Al-madinah Tahfizul Qur'an Group Of Schools Dawakin tofa

Al-madinah Tahfizul Qur'an Group Of Schools Dawakin tofa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al-madinah Tahfizul Qur'an Group Of Schools Dawakin tofa, School, Dawakin Tofa, Between General Hospital and medical store, Kano.

05/12/2025

Jumu'ah Mubarak

Al-Madina Staff Seminar 2025 11/09/2025

Al-Madina Staff Seminar 2025 Enjoy the videos and music you love, upload original content, and share it all with friends, family, and the world on YouTube.

06/06/2025

Eid Mubarak
Taqabbbalallahu Minna Wa Minkum

29/05/2025

FALALAR GOMAN FARKO NA WATAN ZUL-HIJJAH DA NAU’O’IN IBADA DA AKE YI A CIKINSU

✍ Sheikh Prof. Ahmad Bello Dogarawa

SHIMFIDA:
Bismillahir Rahmānir Rahīm. Alhamdu lillah. Wassalātu was Salāmu alā Rasūlillah, wa Ālihi wa Ashābihi wa man wālāh.

Bayan haka:

Wannan rubutu ya kunshi bayanai game da falalar kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah da kuma nau’o’in ibada da ya kamata a shagaltu da su a cikin wadannan kwanaki masu albarka. Ina rokon Allah Yasa rubutun ya zamanto mai amfani gareni da kuma ‘yan’uwa Musulmi baki daya.

FALALAR KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZUL-HIJJAH:

Goman farko na watan Zul-Hijjah su ne ranakun da s**a fi sauran ranakun duniya falala, kuma lokaci ne na yawaita nau’o’in ibada ga Allah (Mai girma da daukaka).

A cikin Alkur’ani, a suratul Hajj, aya ta 28, Allah (Mai girma da daukaka) Ya ce: “Kuma su ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu”. Bukhāri ya ruwaito cewa Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ya ce, ‘kwanaki sanannu sune kwanaki goma na farkon watan Dhu Hijjah’. Haka kuma a suratul Fajr, aya ta 1-2, Allah (Madaukaki) Ya yi rantsuwa da lokacin fitowar alfijir da kuma darare goma. A cikin littafinsa na tafsiri, Ibn Kathīr ya ambaci cewa Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ya fassara dararen da “darare goma na farko cikin watan Zul-Hijjah”.

Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya tabbatar da fifikon wadannan ranaku akan sauran ranaku na duniya baki daya kuma ya bayyana cewa yin kyawawan ayyuka a cikinsu ya fi soyuwa ga Allah (Mai girma da daukaka) fiye da sauran ranaku.

Bazzār ya ruwaito Hadisi daga Jābir dan Abdullah (Allah Ya yarda da su) daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
أَفْضَلُ أَيَّامِ الدُّنْيَا أَيَّامُ الْعَشْرِ
“Mafi falalar ranakun duniya sune ranakun goma (na farkon watan Zul-Hijjah).”

Haka kuma Abu Dāwud da Tirmidhī da Ibn Mājah sun ruwaito Hadisi daga Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
مَا مِنْ أَيَّامٍ الْعَمَلُ الصَّالِحُ فِيهِنَّ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ مِنْ هَذِهِ اْلأيَّامِ الْعَشْرِ، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ! وَلا الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ؟! فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: وَلا الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، إِلا رَجُلٌ خَرَجَ بِنَفْسِهِ وَمَالِهِ فَلَمْ يَرْجِعْ مِنْ ذَلِكَ بِشَيْءٍ
“Babu wadansu ranaku da kyawawan ayyuka s**a fi soyuwa ga Allah fiye da wadannan kwanaki goma”. Sai (Sahabbai) s**a ce: Ko jihadi saboda Allah? Ya ce: “Ko jihadi saboda Allah, sai dai mutumin da ya fita (don yin jihadi), yana mai ba da kansa da dukiyarsa saboda Allah, kuma bai dawo da komai ba daga cikinsu.”

A cikin wata ruwayar, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu wani aiki da ya fi tsarki a wajen Allah kuma ya fi girman lada fiye da (aikin) alheri da (mutum) zai yi a goman (farko na watan) Layya…”

A cikin goman farko ake samun ranar Arfa wacce a cikinta Allah (Mai tsarki da daukaka) Ya fi yawaita ‘yanta bayinSa daga wuta kuma Yake yabon bayinSa wadanda suke tsayuwar Arfa a wannan rana. Muslim ya ruwaito Hadisi daga Nana Ā’isha (Allah Ya yarda da ita), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
ما مِن يَومٍ أَكْثَرَ مِن أَنْ يُعْتِقَ اللَّهُ فيه عَبْدًا مِنَ النَّارِ، مِن يَومِ عَرَفَةَ، وإنَّه لَيَدْنُو، ثُمَّ يُبَاهِي بهِمِ المَلَائِكَةَ، فيَقولُ: ما أَرَادَ هَؤُلَاءِ
“Babu wata rana da Allah Ya fi yawaita ‘yantar da bayinSa daga wuta kamar ranar Arfa.”

