Ilimin Noma Da Kiwo

Ilimin Noma Da Kiwo Wannan shafi ne wanda yake koyar da dabarun noma da kiwo don inganta hanyoyi samun riba mai yawa. da noman dankali

Wannan shafi yana karkashin jagorancin Bashir Abdulaziz, wadda shine marubucin littafin nan mai suna "Yadda ake kiwon broilers Dalla-dalla."

Ciyawar Brachiaria🌿 wadda ake kira signal grass ko (brachiaria) grass tana da amfani sosai a kiwon dabbobi da kuma ƙara ...
04/08/2026

Ciyawar Brachiaria🌿 wadda ake kira signal grass ko (brachiaria) grass tana da amfani sosai a kiwon dabbobi da kuma ƙara kare ƙasa daga ƙarancin amfanin gona.

Ga wasu dagacikin amfaninta ciyawar🌿 brachiaria.

- Ciyar da dabbobi da'ita saboda tana da sinadaran gina jiki da yawa wato (protein) ana Ciyar da shanu, awaki, da tumaki da'ita saboda suna son ciyawar brachiaria sosai🌿

ciyawar brachiaria🌿 tana ƙara yawan madara da nama ga dabbobi.
Saboda ciyawar brachiaria 🌿tana ɗauke da yawan abinci mai kyau da take bayarwa ga dabbobi ciyawar brachiaria 🌿tana taimakawa shanun madara da shanun nama su yi ƙiba da kyawon jiki.

Ciyawar brachiaria 🌿tana Kare ƙasa daga kwararar ruwa wato (erosion).

ciyawar brachiaria 🌿Tana da tushe (roots) Mai zurfi wanda ke riƙe ƙasa sosai.

ciyawar brachiaria 🌿tana Inganta ƙasar gona.

Ciyawar brachiaria 🌿tana ƙara sinadaran nitrogen a ƙasa (idan aka haɗa da legumes)☘️

Ciyawar brachiaria 🌿Tana ƙara danshi da rage datti ga ƙasa.

Sauƙin noman ga ciyawar brachiaria🌿
Tana girma da sauri kuma tana jure fari da sauyin yanayi.

Ana amfani da'ita wurin circular grazing.

Ana iya amfani da ita wajen gudanar da kiwo mai amfani da nagarta ta hanyar raba fili (rotational grazing)

27/07/2026

Big shout out to my newest top fans! Nafisa Abubakar

Daga ganin wadannan hotuna nasan wani abu sai ya zo ranku saboda a cikinsu akwai sakonni masu tarin yawa.A matsayinku na...
13/07/2026

Daga ganin wadannan hotuna nasan wani abu sai ya zo ranku saboda a cikinsu akwai sakonni masu tarin yawa.
A matsayinku na manoma wane sako kuka fahimta cikin hotunan?
Wannan ma ilimi ne..

Matasa Maza da Màta ga Dama Ta Samu Daga Kafar Ilimin Noma Da Kiwo Duba Comments Section Domin Samun Wannan Garabasa.
12/07/2026

Matasa Maza da Màta ga Dama Ta Samu Daga Kafar Ilimin Noma Da Kiwo Duba Comments Section Domin Samun Wannan Garabasa.

Ilimi cikin Hotuna Kashi Na 4, ku karu kuyi share... Ilimin Noma Da Kiwo
12/07/2026

Ilimi cikin Hotuna Kashi Na 4, ku karu kuyi share...
Ilimin Noma Da Kiwo

Ilimi cikin Hotuna Kashi Na 3, ku karu kuyi share... Ilimin Noma Da Kiwo
12/07/2026

Ilimi cikin Hotuna Kashi Na 3, ku karu kuyi share...
Ilimin Noma Da Kiwo

Ilimin cikin hotuna kashi Na 2,  Ku karu dasu kuma kuyi share.... Ilimin Noma Da Kiwo
12/07/2026

Ilimin cikin hotuna kashi Na 2, Ku karu dasu kuma kuyi share....
Ilimin Noma Da Kiwo

Ilimi cikin hotuna kashi na 1, ku karu kuma kuyi share zuwa ga wasu......
12/07/2026

Ilimi cikin hotuna kashi na 1, ku karu kuma kuyi share zuwa ga wasu......

