Malam Shehu Mansur Dala

Malam Shehu Mansur Dala Shafi ne da aka samar da shi domin fadakarwa akan addini da rayuwa.

18/09/2026

*Khudubar Juma'a* ๐Ÿ•Œ

*Me taken*
Dalilan samun Yalwar zuciya da farin ciki

Tare da *Sheikh Abubakar Mansur Dala* (Hafizahullah)

Daga Masallacin juma'a na Bakriyyah Turba waika waje

*Telegram*
https://t.me/Malhalifa

*Juma'a*
07/4/1448==18/9/2026

*AYI SAURARO LAFIYA* ๐Ÿ‘‡๐Ÿป

18/09/2026

Hudubar juma'a kai tsaye

Daga Masjid Bilal Bello Road Singer Kano

Abubuwan da ke jawo mutum ya kauce daga tafarki madaidaici, da kuma illolin hakan ga mutum da al'umma:Dalilai:1- Raunin ...
17/09/2026

Abubuwan da ke jawo mutum ya kauce daga tafarki madaidaici, da kuma illolin hakan ga mutum da al'umma:

Dalilai:

1- Raunin imani: Idan imani ya yi rauni a zuciya, mutum yakan fi fuskantar fadawa cikin sabo.

2- Waswasin shaidan: Shaidan shi ne babban makiyin mutum, yana rura masa wutar sabo kuma yana jarabtar da shi.

3- Muguwar abota: Abokai da ba su bi ka'idojin shari'a ba, za su iya jawo abokinsu zuwa ga hanyarsu.

4- Sha'awa: Bin son zuciya da sha'awoyi marasa inganci na iya haifar da karkacewa.

5- Watsi: Manta makasudin rayuwa, da nisanta daga ambaton Allah, na iya sanya mutum ya fada cikin kuskure.

Illoli:

1- Illar tunani da ruhi: Mai laifi yakan ji da-na-sani, kunya, da damuwa, kuma hakan na iya haifar da damuwar zuciya da rashin kwanciyar hankali.

2- Illar ruhi: Imani na mutum na raguwa, kuma hakan na iya haifar da nisantar ibadu da biyayya.

3- Illolin duniya: Mutum na iya fuskantar hukunci na shari'a, kamar haddi ko ta'aziri, ko kuma hukuncin al'umma kamar rasa amincewar mutane da mutuncinsu.

4- Illolin lahira: Idan mutum bai tuba daga zunubinsa ba, zai iya fuskantar azaba a lahira.

A takaice dai, karkacewa tafarki madaidaici ana daukarsa a matsayin dama ce ta tuba da komawa ga Allah, domin kofar tuba a bude take koyaushe, kuma Musulmai sun yi imani cewa Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.

Shk. Abubakar Shehu Mansur Dala (Khalifa).

16/09/2026

KU FA LIKITOCI NE

Malami Mai da'awa kamar likita ne,Kai,ya ma fi likita,saboda shi yana maganin cututtukan jiki da na zukatu ne da iznin Allah Ta'ala.
Saboda haka,ya kamata Malami mai da'awa ya fi likita tausayi,ya ma fi uwa da uba tausayi.
Shin me kuke zato zai faru idan likita ya kasance yana rike da zumbudediyar doruna domin jibgar marasa lafiya da aka kai masa don ya ba su magani ? Bugu da kari ga bakar magana da ba'a da kushe da sauransu.Duk wanda ya je wurinsa sai ya samu rabonsa ko dai ya ji a jikinsa ko ya ji a ran sa ko duka biyun ?
Don Allah Malamai da Dalibai ku tausaya mana,mu fa marasa lafiya ne a gaban ku.
Ku kai mu dakin duba marasa lafiya da dakin tiyata na
ูˆู…ุง ุงุฑุณู„ู†ุงูƒ ุฅู„ุง ุฑุญู…ุฉ ู„ู„ุนุงู„ู…ูŠู†
Ku ba mu magunguna da alluran
ููŠู…ุง ุฑุญู…ุฉ ู…ู† ุงู„ู„ู‡ ู„ู†ุช ู„ู‡ู… ูˆู„ูˆ ูƒู†ุช ูุธุง ุบู„ูŠุธ ุงู„ู‚ู„ุจ ู„ุงู†ูุถูˆุง ู…ู† ุญูˆู„ูƒ ูุงุนู ุนู†ู‡ู… ูˆุงุณุชุบูุฑ ู„ู‡ู… ูˆุดุงูˆุฑู‡ู… ููŠ ุงู„ุฃู…ุฑ
Da magungunan nan masu karfi da saurin amfani samfurin
ุงุฏุน ุฅู„ู‰ ุณุจูŠู„ ุฑุจูƒ ุจุงู„ุญูƒู…ุฉ ูˆุงู„ู…ูˆุนุธุฉ ุงู„ุญุณู†ุฉ ูˆุฌุงุฏู„ู‡ู… ุจุงู„ุชูŠ ู‡ูŠ ุฃุญุณู†
Da Kuma na ูู‚ูˆู„ุง ู„ู‡ ู‚ูˆู„ุง ู„ูŠู†ุง ู„ุนู„ู‡ ูŠุชุฐูƒุฑ ุฃูˆ ูŠุฎุดู‰
Idan kuwa kuka Kai mu dakin
ู…ุง ุงุฑูŠูƒู… ุฅู„ุง ู…ุง ุฃุฑู‰
Kuka ce da kayan aikin wannan dakin za ku Yi mana aiki da duka kayan aikin wannan dakin, a gaskiya babu abin da zai faru sai dai ciwon ya yi ta cin mu har mu mutu a haka,Kuma wallahi Kuna da babban kamashu na zunubin batan mu.
Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta,ka ganar da mu karya ka ba mu ikon guje mata.
Shehu Mansur Dala
5/4/1448------16/9/2026.

15/09/2026

Address

Turba Waika Waje
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malam Shehu Mansur Dala posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Malam Shehu Mansur Dala:

Shortcuts

Share

Category