Haka kuma, a cikin wadannan kwanaki ne ake samun ranar goma ga wata wacce Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya bayyana ta a matsayin mafi girman ranaku a wajen Allah. Abū Dāwud ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi dan Qurt (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
إِنَّ أَعْظَمَ اْلأَيَّامِ عِنْدَ اللَّهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى يَوْمُ النَّحْرِ، ثُمَّ يَوْمُ الْقَرّ
“Mafi girman ranaku a wajen Allah (Mai tsarki da daukaka) ita ce ranar (sallar) Layya, sannan washegarinta (ranar sha daya ga wata).”

Daga Hadisai da s**a gabata, za a fahimci matsayin wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah, da falalarsu, da kuma alherin da ke tattare da shagaltuwa da kyawawan ayyuka a cikinsu.

Magabata sun kasance suna kokari wajen ganin sun ci moriyar wadannan ranaku ta hanyar jajircewa wajen aikata nau’o’in ibada. Misali, Dārimī ya ruwaito cewa “Abdullahi dan Jubair (Allah Ya jikansa) ya kasance idan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah s**a zo, yana matukar dagewa da jajircewa (wajen yin ibada) har ma kamar ba zai iya ba.” Haka kuma, a cikin At-Tabsirah, Ibnul Jauzī ya ruwaito daga Abu Uthmān An-Nahdī cewa “Magabata sun kasance suna girmama kwanaki goma guda uku: goman farko na Zul-Hijjah da goman karshe na Ramadān da goman farko na Al-Muharram.”

Malamai sun yi maganganu mabanbanta game da kwanakin da s**a fi fifiko tsakanin goma na farkon watan Zul-Hijjah da kuma goman karshe na Ramadan. Bayan sun bayyana dalilai da kowane bangare na Malamai ya dogara da su, Ibn Taimiyyah da Ibnul Qayyim sun rinjayar da cewa darare goma na karshen watan Ramadān sun fi dukkan dararen duniya alheri, kasancewar sun kunshi Lailatul Qadri; su kuma ranaku goma na farkon watan Zul-Hijjah sun fi dukkan sauran ranakun duniya alheri, kasancewar sun kunshi ranar Arfa.

NAU’O’IN AYYUKAN ALHERI A GOMAN FARKO NA ZUL-HIJJAH:

Ibn Rajab, a cikin littafin ‘Latā’iful Ma’ārif’ da Ibn Taimiyyah, a cikin ‘Majmū’ul Fatāwa’ da wasu Malamai masu yawa sun bayyana wasu daga cikin nau’o’in ibada da ya kamata Musulmi ya mayar da hankali kuma ya dage wajen aikatawa a cikin kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah kasancewar Hadisai ingantattu sun tabbatar da lada da kuma falala da ake samu idan an yi su. Daga cikin ayyukan alheri da kuma neman kusanci zuwa ga Allah da ake yi a wadannan ranaku, akwai:

1. Azumin Arfa:

Hadisai ingantattu sun tabbatar da falalar yin azumi a ranar Arfa, wato, ranar tara ga watan Zul-Hijjah, ga wanda ba ya cikin ayyukan Hajji. Muslim ya ruwaito Hadisi daga Abu Qatādah (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Azumin Arfa, ina fatan ya kankare (zunuban) shekarar da ta gabata da wacce za ta zo.” A ruwayar Ibn Mājah daga Qatādah dan Nu’umān (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya azumci ranar Arfa, za a gafarta masa (zunuban) shekarar da ta wuce da wacce za ta zo.”

2. Azumi a cikin Kwanaki Takwas na Farkon Watan Zul-Hijjah:

Hadisin da Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ya ruwaito game da falalar kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah ya tabbatar da cewa kyawawan ayyuka sun fi soyuwa ga Allah a cikin wadannan ranaku. Babu shakka, azumi yana daya daga cikin mafi alherin kyawawan ayyuka da za a iya yi don neman lada da samun kusanci zuwa ga Allah (Mai girma da daukaka) a cikin wadannan kwanaki. Bisa la’akari da wannan Hadisi, za a iya yin azumi a farkon watan Zul-Hijjah, tun daga ranar daya ga wata har zuwa takwas ga wata, daga nan kuma a yi azumin Arfa a ranar tara ga wata.

