuntsu, ko dabba, ko mutum zaune irin zaman tahiyyar sallah, da makamancin haka.
Suna rubuta ayoyin ne ta wata hanya haramtacciya, wato hanyar yin hotuna, alhali Annabi ﷺ ya la'anci masu yin irin waɗannan hotuna".
Yaɗawa:
Markazu Amãnil Jãmiy Nigeria
Kuyi share domin saƙon ya yaɗu, Allah Ta'ala yasa daku acikin ladan,
Wassalamu alaikum.