06/01/2026
KIRA GA DUKKAN HUKUMOMIN DA SUKE DA HAQQI AKAN SIYE DA SIYARWA DA QYANQYASASSUN KANI, AKAN SU SA IDO KUMA SUYI ABINDA YA DACE.
Haramtaccen qarin farashin kudin kaji da gidajen qyanqyasa suke yi, dole ne ayi maganin wannan zalincin.
Ina yin wannan sanarwa ne don na jawo hankalin dukkan hukomomin gwamnati da suke da hurumi akan wannan sha'anin bisa mummunar dabi'a ta rashin adalci da kuka sabawa doka wadda tayi qamari a harkar kiwon kaji a Najeriya.
A fadin qasa, masu kiwon kaji ma fuskantar barazana na biyan qarin kudin akan kajin da s**a siya/booking saboda samun jinkiri, kuma a qaida wannan jinkirin yawanci ana samun sane daga bangaren mai siyarwa ba mai siye ba.
Abinda yake faruwa shi ne, masu kiwon kaji s**an biya kudin kajin da suke so ko wani bangare daga ciki, dan su tabbatar da an karbi odar su, sai a basu ranar da za su dauki wannan kaji, Al'ada ce a cikin harkar cewa za'a tabbatar da farashi ne kadai ranar da za ka dauki wannan kaji, ma'ana idan akace maka za ka dauka 12 ga wata, sai akayi rashin sa'a 12 ga wata kaza ta tashi, to za ka qara kudi, in kuma akayi sa'a ta sauka to za su baka ragowar kudin ka.
To inda rashin adalcin yake shi ne, in s**a ce maka 12 ga wata,sai 12 ga wata tayi, kuma basu iya samu sun cika alqawari ba, bayan kai a shirye kake daka biya ragowar kudi ka dau kazar ka katafi, sai s**e maka kayi haquri an damu tsaiko kajin basu samu ba, ko wani abu makamancin haka, in kace ba komai, sai aka daga aka baka wani date din, to fa kazar za ta tashi, misali daga 1200 zuwa 1600, sai s**e ai sai ka biya 1600.
To a shari'ance wannan dage ranar daukan kaji daga wajen mai siye ne, kuma doka ta haramta masa amfanuwa ko samun amfani daga kuskuren da shi ne ya haifar dashi, saboda haka, abinda yafi doka tace shi ne, za ka dauki kajin ka a ainahin farashin wannan ranar wanda shi ne 1200 saboda ba kai ne ka daga ranar daukar kajin ka ba.
Abinda na kira wannan dabi'a da haramun shi ne, doka bata yarda mai siyarwa yaji gajiyar laifin daya aikata ba, ba zai iya qara farashi ba idan shi ne ya haddasa jinkirin, ko kuma jinkirin daga wajen sa ne, wannan jin zali ne, kuma sabawa yarjejeniya ne.
Kuma rashin kawo kajin nan akan lokaci zai haddasa;
1. Tarwatsa tsarin da mai kiwo yayi nan take.
2. Lalata masa jadawalin allurai da magani
3. Bata duk wani tsari na ma'aikata, hatta tsaftar wurin da aka shirya za a ajiye kaji yanzu tana cikin barazana da sauran abubuwa da mai kiwo ne kadai ya san su.
Idan kuma wannan dabi'a taci gaba to za ta lalata qananu da matsakaitan masu kiwon kaji, za ta hana sababbin mutane shiga harkar kiwo, farashin kaza da qwai zai dinga hauhawa babu lissafi, sannan zai lalata harkar abinci kanta a Najeriya.
Saboda haka ina kira ga wadannan hukumomi dasu gaggauta shiga cikin wannan lamarin, su bincika, su tsara dokoki, kuma su hukunta masu aikata wannan laifi.
Federal Ministry of Agriculture and Food Security
Standards Organisation of Nigeria - SON
Federal Competition and Consumer Protection Commission Consumer Protection Council of Nigeria