Banda ma Hadisin Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su), kwadaitarwa game da yin azumi cikin kwanaki takwas na farkon watan Zul-Hijjah ta zo karara cikin wani Hadisi. Abu Dāwud da Nasā’ī sun ruwaito daga Hunaydah dan Khālid daga matarsa cewa wadansu daga cikin matan Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) sun ce: “Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya kasance yana azumi cikin kwanaki tara na (farkon watan) Zul-Hijjah, da ranar ‘Āshūrā, da kwanaki uku a cikin kowane wata, da kuma ranakun litinin da alhamis na kowane wata.” Sheikh Albānī ya bayyana ingancin hanyar da aka ruwaici Hadisin a cikin Sahīh Sunan Abī Dāwud.

Duk da cewa akwai Hadisi wanda Muslim ya ruwaito daga Nana Ā’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “ban taba ganin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi azumi a goman farko na watan Zul-Hijjah ba”, Imām An-Nawawi a cikin littafin Al-Majmū’, da Ibn Rajab a cikin Latā’iful Ma’ārif, da Ibn Hajar a cikin Fathul Bārī, da Ash-Shaukānī a cikin Naylul Awtār, da wasu Malamai da yawa sun rinjayar da mustahabbancin yin azumi a cikin kwanaki takwas na farkon watan Zul-Hijjah, ko dai saboda Hadisin Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ko kuma saboda la’akari da ka’idar gabatar da Hadisin da ya tabbatar da hukunci akan wanda ya kore hukuncin.

Haka kuma, ruwayoyi da aka samu daga wasu Sahabbai da Tābi’ai cewa suna yin azumi a farkon watan Zul-Hijjah na daga dalilai da suke karfafa Hadisin Hunaydah dan Khālid. Misali, a cikin littafin Latā’iful Ma’ārif, Ibn Rajab ya bayyana cewa Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya kasance yana yin azumi a cikin goman farko na Zul-Hijjah.

Ba dole ne a azumci dukkan ranakun ba. Gwargwadon abinda mutum zai iya, shi ne zai yi. Haka kuma ba azumi ne kadai za a iya yi ba a wadannan ranaku. An fi son a yi nau’o’in ibada mabanbanta. Amma dai azumi na daga cikin mafi girman nau’o’in ibada da za a raya kwanakin da su.

3. Yawaita Kabbarbari:

Yana daga Sunnah, yawaita yin Takbīr (Allahu Akbar) da Tahmīd (Alhamdu Lil Lah) da Tahlīl (Lā ilāha illal Lah) da Tasbīh (Subhānal Lah) a cikin wadannan kwanaki guda goma. Tirmidhī ya ruwaito Hadisi wanda Sheikh Albānī ya tabbatar da sahihancinsa a cikin littafin Sahīh Al-Jāmi’ daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
مَا مِنْ أَيَّامٍ أَعْظَمُ عِنْدَ اللهِ، وَلاَ أَحَبُّ إِلَيْهِ مِنَ الْعَمَلِ فِيهِنَّ مِنْ هَذِهِ الأَيَّامِ الْعَشْرِ، فَأَكْثِرُوا فِيهِنَّ مِنَ التَّهْلِيلِ، وَالتَّكْبِيرِ، وَالتَّحْمِيدِ
“Babu wasu ranaku da s**a fi girma a wajen Allah kuma ayyuka a cikinsu s**a fi soyuwa wajen Allah kamar wadannan kwanaki goma (na farkon watan Zul-Hijjah). Don haka, ku yawaita Tahlīl (fadin Lā ilāha illal Lah) da Takbīr (fadin Allahu Akbar) da Tahmīd (fadin Alhamdu lil Lah) a cikinsu.”

Ana yin wannan zikiri ne a bayyane. Kuma ana iya yinsa a kowane wuri, (kamar gida, kasuwa, kan t**i, da sauransu) banda wuraren da aka samu nassi sahihi da ya hana a yi. Kabbarbarin na iya daukar sīgar: Allahu Akbar, Allahu Akbar, lā ilāha illal Lah, wal Lāhu Akbar, wa Lillāhil Hamd; ko kuma duk wata sīga mai kyawun ma’ana, musamman wadanda Sunnar Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ta tabbatar.

