03/02/2026
Gayyata ta musamman
TAURARIN ALQUR'ANI GROUP NE DA'AKA BUDESHI DOMIN GABATAR DA SHIRYE-SHIRYE DASUKA SHAFI ALQUR'ANI KAD
03/02/2026
Gayyata ta musamman
07/01/2026
Tunda ake S A Tsangaya a jihar Kano ba a taba S A Tsangaya me kishin Tsangaya da yan Tsangaya irin wannan bawan Allahn Gwani Musa Falaki ba, wasu Gwamnatocin ma ba a san sunan waye ya rike irin wannan muƙamin ba, bare an san aikin da su ka yi, bare kuma korafi a kan sun yi kaza ba su yi kaza ba.
Idan aka buɗe zuciya za a gane shi aikin sa bayar da shawara ne ba zartarwa ba, kuma ba Hukuma ce da shi da ake ware mata wani kaso domin yin wani aiki ba, aikin bayar da shawara, idan ya bayar an dauka Shikenan idan ba a ɗauka ba, shi dai ya yi nashi aikin.
Wannan bawan Allah ta karkashin ofishin sa ya saka wasu daga cikin yan'uwa ƴan Tsangaya cikin farin sau babu adadi. Ba za iya yi wa kowa komai ba, k**ar inda ko Gwamnatin tarayya bata isa ta yi wa kowa komai ba, duk abin da za a yi a gwamnati ko ta jaha ko ta Tarayya ko ta Local Government sai kana da rabo za ka samu.
Jahilci da hassda da son zuciya da rashin sanin ya tsarin gwamnati yake, shi ne zai sa idan ba a yi tsari da kai ba ka ce ba a yi, ko ka ce ba a yi daidai ba, idan kuma an yi da kai ka ce an yi daidai, wannan ya zama banbaɗanci na siyasa, idan kuwa haka ne k**ata ya yi mutum ya fito fili ya k**a siyasa haikan domin cimma burin sa.
Idan mutum yana son gaskiya kuma yana son kawo ci gaba a wani tsari, to Gwamnati ake ƙalu balan ta ba wai wani wanda yake da wani muƙami ba, domin wanda ya bayar da wannan muƙamin ya fika sanin wa ya bawa mukami, ya fika sanin iya hurumin aikin sa, idan wanda ya bawa aiki baya yin abin da Yak**ata to ya fika sani, tunda shi ya bashi aikin.
Wannan bawan Allah Ya yi Abubuwan alkhaiiri da yawa a Tsangaya wanda tun zamanin Malam Ibrahim Shekarau ba a yi su ba.
Muna yi masa fatan alkhaiiri da fatan samun nasara a wannan aiki da aka bashi da fatan samun kujerar zartarwa da tafi ta bayar da shawara domin kawo ci gaba ga Alarammomi.
Allah ya shiga Lamarin sa Amin
Yasir Gwani Badamasi
Yanzu Mun Ransar Da Gidan Gwamnatin Kano
Saura Villa In Sha Allah
Mai Bawa Gwamna Shawara Wato S.A Tsangaya GWANI MUSA FALAKI. yayi abun ayaba Dama yasaba Da qoqari Akan Yan Tsangaya Allah yayi Masa Jagora Allah yakareshi Daga Sharin Maqiya
03/12/2025
ALHAMDU LILLAH
GA GWAMNAN MAHADDATA ALQUR'ANI YOBE STATE
WANNAN TAFIYACE TA HADINKAN MATASAN
DA QARA ZABURARWA AKAN ALQUR'ANI.
DAYA BAYAN DAYAN ZASU BIYO IN SHA ALLAH.
DAGA DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA
3/12/2025
27/11/2025
TA'AZIYYA GA IYALAN SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI
A madadin Dukkan Mahaddatan Alƙur'ani na Kano da Kewaye
A madadin dukkan Mahadda Alƙur'ani na Jihar Kano da kewaye, Gwani Sidil Faruk, Gwamnan Mahadda na Kano State (Da Kuri Da Maimai), yana mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan marigayi Sheikh Dr. Dahiru Usman Bauchi (Rahimahullah), musamman ɗansa *Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi (Khadimul Faidha)*, da kuma ɗalibansa da mabiya a ko’ina.
Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga al’umma gaba ɗaya, musamman bangaren ilimi, tasawwuf, da tarbiyyar al'umma bisa tsantsar koyarwar Qur’ani da Sunnah. Rayuwarsa ta kasance abar koyi wajen shimfiɗa zaman lafiya, karfafa ɗa’a da gina al’umma masu tsoron Allah da biyayya ga Annabi Muhammadu (SAW).
Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya ɗaukaka darajarsa a Aljannah, Ya sa Alƙur’anin da ya koyar da shi da miliyoyin mutane s**a haddace ya zama hujja a kansa. Allah Ya ba iyalansa, dalibansa da mabiya, musamman Sheikh Khadimul Faidha haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Allah Ya jikan Sheikh Dahiru Usman Bauchi da rahma ya b iyalansa da mabiya haƙuri
26/10/2025
Gayyata ta musamman
Daga Gwarzon Shekara na Tsangaya na 2025
Gwani Saminu Barden Tilawa Vice president na Matasa na QASA
sanarwa Daga Gwani Sidil Furuk Alhamzawy
Gwamnan Mahaddata Alqur'ani na kano da kewaye (DAKURI DA MAIMAI)
DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA
Yan izala sun yiwa Yan Tsangaya illa ba karama.ba sabo da Abubuwa da yawa sedai Ayi haquri nasan Akwaisu da yawa Acikin Yan Tsangaya
01/03/2025
RANAR MAHADDATA TA DUNIYA !
MAJALISAR DINKIN DUNIYA TAKI TA WARE MANA RANAR MAHADDATA ALQUR'ANI TA DUNIYA, DON HAKA MUN WAREWA KAN MU RANAR 1 GA WATAN RAMADAN TA ZAMA RANAR MAHADDATA.
WANE MAHADDACIN ALQUR'ANI KA SANI KA SA MANA A COMMENT SECTION
NI DAI NA SA MATASHIN GONI WATO GONI
DR GONI SIDI BASIRU ALHAMZWY
SARKIN YAQIN AHLILBAITI
Sidil Faruk Alhamzwy
1/3/2025
DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA
26/02/2025
Wannan Shine Gwani MUHAMMADU Maei katibi 1 Deputy Gwamnan mahaddata Alqur'ani na jihar Kano Shine Wanda yafara Rubutu na gayyata A tsangaya
Shine Wanda yadauki tsawon lokaci yana raba tilawa A cikin group na Ahlul Qur'an kafin A bude shafin mu koma tsangaya Wanda yazama zakaran gwajin dafi wajan zaqulo harji inda Gwani yahaya Bajude tare da Gwani Ibrahim Mai sittin s**a rufa masa baya waja fito da harji acikin group na Whatsapp s**aci gaba da bawa Yan uwa gudun mowa Acikin tsangaya
Shine mafi qarancin shekaru Acikin Wanda aka nada gwanayen Alqur'ani A cikin mutum sama da 100 Wanda marigayi Gwani lawi Gwani Dan zarga yayi Wannan baiwace da Allah yabashi Dakuma biyayyar iyaye
Shine 1 wajan goyan Baya akan tafiyar Gwamnatin mahaddata Alqur'ani da aka kafata tsawon Shekaru 9 A qarqashin Shugaban Matasa na Mahaddata Alqur'ani na NIGERIA Gwani saminu Mai 30
Bisa izinin Gwani lawan SHUGABA Mai Daja ta 1 Tare da Shauran Matasan Alqur'ani na NIGERIA
Allah yaqara maka jangora A cikin lamuranka Allah yatsareka daga dukkan sharri Deputy Abu ihsan
Sidil Faruk Gwamnan Mahaddata Kano
25 /2 /2025
DA'IRAR MUSAFFA NIGERIA
21/10/2024
Akwai tattaunawa ta musamman a yau Litinin 21/10/2024 tare da Gwani Sidil Faruk (Gwamnan Mahaddata Alqur'ani Kano State) da misalin 3:00 PM a tashar Aminci Radio
05/08/2024
Zamu jagoranchi addu'a ta kasa (national prayer) a rana 10 ga wata insha allah!
Zamuyi saukar alqur'ani miliyan 1 da salatin annabi biliyan 1 da azumi a wannan rana! Domin nemawa kasarmu zaman lafiya da saukin rayuwa.