Risala Charity Foundation

Risala Charity Foundation

Share

ترحب بكم مؤسسة الرسالة الخيرية في أنشطتها العلمية والثقافية.

03/10/2025

“An ruwaito daga al-Hasan al-Basri (Allah ya jikansa) wani labari sananne game da falalar istigfari, wanda aka saba samu a cikin littattafan wa’azi. Ma’anarsa dai sahihiya ce kodayake isnad ɗinsa ba ya rasa magana a kansa. Takaitaccen labarin shi ne:

Wani mutum ya zo wurin al-Hasan al-Basri ya ce:
“Ya Aba Sa’id, sama ba ta saukar da ruwan sama ba.”
Sai ya ce: “Ku roƙi Allah gafara.”

Wani ya zo ya ce: “Ni fa talaka ne.”
Sai ya ce: “Ku roƙi Allah gafara.”

Na uku ya zo ya ce: “Matar tawa ba ta haihuwa.”
Sai ya ce: “Ku roƙi Allah gafara.”

Sai wani daga cikin masu halarta ya ce:
“Duk wanda ya zo maka yana kuka da halinsa, kana cewa masa: ‘Ku roƙi Allah gafara!’”

Sai al-Hasan ya amsa da cewa:
“Ba daga kaina nake faɗa ba, Allah Maɗaukaki ne ya faɗa a cikin Littafinsa:
﴿Faqultu istaghfirū rabbakum innahu kāna ghaffārā * Yursil issamā’a ‘alaikum midrārā * Wayumdidkum bi-amwālin wa-banīna wayaj‘al lakum jannātin wayaj‘al lakum anhārā﴾ (Nūḥ: 10-12).

Wannan labari ana rawaitonsa ne don nuna cewa istigfari ba kawai don gafarar zunubi ba ne, har ila yau hanya ce ta samun arziki, albarka, da kawar da masifu. Haka kuma yana bayyana yadda al-Hasan al-Basri ya danganta nassosin Alƙur’ani da ainihin rayuwar mutane.”

03/02/2025

🌙DAUSAYIN RAMADAN 1446🌙

Ina mai neman rabauta a watan Ramadan⁉️
Ina mai son ya kasance cikin waɗanda s**a ci nasara a Ramadan⁉️
Ina mai son ya kasance cikin waɗanda Allah zai ƴanta su daga wuta zuwa aljanna⁉️

Zo ga amsar tambayoyinka📑

Cibiyar Al-Wesam ta samar da wannan shiri domin ƙoƙarin taimakawa ƴan uwa su yi shiri domin tunkarar azumin Ramadan, da kuma cikin Ramadan ɗin.

✨Shirin zai taimaka wajen kula ayyukan ibada tare yin su da wani irin salo da zai ka riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar, (ibada daga cikin zuciya, ba a iya gaɓɓai ba).

✨Shiri ne da zai taimake mu domin mu gyara tsakanin mu da Ubangiji domin tunkarar azumin Ramadan

✨Shiri ne da zai yi ƙoƙarin haɓaka imanin da gyara ibadun domin mu riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar.

✨Shiri ne da ya shafi dukkanin ɓangarorin imani, tarbiyya da ibada, a cikin rayuwar Musulmi.

🗒️Wannan shiri ya ƙunshi abubuwa kamar haka:

1- Wuridin Karatun Alƙur'ani Na Kullum📓
2- Tafsirin Izun ƙarshen Alƙur'ani (Suratul A'ala Zuwa Nasi)📖
3)- Jerangiyar darussa na sauraro 🎤
4- Ramadan Calendar 📅
5- Taƙaitattun rubuce-rubuce📝
6- Azkar na safiya da maraice🗒️
7- Tuni a lokutan aikata ibadu⏰

Shirin zai gudana tsawon kwanaki 45

📅Za'a fara a tsakiyar watan Sha'aban 15/8/1446

📅Za'a kammala ƙarshen watan Ramadan zuwa 29/9/1446

Da wasu abubuwa masu yawa wanda za su zo in sha Allah.

Domin babiyar wannan shiri👇🏼

WhatsApp 👇🏼
https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7

Telegram👇🏼
https://t.me/dausayinramadan

27/11/2024

Sanarwar Muhadara ta Mata

Mai taken: Gudunmawar Mata wajen gina Al'umma

Mai gabatarwa: Dr. Suleiman Mahmud Al-Azhary

Wuri: Masjid Khatimir Rusul, Ruwan Sai farawa, kusa da gidan gas titin kureke.

Lokaci: 10:00 na safe

Domin karin bayani: 09035033049, 09037291177

16/10/2024

Kulawa Da Safiya Da Maraice

A shawarce idan kana so ka daina fashin zikirin safiya da maraice to ka sanya zikirin safiya bayan sallar asuba, shi kuma zikirin maraice kuma bayan sallar la'asar.
Idan ka idar da sallah kar ka bar wajen sai ka karanta zikirin sannan zaka tashi.

Wannan zai taimaka sosai wajen kula da zikirin

23/09/2024

Zaku iya samun littafan مركز تفسير a bajakolin littafai na Riyadh na bana 2024
https://tafsir.net/uploads/publications/66eed5935a58a.pdf

Dr Sulaiman Mahmud Al-Azhari 31/12/2023

🔖Complete Karatuttukan Dr. Sulaiman Mahmud Abdullah Al-Azhary

1) Attuhfatus saniyyah
2) Arba'una Hadis
3) Alfiyatu Ibn Malik
4) Manhajus Salikeen
5) Mukhtasar Minhajil Qasideen
6) Mukhtasar Suratur Rasuul
7) Mukhtasar Sahih Muslim
8)Maqsuratu Ibn Duraid
9) Al-Wabilussayyib
10) Ramadan Tafseer 2021, 2022 & 2023
11) Tafsirin Juz'u Amma
12) Albahrurra'iq
13) Muhadara
14) Khudbah

✒️Wasu Complete ne wasu kuma ana kan yin su

🔖Zaku iya samun su a wannan link ɗin na ƙasa 👇

https://darulfikr.com/sc/861

📌Ka yaɗa domin muyi tarayya a cikin ladan

Dr Sulaiman Mahmud Al-Azhari Darulfikr.com is an Islamic website that provides a comprehensive resource for Muslims to deepen their understanding of Islam. It focuses on promoting the values of Islam and spreading the message of peace, love, and unity.

Photos from Risala Charity Foundation's post 26/12/2023

Tarihin Manzon Allah (SAW) a takaice cikin takardu guda huɗu 6 kacal 👇

Ya kamata ku haddace shi yana da matuƙar amfani 💯📚

©️ Abdullahi Daurawa

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kano