programming CIKIN harshen HAUSA

programming CIKIN harshen HAUSA

Share

Wannan page din anbudeshi Dan koyar da ilmin programming cikin harshen HAUSA

Photos from programming CIKIN harshen HAUSA 's post 16/02/2025

Hanyar tana da dan tsawo, amma duk ma bukatar yadda ake automating na duk kanin wani abu dakasani wanda yake faruwa akai akai, kuma yana bukatar koda yaushe saika sabuntashi kayi magana domin samo maka hanyar da daza sauka maka ta hanyar amfani da AI(Artificial Intelligence)

Photos from programming CIKIN harshen HAUSA 's post 16/02/2025

Yadda zakai automating na CV da COVER letter a duk lokacin da kakeso cike wani sabon aiki, kawai abunda kake bukata ka kirkiri google form, Lindy.ai account, nantake zakake karbar sabon cover letter da CV da zarar ka cike sabon aiki.
Ga misalin yadda nai automating din CV dina da kuma Cover letter. Sannan na karbi email directly daga Lindy.ai.

03/02/2024

I'm learning Django which is a python web development framework.

02/09/2023

Sati biyu dasuka wuce nasha fama da project na PRINTF, printf built-in function ne a C programming Wanda kusan anfi amfani dashi sama da ko wanne function. Nasarar kirkirar 'printf' naka ta ta'allakane da sanin wadannan concepts din a C programming.
1) Typedef (type definition)
2) Struct (structure)
3) Variadic function, sai Kuma ka hada da
4) Function pointer.
Idan kanasan fahimtar C programming sosai to kayi kokarin sanin yaya POINTER take aiki.

-Namujibril.

09/04/2023

Wannan shine screenshot na Termux dinda mukai amfani dashi.

09/04/2023

Farkon abunda zamu fara koya shine yadda zamuyi amfani da “Terminal” a Linux dinmu ko kuma Termux dinmu.
Dan haka yanzu ga wasu cammands masu sauki da muke bukatar saninsu.
1) pwd – “print working directory”
shi wannan command din ana amfani dashine domin sanin a wanne directory mutum yake aiki, idan ance directory a command line ana nufin “folder” idan mutum yana amfani da “GUI” ma’ana graphical user interface.
2) cd – “change directory”
shi kuma k**ar yadda sunansa ya nuna, yana nufin ka canja daga folder din dake zuwa wata folder din.
3) ls – “List contents in the directory”
Shikuma yana nuna mana dukkanin abubuwan da suke cikin directory din mutum k**a daga kan folders, files da dai sauransu.
4) mkdir – “Make directory”
Da wannan command dinne mutum zai kirkiri folder, sannan ya ajiye abubuwanda yakesan ajiyewa,
5) cp – “Copy”
zaka iya copy na file daga wani directory din zuwa wani da wannan command din na cp.
6) mv – “move or rename”
zaka iya tura file daga current folder dinka zuwa wata mai makon kayi copy nashi, sannan zaka iya amfani da wannan command na “mv” ka sauyawa wani file ko directory suna.
7) rm – “Remove”
Idan kanasan goge file wannan command din shi zakai amfani dashi, amma idan folder kakesan gogewa to dole sai kayi “forcing” nashi, sai command din ya kasance k**ar haka, (rm -rf ).

MISALAI:
1. Da farko zanfara da kirkirar folder wato directory, zan bashi suna NAMU
~$ mkdir NAMU
yanzu na kirkiri directory mai suna NAMU
2) zanyi amfani da cd domin in canza zuwa NAMU directory
~$ cd NAMU
3) tayaya zansan cewa yanzu na canza directory zuwa NAMU? Shine sai muyi amfani da command ls.
~$ ls NAMU
bayan mun danna enter zamuga yanxu muna cikin directory NAMU, kuma zai sauya kala zuwa “Blue” ya danganta da yadda mutum ya tsara terminal din tasa
~/NAMU $
Zakuma mu iya kara kirkirar wani directory din a cikin NAMU directory misali mubashi suna “jibril”
~/NAMU $ mkdir jibril
idan munaso mugane cewa mun kirkiri sabon directory sai muyi amfani da ls.
~/NAMU $ ls
jibril
~/NAMU $
yanzu bari mu canza zuwa sabon folder da muka bude mai suna jibril
~/NAMU $ cd jibril
~/NAMU/jibril $
To idan muka lura za muga cewa directory jibril yana cikin directory NAMU, dan haka daga nan zamu iya komawa duk directory din da mukesan komawa da taimakon cd(change directory)

Note: Muyi sani cewa command line suna da “case sensitive” ma’ana cd ba daidai yake da CD ba, hakana ls ba daidai yake da Ls ba, dan haka yadda aka gansu a karamin bakinsu to a haka mutum zaita amfanindasu.

Akwai screenshot na wasu commad din da mukai amfani dasu zan turasu, amma nayi sune a Termux masu amfani da wayar hannu kenan su zasufi ganewa duk da cewa haka command din yake hatta ga masu amfani da Linux din ko muka Mac.

Sannan littafin "command line" shima zan turashi ga masu bukata sai suyi download dinsa, domin zasu kara samun fahimta sosai.

~Namujibril

03/04/2023

Wannan wadda Akai zagaye itace wadda mutum zaiyi amfani da ita.

Termux | F-Droid - Free and Open Source Android App Repository 03/04/2023

03/04/2023

Kamar yaddai mukai bayani abaya cewa zamu nuna yadda za’ai installing na Linux da Termux.
Yanzu zamu fara da shi Linux din domin masu amfani da computer.

1)Linux installing(Ubuntu)
zaka iya bin wanna link domin sanin yadda zakai installing nashi step by step
https://ubuntu.com/tutorials/install-ubuntu-desktop
ko kuma ta youtube a wannan link din.
https://www.youtube.com/watch?v=oNEwEQ0uU1Y
ko kuma kasamu wanda yake dashi yai ma installing nashi cikin sauki, ko kaje kasuwar computer duk ba laifi bane.
2)Termux
Su kuma masu amfani da Android zasu iya ziyartar playstore suyi searching na “Termux” ko kuma subi wannan link din domin dakkota kai tsaye ba tare da samun wani tsaiko ba.
https://f-droid.org/en/packages/com.termux/
Ga masu amfani da termux zanyi short video wanda zai nuna yadda zaku dakkota domin tana zuwa da ma bam-bamta version wanda haka zai iya rikita wasu.

To yanzu mu kaddara koya ya dora ubuntu linux da kuma termux akan system dinshi, sai fara programming kenan.
Karku manta wadannan basune dole sai dasu mutum zai fara programming ba, amma dai a shawarce nake ganin dasu yaka mata mutum ya fara tukunnan inyaso daga baya sai ya kara update/upgrade nasu.

Kamayarda nayi magana akan “Text editor” wadda itace zata bamu damar rubuta “code” ko "program" suma suna da yawa amma zanyi amfani da wadda ake kira “Vim” ko “vi” a takaice, idan kana da wadda kake ganin zakayi amfani da ita to babu laifi zaka iya yi da ita.

Dan haka darasinmu na gaba zamuyishine akan
yadda zamuyi installing “vim” akan wayarmu ko kuma “Ubuntu” domin fara programming.

Sanin wannan basic din yana da matukar mahimmanci dan haka kada kaga cewa har yanzu bakaji anfara maganar su Python, Javascript, c++ da sauransu ba, idan kuna biye damu suma sannu a hankali zamuzo kansu daya bayan, kai harma dasu HTML & CSS.

~Namujibril

Termux | F-Droid - Free and Open Source Android App Repository Terminal emulator with packages

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kano
Kano