24/10/2025
010. Annabir-Rahama صلى الله عليه وسلم
Da Sunan Allah mai Rahama Mai Jinkai, tsira da amincin Allah s**ara tabbata ga Annabi Muhammad dan Abdullahi.
النبي أولى بالمؤمنين من أنفسهم وأزواجه أمهاتهم وأولوا الأرحام بعضهم أولى ببعض في كتاب الله من المؤمنين والمهاجرين إلا أن تفعلوا إلى أوليائكم معروفا كان ذلك في الكتاب مسرورا.
(Annabi shi ya fi cancanta ga muminai fiye da kansu; matansa kuma iyayensu ne. Dangi na zumunta kuma shashinsu ya fi kusanci daga wani shashi a cikin Littafin Allah daga kusancin muminai da masu Hijira, sai dai idan za ku aikata wani alheri ne ga masoyanku "muminai". Wannan ya kasance a rubuce a cikin Lauhul Mahafuz)
- Gidan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم:
Manzon Allah a Rayuwar sa a Makka sannan ya auri Nana Khadija a lokacin yana da shekara Ashirin da Biyar (25), Nana Khadija ta na da shekara Ashirin da Takwas (28), ta kasance Matar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ta farko, bai auri Wata Mace ba sai Bayan Rasuwar ta.
Nana Khadija ta haifawa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم 'ya'ya Shida (6)
Mazan Sune:
Alkasim da Abdullahi, duka sun Rasu a yarintarsu.
Matan sune:
Zainab, Rukayya, Ummukulsum da Fadima.
1. Zainab ta auri Abil Ãs dan Rabi'a, s**a rabu Bayan ya Musulunta aka Maida auren nasu.
2. Rukayya da Ummukulsum sun auri Usman dan Affan Bayan Rasuwar Rukayya sai aka aura masa Ummukulsum.
3. Fadima ta auri Aliyu bin Abi Dalib Bayan Yakin Badar da Uhud, ta haifi Alhasan, Alhusain, Zainab da Ummukulsum.
- Sauran Matan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم:
Allah ya hallatawa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم auren Mata Sama da guda Hudu (4), Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya auri Mata Goma sha Uku, Biyu sun Rasu a Rayuwar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, sannan Biyu Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya rabu dasu kafin su tare, Tara (9) daga ciki sune s**a yiwa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم takaba (Idda).
- Matan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم sha Daya:
1. Khadija yar Kuwailid.
2. Saudat yar zam'a, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shawwal shekara ta Goma da Annabta, bayan Rasuwar Khadija da Wata daya, ta Rasu a Madina a shekara ta Hamsin sa Hudu (54).
3. Aisha yar Abubakar, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shawwal shekara daya da auren Saudat, kafin Hijira da shekara Biyu da Wata Biyar, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya Aure ta Budurwa, ta Rasu a Madina shekara ta Hamsin da Takwas (58).
4. Hafsat yar Umar, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Uku Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Arba'in da Biyar (45).
5. Zainab yar Khuzaima, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Hudu Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Bayan auren ta da Wata Uku.
6. Hindu yar Abi Umayya, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Hudu Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Hamsin da Tara (59).
7. Zainab yar Jahash, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Biyar Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Ashirin (20), ta kasance Matar zaid sai ya saketa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya Aureta.
8. Juwairiyya yar Harisa, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Shida Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Hamsin da Biyar (55).
9. Ramlat yar Abi sultan, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Bakwai Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Arba'in da Hudu (44).
10. Safiyya yar Huyyayi, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Bakwai Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Hamsin da Biyu (52).
11. Maimuna yar Harith, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya aureta a shekara ta Bakwai Bayan Hijira, ta Rasu a Madina Shekara ta Sh*ttin da Uku (63).
- Bayin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Mata:
1. Mariyatul Kibdiyya, itace ta haifawa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Dan sa Ibrahim.
2. Raihana yar Zaid.
02/5/1447
24/10/2025
✒ Usman Saminu Nuhu