29/11/2022
Spread Islam
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Spread Islam, Education, Sharada, Kano.
29/11/2022
29/11/2022
*SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP*
*_MUHIMMANCIN SALLAH_* {3}
Ya ku bayin Allah; haqiqa akwai wasu abubuwa da sukan janyo halartowar zuciya ga mai yin sallah, daga cikin su akwai: halarto da ma'anar abin da (shi mai sallar) yake fada kuma yake aikatawa a cikin sallarsa: misali: idan ya yi kabbara ya daga hannayansa, ya tuna cewa wannan girmamawa yake ga Allah, kuma idan ya sanya hannun dama a kan na hagu ya tuna cewa wannan qasqantar da kai yake a gabansa. Kuma idan ya yi ruku'u to yana girmama Allah ne, kuma idan ya yi sujjuda to wannan qasqantar da kai ne gaba ga daukakar Allah.
An karbo daga Abu Hurairata (R.A.) daga Annabi )ﷺ ( ya ce: "Allah Ta'ala Ya ce, *_"Na raba sallah tsakanina da bawana gida biyu, kuma bawana zai sami abin da ya roqa*
(a ( الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ 2 ) [الفاتحة: 2]
Sai Allah Ta’ala ya ce, *«Bawa na ya gode mini».* Idan bawa ya ce,
الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ 3 ) [الفاتحة: 3]
sai Allah Ta’ala ya ce, *«Bawana ya yabe ni».* Idan kuma ya ce,
( مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ 4 ) [الفاتحة: 4]
sai Allah Yace, *«Bawana ya girmama ni»,* wani karan kuma ya ce, *«Bawana ya fawwala lamarinsa zuwa gare ni».* Idan ya ce:
( إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ 5 ) [الفاتحة: 5]
sai Allah ya ce: *«Wannan tsakanina ne da bawana, kuma bawana zai sami abin da ya tambaya».* Idan ya ce,
( اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ 6 صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ 7 ) [الفاتحة: 7]
sai Allah yace *wannan na bawana ne kuma bawana zai sami abin da ya roqa».* Muslim ne ya ruwaito shi.
Yayin da ka ce:
((سبحان ربي العظيم وبحمده
*_subhana rabbiyal azeem wabi hamdi_*
ko ka ce,
(سبحان ربي الأعلى وبحمده),
*_subhana rabbiyal A'ala wabi hamdi_*
ko da kuwa ka fade su ne da murya qasa-qasa to haqiqa Allah yana jin duk wata magana da kake fada, kuma yana ganin duk wani aiki da kake aikata wa, komai qanqantarsa. Kuma ya san duk abin da kake tunani a cikinsa ko da kadan ne. Kuma yayin da ka kalli
05/09/2022
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Culinary Team
Attire
Contact the school
Website
Address
Sharada
Kano