05/03/2026
Today is special day
Today is my birthday 🎂 May god bless you with all the happiness, love and success. Wish you a very Happy Birthday! 🎁Nasir Bashir@highlightFollowingNANSNANS ZONE DNansforumNans Voice Kaduna
06/11/2025
DUK MAI SONKA DA GASKIYA DOLE WATARAN YAYI YABO WATARAN YAYI S**A INDAI YANA SO KU HADU A ALJANNA YAU DAI YABONE
Hakika Abunda Sen. Barau I. Jibrin yayi na Yunkurin sabunta masallacin matafiya wanda akafi sani da masallacin , Yunkurine na ginawa kansa gida A Aljanna, kuma Alamace ta cikakken Imani, kuma ina kira ga Sauran jagorari suyi koyi dashi.
Ga Hujja daga cikin Al-Kur’ani mai girama da Hadisan Manzon Allah s.a.w
Acikin Suratu At-Tawbah aya ta (9:18) Allah madaukakin sarki yana cewa
إِنَّمَا يَعْمُرُ مَسَاجِدَ اللَّهِ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ...
Ma’ana: “Lalle ne waɗanda suke ginawa (ko kula da) masallatan Allah su ne waɗanda s**a yi imani da Allah da ranar ƙarshe...”
Wannan aya tana nuna cewa gina masallaci alama ce ta cikakken imani da kyakkyawar niyya ta ibada. “Ya’muru” a nan na nufin ginawa, ko gyarawa, da kula da masallaci.
Hujja daga Hadisan Manzon Allah s.a.w
1. Hadisin Uthman bn Affan (RA)Acikin littafin – Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim
قال رسول الله ﷺ:
"من بنى لله مسجداً بنى الله له مثله في الجنة."
Ma’ana: “Wanda ya gina wa Allah masallaci, Allah zai gina masa makamancin sa a Aljanna.”
(Bukhari, Hadisi na 450; Muslim, Hadisi na 533)
Amma wanda ya gina don neman Yardar Allah ba don isaba Allah ya sakawa Sanata Barau da Alkhairi ya kuma biya masa bukatarsa ta Alkhairi A duniya da lahira
Barau I. Jibrin
Dan Afirka
Saminu Uba Maiturare
Shiek Yusuf Abu Sumayya
Auwal Uba Maiturare
Ishaq Adam Rijiyar Zaki
Basiru Yusuf Shuwaki
DSports
18/09/2025
APC YOUTH PROGRESSIVE CONGRESS GWALE (AYPC)
Kamar yadda jam'iyyar APC ta raba taki ga ƴaƴanta cikin ikon Allah wannan ƙungiya mai suna a sama itama ta rabauta da takinta wanda ta karɓa a jiya ta hannun jigo shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Gwale, Hon Umar Yusuf Umar (Kashe Kwabo) Ɗan masanin siyasar Gwale.
Wanda wasu da daga cikin shugabbanin APC Youth Progressive Congress Gwale s**aje s**a karɓa a madadin ƴan ƙungiya gaba ɗaya.
Ƙungiyar matasa masu son ganin nasarar APC a kowanne mataki, ta APC Youth Progressive Congress Gwale da yawun kowane member muna godiya da wannan kaɓakin arzki da Jam'iyya tayi mana, Allah ya bamu Nasara da juriya dan samun Nasarar APC.
Sign
Comrd Khalifa Salihu Bashir
A.g Director Media AYPC
26/08/2025
Acigaba da yaudarar mutane da gwamnatin Kano takeyi ta Bangare daban-daban yauma mun samu labarin Karin kudin makaranta na kwalejin legal bayan samun Karin kudi da akayi a Jami'ar Northwest
Karatu a jahar kano Yana Nema ya gagari Yan garin ballantana Baki masu shigowa Neman ilimi
Lokacin tsohuwar gwamnatin Dr abdullahi Umar ganduje anayin registration a legal akan kudi Naira Dubu Shatakwas 18k wannan gwamnatin tace Basu iya ba,s**ai karyar zasu bada ilimi kyauta Ashe abun yaudara ce
Yau an wayi gari Daliban Kano masu karatu a legal zasu biya kudin registration 33k maimakon 18k
Da haka muke sanar daku cewa wannan gwamnatin ta kano bata kishin ilimi bata son cigaban al'ummar Kano
Babu abunda s**a Saka a gaba sai sata da kwashe dukiyar talakawa
Comr.Lamma