Halqatu Muhammadil Ayyub Litajweedil Qur’an

Halqatu Muhammadil Ayyub Litajweedil Qur’an

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Halqatu Muhammadil Ayyub Litajweedil Qur’an, School, dorayi sheik jaafar mahmoud Road, garejin kamilu, kumbotso local government, Kano.

Assalamu Alaikum Warahmatullah
‘Yan’uwa masu albarka wannan zaure mun samar da shi ne domin yada da’awar addininmu na Musulunci (A bisa fahimtar magabata na kwarai ) da kuma nuna muku yadda muke gudanar da tsare-tsaren karatu a wannan Halqa mai albarka.

06/03/2026

Shaikh Muhammad Ayyub Rahimahullah | 1952-2016.

Sheikh Muhammad Ayyub yana daga cikin shahararrun limaman Haramin Madina kuma fitaccen mai karatun Al-Kur’ani wanda murya da karatunsa s**a shahara a duk faɗin duniyar Musulmi. Ya yi hidima mai tsawo a Masjid an-Nabawi a cikin birnin Medina.

An haifi Sheikh Muhammad Ayyub a shekarar 1952 a birnin Madina. Ya taso cikin iyali masu son ilimin addini da karatun Al-Kur’ani. Tun yana ƙarami ya fara koyon Al-Kur’ani har ya haddace shi gaba ɗaya yana matashi.

Tun daga wannan lokaci malamansa s**a lura da: Kyakkyawar muryarsa mai haɗe ta Tajwidi da kuma fahimtarsa da ilimin Al-Kur’ani.

Sheikh Muhammad Ayyub ya yi karatu a makarantu da jami’o’in Madina, inda ya kware a fannin Islamic Studies. Ya yi karatu a Islamic University of Madinah, ya samu digiri a ilimin Tafsir da Ulumul Qur’an (ilimin fassarar Al-Kur’ani).

Sheikh Muhammad Ayyub ya zama ɗaya daga cikin limaman Masjid an-Nabawi a shekarun 1980s. wanda yake jagorantar sallar Tarawihi a watan Ramadan kuma karatunsa ya shahara sosai saboda nutsuwa, tsari da taushi.
Mutane daga ko’ina cikin duniya suna sauraron karatunsa a rediyo da talabijin.

Sheikh Muhammad Ayyub ya rasu a ranar 16 ga Afrilu 2016 a birnin Madina bayan fama da rashin lafiya. An yi masa jana’iza a Masjid an-Nabawi, kuma an binne shi a makabartar Jannat al-Baqi kusa da masallacin Annabi ﷺ.
Rasuwarsa ta girgiza al’ummar Musulmi saboda kasancewarsa ɗaya daga cikin fitattun masu karatun Al-Kur’ani na zamaninsa.

Ahlul Qur'an TV

22/10/2025

Alhamdulillah a yau ne laraba 22-10-2025
Wannan Daluba (fatima Auwal)ta samu Nasarar kammala Haddar Alqur’ani mai girma.
Muna Addu’a Allah ya Albarkaci karatun ta,Allah Ya sakawa Malaman ta da iyayen ta Da Alkhairi.
Allah ya Bawa Ragowar Abokan Karatun ta Nasarar kammalawa Suma.
Amen.

21/10/2025

Innalillahi wainna Ilaihi Rajiun 😭
Allah yayiwa Malam Aminu library Rasuwa
Na’ibin Dr.Bashir ,Limamin Masallacin Alfurqan Nasara GRA
Kuma Ubane Ga Wannan Makaranta Wanda Duk Wata Gudunmuwa Yana Bawa Wannan Makaranta
Muna Addua Ubangiji Allah ya Haskaka Qabarin sa Allah kuma ya Sa Mutuwa hutu ce a gare shi
Haqiqa Wannan Makaranta Baza ta taba Mantawa da Alkhairan Malam ba.
Muna fatan Iyaye Masu Albarka za a Saka Malam a cikin Adduoin ku na yau da kullum 😭

19/10/2025
20/08/2025

Our humble headmaster 🥰

20/08/2025

Allah ka kara mana Albarkar Alqur’ani🤲🏻🤲🏻.

Photos from Halqatu Muhammadil Ayyub Litajweedil Qur’an's post 12/08/2025

Allah yayi muku Albarka🤲🏻.

07/08/2025

🥰

Muna godiya Halqatu Sh Muhammadil Ayyub...

12/07/2025

Babban malamin mu sheik Goni Abubakr sadiq Amin tafida yayin gabatar da Nasiha ga dalibai.

03/06/2025

🥰

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address

Dorayi Sheik Jaafar Mahmoud Road, Garejin Kamilu, Kumbotso Local Government
Kano