ATM Islamic Foundation Online Quiz

ATM Islamic Foundation Online Quiz

Share

Wann kafa ce da za ta baka damr gwada Kwazonka ta hanyar amsa tambayoyin musulumci d kyauta ta musamn

Photos from ATM Islamic Foundation Online Quiz's post 19/10/2023

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION
ONLINE QUIZ

MUN DAWO
INSHALLAH ZA MU CIGABA DA GABATAR DA GASAR TAMBAYOYIN MUSULUMCI TARE DA BA DA KYAUTUTTUKA GA WADANDA S**A YI NASARA

09/12/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

TAMBAYOYINMU NA YAU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Q1. KAWO AYOYI BAIYAR WACCE TAKE DA YAR'UWA IRI DAYA SAK A WATA SURAR KO A WANI BANGARE NA AL-QURANI

Q2. KAWO SUNAYEN MAWALLAFAN WADANNAN LITTAFAN MASU ZUWA

Al-Akhdhari
Kitabul Kaba'ira
Bulug Almaram
Risala
Silatul Arham

Q3. AMBACI ABUBUWA BIYAR DA AL-QURANI YA ZO DA SU KUMA BINCIKE NA KIMIYYA YA GANO SU

Q4. Kawo kaba'ira goma a jere k**ar yanda s**a zo a cikin Littafin Kaba'ira.

02/12/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

TAMBAYOYINMU NA YAU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Q1. WACCE SURA CE DUKKAN AYOYINTA S**A KARE DA HARAFIN "Ψ―" ?

Q2. A WACCE SURA NE HADDIN ZINA YA ZO ?

Q3. SAU NAWA NE AKA AMBACI SUNAN ANNABI AYUB (A.S) DA ZAKARIYYA (A.S) A QUR'ANI

Q4. AMBACI QIRA'O'I BAKWAI DA MUKE DA SU

Kyautar yau ita ce k**ar haka:

1st. Data 3Gb

2nd. 2Gb

3rd. 1Gb

02/12/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

Yau ma inshallahu muna nan tafe muku da gasa da muka saba yi ta tambayoyin musulumci a dai-dai lokacin da muka saba 9:00pm

Yau kyautar ita ce k**ar haka:

1st. Data 3.0Gb

2nd. Data 2.0Gb

3rd. Data 1.GB

Fatan Allah ya yi mana jagora mu da ku baki daya.

26/11/2022

Alhamdulillah

Yan'uwa muna godiya kwarai bisa participating da kuke yi a wannan gasar, shigowarku ita ce kwarin gwaiwarmu ta ci gaba da yi, inna fatan za mu ci gaba da amfanar da juna Ilimi

Cikin ikon Allah a wannnan gasar har lokaci ya cika babu amsa cikakkiyar amsawa, sai bayan cikar lokaci danuwa Adamu Muhammad Sani ya sami amsawa dai-dai, a bisa wannan dalilin ya sami shiga cikin kunshin Bonus

Sannann sai yar'uwa wadda ita ce ta fara amsawa dai-dai amma kuma tare da dan kankanin kuskure wato Ummu Muhsin Wa Muhsina , a bisa haka ita ma ta shiga cikin kunshin Bonus domin kwazon da s**a nuna babban abin a yaba ne

1. Ummu Muhsin Wa Muhsina

2. Adamu Muhammad Sani

Sai su tura mana numbobinsu domin saka musu kyautarsu.

25/11/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

TAMBAYOYINMU NA YAU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Q1. Kawo cikakken hadisin da ka sani a kan azumi tare da Isnadinsa da larabci

Q.2 Sallar farilla raka'a nawa kake/kike yi a cikin kwana talatin da daya ?

