10/06/2025
Ina farin cikin sanarda al'umma cewa Noor English Classes ta buɗe ajin Reading & Writing Class.
Menene Reading & Writing Class
Wannan aji ne da zai bada mentoring akan reading and writing skills, tare da yin karatun da rubutun a aikace.
Ga Suwa Aka Samar da Ajin?
Idan kai ɗalibin secondary ne, ko kwaleji ko jami'a amma karanta littafi na ba ka wahala sosai ko kuma kana gwada yin karatun da rubutun amma tsinta ka yi, ba wai koyanshi ka yi ba a makaranta ko gaban malamai ba, wanda tasa kana fama da ƙalubale daban-daban, to wannan ajin na ku ne!
Yaushe da Yaushe Za a Ringa Yin Ajin?
Za'a ringa gabatar da wannan ajin a ranakun Litinin da Talata daga ƙarfe 7pm – 9pm a makarantar Noor dake no 145 Tal'udu Opposite B-Medix 24hrs Layin dake Jikin Gidan Alaramma Kano.
Akwai Online:
Ei, akwai online. Idan shi ka ke so, ka yi magana ta WhatsApp da lambar da ke ƙasan wannan rubutun. Akwai tsarinsa.
Duration fa?
Zangon karatun wata uku ne (3 months).
Matakai (Levels) Nawane da Ajin?
Akwai matakai guda biyu a yanzu haka: Reading & Writing Learner da kuma Reading & Writing Intermediate.
Ya Batun masu son koyon rubutun Adabi?
Duk wanda ya ke son ƙwarewa sosai akan iya karatun littafi cike da skills da sanin makama sannan ya na son gogewa a rubutu tun daga formal writing izuwa creative writing, tofa gaskiyar zance wannan ajin ne nasa.
Menene Requirements ɗin Ajin?
Ana bukatar wanda zai shiga aji ya zama yana da basic English kuma yana iya kwatanta karatun littafi koda baya sauri amma ya zama yana fahimtar Turanci kuma yana iya rubuta shi.
Mutun Nawa Kuke Sawa a Aji?
Mutum 15 kacal mu ke buƙata a yanzu haka. Kuma mun fara registration kai tsaye.
Form da register: 15k
Materials: 15k
Materials su ne: Reader's Handbook da Write Source. Idan kana Reader's Handbook, za ka siyi Write Source 8k only. Wannan ga ɗaliban makaranta kenan.
Me ku ke jira? Ku tuntuɓemu ta: 09044448060 domin booking ɗin slots ɗinku kafin ya cika.
This is a very serious class for those interested in changing their lives!
Please share!