Kabbarbari a wadannan ranaku, wata Sunnah ce da mafi yawancin mutane s**a manta da ita. Da wahala mutum ya ji ana yin kabbarbari a wadannan ranaku, musamman daga farko-farkon watan. Ya kamata a raya wannan Sunnah ta hanyar yin wannan zikiri a bayyane kuma a duk inda aka samu dama. Bukhāri ya ruwaito, “Abdullahi dan Umar da Abu Hurairah (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna yin wadannan kabbarbari a cikin kasuwa (don tunatar da mutane muhimmancin yin su) kuma sai mutane su ma su yi kabbarbarin.” Haka kuma Sayyiduna Umar (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana yin kabbarbari a cikin hemarsa, a Muna (lokacin aikin Hajji).

Da yawa daga malamai sun ce kabbarbarin da ake yi a wannan lokaci sun kasu gida biyu: Mutlaq (wanda bai da iyakantaccen lokaci) da Muqayyad (wanda aka kebe wa lokaci). Kowanne daga cikinsu ya tabbata a sahihiyar Sunna ta Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi). Mutlaq shi ne wanda za a yi tun daga daya ga wata har zuwa goma ga wata. Muqayyad kuwa shi ne wanda za a yi daga bayan sallar asuba na ranar Arfa zuwa sallar la’asar na ranar sha uku ga wata. A cikin Fathul Bārī, Ibn Hajar ya bayyana cewa fara yin wadannan kabbarbari daga bayan fitowar alfijir na ranar Arfa shi ne bayani mafi inganci da aka ruwaito daga Sahabban Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi).

4. Yawaita Addu’a da Zikiri ranar Arfa:

Muslim ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
خَيْرُ الدُّعَاءِ دُعَاءُ يَوْمِ عَرَفَةَ، وَخَيْرُ مَا قُلْتُ أَنَا وَالنَّبِيُّونَ مِنْ قَبْلِي: لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
“Mafi alherin addu’a ita ce addu’ar (da aka yi) ranar Arfa, kuma mafi alherin abinda ni da Annabawa kafin ni muka fada (a ranar Arfa) shi ne: Lā ilāha illāl Lah Wahdahu lā sharīka Lah, Lahul Mulk wa Lahul Hamdwa Huwa alā kulli shay’in Qadīr.”

5. Hajji da Umrah:

Hajji da Umrah na daga mafifitan nau’o’in ibada da ake yi a cikin watan Zul-Hijjah. Hadisi ya tabbata cewa Aljanna ce sakamakon aikin Hajji da ya kubuta daga sabon Allah da rashin bin ka’idodin Sharī’ah wajen gudanar da shi.

A wannan shekara ta 1441 bayan Hijira, wato shekarar 2020 a kalandar Bature, Allah (Mai girma da daukaka) Ya kaddara ba za a iya shiga kasar Saudi Arabia ba don gudanar da ibadar Hajji da Umrah saboda annobar Korona (Covid-19). Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa wadanda ke cikin kasar ce kawai za su samu damar gudanar da aikin Hajji don a kauce wa yiwuwar annobar Korona ta yadu saboda haduwar jama’a masu yawan gaske a wuri daya da kuma cakuduwar da za su yi da juna a lokacin gudanar da ayyukan Hajji. Muna rokon Allah Ya yaye mana wannan bala’i.

6. Ibadar Layya:

Ana yin layya ce ta hanyar yanka dabba daga cikin nau’o’in dabbobi guda uku (awaki da shanu da rakuma) daga ranar goma ga watan Zul-Hijjah (bayan an yi sallar idi) zuwa sha uku ga wata, don neman kusanci ga Allah (Mai girma da daukaka). Kasancewa ranar goma ga Zul-Hijjah ce rana ta farko ta yin layya, hakan ya nuna cewa layya tana cikin ayyukan da ake yi a goman farko na watan.

Ibadar layya tana daga manya-manyan ibadodi a Musulunci. Tana kara tunatar da Musulmi kadaituwar Allah (Mai girma da daukaka), da falalar Allah akan al’umma, kuma tana tabbatar da tsantsar biyayyar babanmu Annabi Ibrahim (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ga Allah (Mai girma da daukaka).

7. Sallar Īdi:

Sallar īdi na daga cikin ayyukan alheri da ake yi cikin kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah. Ana gudanar da ita a ranar goma ga wata, wato washegarin ranar Arfa.

