Ina jinka.❎
Ina jin ka.✅️
Amma, kalmar "jinka"(a haɗe) takan zo da ma'anar "thatch" da Turanci — wadda dai Bahaushe yake amfani da kalmar wajen, "hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka".
Madalla!
Teachers & Learners
Mun samar da wannan feji ne don koyo da koyar da kyautata Hausa a rubuce.
"Nafa cema banda ni acikin ƴan uwan su"
A gyara mana wannan jimlar bisa cika dukkan ƙa'idojin rubutun Hausa. 👇
Ni dai "bana" sam "ba na" son a liƙa kowacce irin "bana" a ƙofar gidana.
1. Bana = this year
2. Ba na = I don't
3. Bana = banner
Wannan darasin yana koyar da mu cewa kuskure ne a ƙa'idar rubutun Hausa a haɗe kalmar "ba" da "na" a lamba ta 2. Kullum suna zuwa ne a rabe; don kuwa a kodayaushe zaman kansu suke yi.
Ku kawo naku misalan da ɗaya daga cikin kalmomin a cikin jumla.👇
Madalla!
"Kaji wai shine ya cin ye kaji uku azama ɗaya beje ko ina ba."
A gyara mana wannan jumlar bisa cika dukkan ƙa'idojin Hausa a rubuce.
Ban
Banji labarin ba.❎️
Ban ji labarin ba.✅️
Banda ni fa.❎️
Ban da ni fa.✅️
A kawo misalai a cikin jumloli don auna fahimta.
Itace ta gayawa ɗan sholin hanyar da su ke bi
ko da yaushe in zasu tafi daji samo ita ce."
A gyara mana wannan jumlar bisa kiyaye ƙa'idojin Hausa a rubuce.
Ƙwayoyin Ma'anar "Na" da "Ta"
A taƙaice dai ana amfani da su ne wajen samar da sunayen laƙabi. A dokar ƙa'idojin Hausa a rubuce, ba a raba su da kalmar sunan da aka liƙa su da ita. Ga wasu misalai:
Na Madi❌️
Namadi✅️
Na Ƴartalla❌️
Naƴartalla✅️
Na Rambaɗa❌️
Narambaɗa ✅️
Na Abba❌️
Na'abba✅️
Ta Bawa❌️
Tabawa✅️
Ta Rasulu❌️
Tarasulu✅️
Ta Sidi❌️
Tasidi✅️
Ku kawo mana misalai a jumlace da ko da ɗaya ne daga cikin sunanayen da ke sama.
Madalla!
Bashir Jammaje
Menene, wacece, wanene❎️
Mene ne, mece ce, wane ne✅️
Ku kawo misali da ko da ɗaya daga cikinsu ne a cikin jumla.
Ya "gan ni" a "san da" na "fid da" kayan!
_ganni❌
_sanda❌
_fidda❌
Amma akwai kalmar "sanda"(stick) da "Sanda"(sunan mutum).
A gyara mana wannan jumlar bisa kiyaye ƙa'idojin Hausa a rubuce:👇
"Baka da abinda za ka cewa Allah se godiya a ko da yaushe acikin lamuran ka."
Ƙa'idojin Rubutun Hausa!
"Nace masa muje donni na ga ji da jira. Amma yaƙi yazo muje!"
A gyara mana wannan maganar bisa cika ƙa'idar Hausa a rubuce.
"Kaji tsoronsa don shine ya ganni ya sanar dasu."
A gyara mana wannan jumlar bisa cika ƙa'idojin Hausa a rubuce.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Kano
BASH()68