Abu Nihlah As-Salafiy

Abu Nihlah As-Salafiy

Share

Researcher and Observer on Islamic Issues and Comparative Religions

01/08/2023

In ka samu ikon amfanar kai ko wasu, ba a jira, marmaza kayi me ya dace, domin ba kada tabbacin samun ikon nan gaba, ta yiwu wannan ce ɗorarriya!

01/08/2023

Kar ka jira sai ka samu dama za ka gyara kuskure, kana gane kuskure gyara shi kawai, domin damarmakin za suyi ta zuwa baka iya zaɓar ɗaya ciki ba!

24/07/2023

Taƙaici ne Mai Ƙuna Rai da Baƙanta Rai kaga MUSULMI ya mato kan wani FITACCEN ƊAN ƘWALLO ko wani SHARARREN MAWAƘI da sun tsani ADDININ ALLAH da MANZON ALLAH (S.A.W.)

12/05/2023

AURE TUFA CE DA AKE SUTURCE KAI DA ITA!

In an saka ta, ba a cire ta, dole sai an kula domin ba ko ina ake zama ba, gudun kar ta ɓaci, saboda wata ƙazantar in ta taɓa tufa bata fita duka sai ta bar gurbi, wani tabon in ya ɗisa a tufa gurbin shi sai ya dafe, sannan ba kowanne irin sabulu za ayi amfani ba wajen wanke ta ba gudun koɗau, sannan ba a gwamutsa cikin kayan da suke bau gudun kar ta rine tayi dabbare-dabbare, miji ke matsayin tufar sama, mace kuma matsayin tufar ciki. Dole mace ta tsaftace mijin ta, domin sutura ne gare ta dake rufa mata asiri, haka dole miji ya kula wajen tsaftace matar shi domin sutura ce gare shi dake rufe masa tsiraici.

Allah ka tufatar da mu, ka kuma bamu suturta da dindindin.

26/02/2023

An bi maslahar ƙashin kai sama da maslahar al'ummar musulmi da sunan cancanta, wanda tsantsar ƙwarar kai ne

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kano
700321