Ƙasashen Duniya

Ƙasashen Duniya

Share

Ƙasashen Duniya shafi ne da zai riƙa ba ku bayanai kan ƙasashen duniya, harsuna, addinai, dabbobi, da sauran abubuwan al'ajabi da tarihi.

20/09/2025

Gandun Dabbobi na Maasai Mara a ƙasar Kenya

20/09/2025

'Yan gida ɗaya masu k**a ɗaya

Yan matan gidan Dibaba ke nan daga ƙasar Habasha. Dukkansu 'yan wasan gudu ne. Kuma kowacce daga cikinsu tana da lambar yabo na wasa a matakai daban-daban na duniya.

Uku daga ciki uwa ɗaya ta haife su, ragowar biyun kuma 'ya'yan 'yan uwan mahaifinsu ne.

20/09/2025

Saɓanin yadda muka ɗauki cin miyar kuka ko amfani da wani abu daga jikin bishiyar a matsayin talauci ko ƙauyanci, su mutanen ƙasar Madagaska sun ɗauke ta a wani ɓangare na rayuwarsu. Suna yin abubuwa da yawa da ita. K**a daga abinci, abubuwan sha, magani, kayan amfanin gida, har ma da tufafi suna saƙawa daga jikin ɓawon bishiyar.

18/09/2025

Yara 'yan ƙabilar Nama. Ana samunsu ne a ƙasashen Namibiya, da Afirka ta Kudu, da kuma Botswana.

Photos from Ƙasashen Duniya's post 18/09/2025

Za a fara koyar da yaren Cananci a makarantun sakandare na Najeriya.

Sakataren ilimi na Birnin Tarayya Dr. Ɗanlami Hayyo ne ya ba da sanarwar a ranar Talatar da ta gabata.

Ya bayyana haka ne a yayin buɗe wata cibiyar ilimi da wayar da kai ta ƙasar Sin. Wadda kamfanin gine-gine na ƙasar Sin CCECC ya gina a sakandaren gwamnati ta Tudun Wada a birnin Abuja.

18/09/2025

'Yan matan ƙabilar Amhara ke kiɗa yayin wani shagali.

Amhara ita ce ƙabila ta biyu da ta fi yawan al'umma a ƙasar Habasha/Itofiya. Kuma yarensu na Amharanci (Amharic) shi ne yaren da hukuma ta zaɓa a yi amfani da shi a duk makarantu da hukumomin ƙasar

Photos from Ƙasashen Duniya's post 17/09/2025

An ɗauki wannan hoton ne a shekarar 1973, lokacin da shugabannin ƙasashe rainon Ingila suke taro a ƙasar Kanada.

Janar Yakubu Gawan ne yake gaisawa da wani yaro ɗan shekara ɗaya da watanni. Ɗa ne ga Firaministan ƙasar Kanada a lokacin.

Sunan yaron Justin Pierre Trudeau. Kuma shi ne ya zama Firaministan ƙasar Kanada na 23 a shekarar 2015, sannan ya sauka a farkon wannan shekarar da muke ciki.

Photos from Ƙasashen Duniya's post 16/09/2025

Mutanen ƙabilar Dinka ta ƙasar Sudan ta Kudu. Suna daga cikin mutane mafiya tsawo a duniya.

16/09/2025

Nau'in gidajen mutanen ƙabilar Barbar da ke zaune a kusa da tsaunukan Atlas a ƙasar Maroko

Photos from Ƙasashen Duniya's post 16/09/2025

A shekarar 1978 ne mawaƙi Fela ya auri mata guda 27 a rana ɗaya. Hakan ya biyo bayan ƙonawa tare da rushe masa gidansa da sojoji s**a yi bisa zargi daban-daban. Daga ciki akwai maganar yana sato 'yan mata suna zama tare da shi a matsayin 'yan amshi da rawa ba tare da yardar iyayensu ba.

Rushe gidan ya sa sun rasa wurin zama. Hakan ta sa ya yanke shawarar auren su domin ya samar wa kansa da 'yan matan kariya. Bayan ya nemi amincewar su ne aka sa ranar aure.

Malaman addinin gargajiya na Yarabawa 12 ne s**a ɗaura auren a watan Fabrairu na shekarar 1978. Kuma an ɗaura auren a wani hotal a gefen birnin Legas.

Bayan an gama hidimar ɗaura auren ne ya kwashe su duka s**a tafi yawon cin amarci a ƙasar Gana.

A shekarar 1984, masu mulki sun ɗaure Fela a gidan yari. Bayan fitowarsa ne a shekarar 1986 ya saki duka matan. Inda ya bayyana cewa zaman aure yana jawo hassada da son kai tsakanin ma'aurata. Sai dai wasu daga cikin matan sun cigaba da zama tare da shi har zuwa mutuwarsa.

Ɗan'uwansa ya shaida wa duniya cewa cutar Sida ce ta kashe Fela. Amma matar da ya bari ta musanta hakan.

16/09/2025

Barka da safiyar Talata. Yanzu ƙarfe shida a garin Ɗan Zabuwa da ke jahar Kano, ƙarfe sha biyu na daren Litinin a birnin Bogota na ƙasar Kolombiya. Yayin da kuma ƙarfe 10 da minti 45 a birnin Katmandu na ƙasar Nepal.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Kano
700104