02/02/2025
The Mariana Trench 🇲🇵 Kwarin Ruwa Ne Mafi Zurfi A Duniya Kuma Mafi Duhun Waje A Wannan Duniya
Mariana Trench rami ne na teku da ke yammacin tekun Pasifik, (tekun Pasifik shi ne teku mafi girma a duniya), wajen ya na kimanin kilomita 200 (124 mi) gabas da tsibiran Mariana; shi ne waje mafi zurfin ruwa a duniya, (waje mafi zurfi a teku a na kiransa Deep Challenger). Ya na da zurfin mita 10,984 kimanin taku (kafa 36,037), zurfin nasa, da za a jefa dutsen da yafi kowanne dutse tsayi a duniya (Mouth Everest) zan shaye kansa, (Mouth everest tsayin mita 8,000 da dan motsi kadan ne).
Jirgin masu bincike na Burtaniya Challenger II ne ya fara gano ramin a cikin shekarar 1951. Don Walsh da Jacques Piccard su ne mutanen farko da s**a je ainihin wajen zurfin. Mai shirya fina-finan Amurka kuma mai binciken teku dan kasar Kanada James Cameron (wanda shi ne ya shirya fim din Titanic) shi ma ya yi tafiya shi kaɗai a cikin ramin a cikin shekarar 2012.
A ranar 10 ga Nuwamba, 2020, Fendouzhe dan kasar Sin (China) mai wasan ninkaya, yayi nutson da ya kusa kai karshen zufin kwarin na Mariana Trench, ya shiga zurfin da ya kai mita 10,909 wato taku (35,791).
A cikin zurfin ruwan Mariana akwai tsananin duhu, da tsananin zafi, saboda karancin iskar (Oxygen). Duk da haka, akwai halittu na musamman da ke rayuwa a cikin ruwan, k**ar kifaye da na fassara su da hausa (kifayen fatalwa), da manyan-manyan wasu halittu masu haske a idanunsu, wasu kuma a kan goshinsu, (Allah ya haliccesu da hasken ne cikin hikimarsa saboda tsananin duhun ruwan). Bayan wannan akwai halittu iri-iri, wadanda ba a taba gani ko jin labarin su ba, a wannan duniya, domin akwai wata halitta da aka taba ganowa a cikin shekarar 2015 mai siffar miciji da kafafuwa guda 6 da tsayi k**ar (Dragon 🐉), kana kuma ga wasu halittu musu kawuna shigen irinna yan adam, baya ga wasu dabbobi masu k**a da raguna amma kansu na kifaye ne.
A shekarar 2023 Masana kimiyya sun gano wata sabuwar kwayar cuta da ke a nisan mita 8,900 a cikin