Ranar īidi na daga alamomi na Allah wadanda Musulmai a ko’ina cikin duniya ke yin bukukuwa da shagulgula don bayyana godiya ga Allah saboda samun nasarar kammala wata babbar ibada, da jaddada ‘yan uwantakar addini, da kuma taya juna murna da farin cikin zagayowar daya daga cikin ranakun da Musulunci ya ba muhimmanci. Īdul Adhā, wato īdin babban salla na biyo bayan nasarar kammala tsayuwar Arfa da mahajjata s**a yi wacce ita ce rukunin aikin Hajji mafi girma.

A wajen mafi yawan malamai, sallar īdi Sunnah ce mai karfi. Wadansu Malamai na ganin cewa mustahabbi ce, a yayin da wasu kuma s**a tafi a kan wajabcinta. Salla ce da aka shar’anta ta ga Musulmi, maza da mata. Saboda muhimmancinta, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) har umurni ya bayar game da fita don gabatar da ita, shi kuma a karan kansa, ya lazimce ta tun daga shekarar da aka fara yinta har zuwa lokacin da ya bar duniya. A cikin Hadisin da Bukhāri da Muslim s**a ruwaito daga Ummu ‘Atiyyah (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “An umurce mu da fitar da ‘yan mata (wadanda s**a balaga) da matan aure da ke cikin dakunansu (har da wadanda ke cikin jinin al’ada) zuwa sallar īdi…” Haka kuma, Bukhāri da Muslim sun ruwaito Hadisi, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya umurci macen da ba ta da mayafin da za ta sanya don halartar sallar īdi ta karbi aro wajen wacce ke da safayar mayafi (don dai kowa da kowa ya halarci sallar).

8. Nau’o’in Ibada daban-daban:

Banda nau’o’in ibada da bayani ya gabata akansu, mutum yana iya yin duk wani aikin alheri da yake kusantar da bawa ga Allah (Mai girma da daukaka) don samun lada da kuma fatan dacewa da falalar wadannan kwanaki. Irin wadannan ayyuka sun hada da karatun Alkur’ani, da zikiri, da addu’a, da tuba daga zunubai, da yawaita istigfari, da salati ga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi), da sadar da zumunta, da ziyara, da kyautata wa iyaye, da sadaka, da fitar da zakka (idan ta dace da lokacin).

KAMMALAWA:

Ina rokon Allah (Madaukaki) Yasa mu dace da alhairan da ke cikin goman farko na watan Zul-Hijjah kuma Ya sanya mu cikin wadanda za su shagaltu da nau’o’in ibada cikin wadannan kwanaki don dacewa da falalarsu da kuma rabauta da samun kusanci ga Allah. Allah Ya magance mana annobar Korona kuma Yasa mu ci jarabawar da ke tare da ita.

Alhamdu lillah.

DOGARAWA

10/02/2025

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!
Makarantar Al-madinah Tahfizul Qur'an Dawakin tofa na farin cikin gayyatar daukacin al'ummar musulmi zuwa gagarumin taron walimar saukar Alqur'ani maigirma wanda za'ayi ranar Lahadi 16/2/2025 da misalin karfe 10:00 nasafe Allah yaba da ikon zuwa

16/12/2023
27/06/2023

Alhamdulillah yau muna 9 gawatan Dhul-hijja, 1444AH,
27 kenan gawatan June, 2023.
A yaune kuna Ranar Arfa.
Annabi S.A.W yace "Mafificiyar Addu'a itace Addu'a ranar Arfa kuma mafificin abinda nafada ni da Annabawan da s**a gabata shine

LA'ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER.

Yalla ya karba mana🙏

27/06/2023

Ma'aiki {ﷺ} yace;
Babu wata Rana da Allah yake zunzurutun 'yanta bayinsa daga wuta kamar ranar Arfa.

Allah yasa Muna daga cikin Wadanda za'a yanta a wannan Rana. 🤲🤲🤲

__Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)

23/06/2023

L A Y Y A !!!

--SAMARI DA YAN MATA GAREKU--

Annabi SAW yace duk wanda ya sami wadatar yin layya kuma baiyiba to kada ya kusanci massalin idin mu, yanzu dubarar da mutane sukeyi kaga mutun ya yanka shadda iya ganinka yana hawa mashin din dubu dari barkatai amma wallahi sai yazo baya layya ALLAH SAIYA KAMAKA duk wanda yake da halin sayen rago yaje ya saya wallahi, ba maganar sai nayi aure kafin damai aure da marar aure ibada ne, sallar nafila, hajji, umara ba zakaje ba sai kana da aure, wa yace maka ba'a layya saimai aure, samari da yan mata kun tara kudi kun boye.

DR ABDALLAH USMAN G/KAYA

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Dawakin Tofa, Between General Hospital And Medical Store
Kano