Q3. Kawo sunayen mata biyar wadanda s**a ba da babbar gudunmawa ga addinin musulumci tare da fadar gudunmawar

Q4. Kawo nasarori biyar manya da aka yi lokacin khalifancin Usman (R.A)

Kyautar yau ita ce k**ar haka:

1st. Data 3Gb

2nd. 2Gb

3rd. 1Gb

18/11/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

TAMBAYOYINMU NA YAU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

1. Karanta Hadisi mai zuwa sannan ka yi cikakke kuma gamsasshen bayanin abin da hadisin ke nufi tare da darussan da ya kunsa:

An karbo daga dan Umar Allah shi yarda dasu ya ce; Manzon Allah s.a.w ya k**a kafaduna sannan ya ce: Ka zama k**ar bako a cikin duniya, ko matafiyi a kan hanya kuma dan Umar Allah ya shi yarda dasu yana cewa: Idan ka yi yammaci, to kar ka jiraci safiya, kuma idan ka wayi gari, to kada ka jiraci yamma. Nemi ribar lafiyarka kafin ciwonka, da kuma rayuwarka domin mutuwarka. [Buhari ne ya rawaito shi]

Q2. Ambaci Sunayen Dabbobi 5 da Allah ya ambaci sunayensu a Al-Qurani tare da zuwa da ayoyin da aka ambace su

Q3. Kawo abubuwa manya guda biyar da s**a faru a lokacin Hijira daga maka zuwa madina

Q4. Kawo ayoyi uku inda Allah yake yiwa kafirai martani domin kariya ga Annabinsa Muhammad sallahu alaihi wa sallam

18/11/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

Yau ma inshallahu muna nan tafe muku da gasa da muka saba yi ta tambayoyin musulumci a dai-dai lokacin da muka saba 9:00pm

12/11/2022

Alhamdulillah

Muna godiya ga bayin Allah da suke sa albarka domin karar da junanmu ilimi, Allah ya saka muku da alkhairai

Kuma k**ar yanda na sha fada shi ne kowannenku mai nasara ne, a kadartawa kuma ta ubangiji wadanda s**a sami fitowa su ne :

1st. Hannatu Muhammad

2nd. Yar Amanah

Su biyu ne kadai s**a amsa cikakkiyar amsawa

Saboda wadanda s**a ji sunayensu sai su tura mana numbobinsu ta inbox mu tura musu kyautarsu

Godiya ta musamman ga shugaban wannan gidauniya Ahmad Tijjani Musah da kuma mai jagoranta tare da daukar nauyi Suleiman Isah Wada fatan Allah ya saka muku da alkhairai ya sanya muku a mizani.

11/11/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

TAMBAYOYINMU NA YAU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

1. Karanta Hadisi mai zuwa sannan ka yi cikakke kuma gamsasshen bayanin abin da hadisin ke nufi:

An karbo wannan hadisin daga Abi Ruqayya Tamin dan Ausid Ad-dari Allah madaukakin sarki ya yarda dashi, lalle mazon Allah s.a.w yace β€œAddinni tunatarwa ce” sai muka ce gawa?, Sai Annabi yace β€œga Allah, da kuma littafinsa, da kuma mazonsa, da kuma shuwagabannin musulmi, da kuma al-ummarsu baki daya” [Muslima ya ruwaitoshi]

Q2.Surori nawa ne s**a fara da AlhamdulilLah ? AMBACE SURORIN
a. 5
b. 6
c. 8
d. 4

Q3. WaΙ—anne siffofi Matar Annabi Musa da Ζ΄ar'uwarta s**a gani har s**a labartawa mahaifinsu sahihancin Annabi Musa? Allaha ya bamu labarin siffofin a Qur'an, ambaci gurin
a. Surutu da kyau
b. Ƙarfi da kuri
c. Karatu da kyau
d. Ƙarfi da aminci

Q4. Da wanne abubuwa Allah ya Ι—aukaka Annabi DAUDA da SULEIMAN? Ayoyi biyu mabanbanta sun labarta mana su, ambace su
a. Kudi da lafiya
b. Tsawan rai da 'ya'ya
c. sanin mutane da taimakon su
d. Ilimi da mulki

Kyautar yau ita ce k**ar haka :

1st. 3GB

2nd. 2GB

3rd. 2GB

Sponsored by: MALM. SuleSuleiman Isah WadahSuleiman Isah Wadaa

11/11/2022

A.T.M ISLAMIC FOUNDATION

Yau ma inshallahu muna nan tafe muku da gasa da muka saba yi ta tambayoyin musulumci a dai-dai lokacin da muka saba 9:00pm

Yau kyautar ita ce k**ar haka:

1st. Data 3.0Gb

2nd. Data 2.0Gb

3rd. Data 2.GB

Fatan Allah ya yi mana jagora mu da ku baki daya.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kano-Jos Road
Kano