Muna Maraba da ku sabbin mabiyanmu! A wannan kafaManoma da makiyaya abokan juna ne mu hadu a wannan kafa mu karu da juna...
09/07/2026

Muna Maraba da ku sabbin mabiyanmu! A wannan kafa
Manoma da makiyaya abokan juna ne mu hadu a wannan kafa mu karu da junanmu!
Barka da shigowa Jonathan Zakariya, Mamy Umar, Kabiru Shehu, Sadeeyarh Aleeyou, Ummul Khairi, Zainab Alkhaseem
Mu kasance tare a tsawon shekaru masu yawa.

Zamuyi farin ciki sosai idan kuka sake karanta wannan rubutu, domin akwai muhimman dalilai da yasa mukayi shi tun a baya...
09/07/2026

Zamuyi farin ciki sosai idan kuka sake karanta wannan rubutu, domin akwai muhimman dalilai da yasa mukayi shi tun a baya. Abu ne mai kyau ka gane wannan bayan kayi girbi yaya zakayi da amfanin gonarka?
*Ko da nufinka son sayarwa ne.
*Ko dà nufinka son cinyewa ne a gidanka.
*Ko da nufinka duka biyun ne.
To mafarmu cikin rubutun a bayyane take zaka fahimta domin karawa kai hangen nesa bisa tafarkin noma.
Allah ya karawa ayyukanmu albarka.

Wannan rubutu shawarace ta musamman ga manoma bayan Girbin Amfanin Gona.
Kila baza ka fahimce ni ba har sai ka kammala karanta rubutu na baki daya. Wannan rubutu nayi shine musamman domin kananan manoma da har yanzu basu fi karfin noma abincin da zasu ci da iyalansu a shekara ba, kuma suke son suyi arziki da harkar noma.

Dayawan mutane a kasar nan abin da zasu ci da iyalansu a kowace rana wahalar samu yake musu saboda matsin rayuwa da kuma talauci.

Nasan dai matukar mutum lafiyarsa kalau yasan cewa sai an ci an koshi ake gudanar da al'amuran rayuwa.
Tsarin Rayuwa da muke ciki kewaye take da wajibabbun abubuwa da wadda basu wajabta ba, wasu mune muka kirkirarwa kammu wasu kuwa halittarmu ce tazo dashi a haka wato k**ar dai cin abinci, babu yadda za ayi dashi sai anci a zauna lafiya.

Abin da yasa nayi wannan rubutu shine akwai wani babban kuskure da manoma da dama ke yawan maimaitawa cikin kasarnan a duk shekara wajen sayar da duk abinda s**a noma tun daga farkon girbi, ba tare da sun ajiyewa kansu da iyalinsu ba na cin da zai kai musu shekara ba. Wannan kila baya rasa nasaba da harkokin bukukuwa, kasuwanci, sharafin Aure, bikin Sallah, shari'a, karatun yara, ko rashin lafiya da ma dalilan da ba lallai na sansu ba.

A halin da rayuwa yanzu take ciki zaka sami mutum yana aikin gwamnati ko sana'a yana samun kudi a kalla dubu dari zuwa da hamsim (100,000 zuwa 150,000) a wata, amma wallahi bata iya isarsa wajen ci da iyalansa balantana ayi maganar jin dadi, wannan mai dama kenan. Wani kam idan ka duba hakan ma baya samu domin da aikin karfi yake nemowa yaci da iyalinsa.
Amma duk da wadannan kalubale a hakan mutane dayawa ke dagewa su yi tarun kudin noma su noma amfanin gona mai yawa da damina ko da rani.

Abin takaici na anan shine wani idan ya tashi noman sai ya manta da noma abin da zaici bayan yasan matsalarsa kullum ta abinci ne sai kawai ya tashi ya noma kayan kudi wadda sai ya sayar ya sayi abinci. Wani kuma zaiyi noman abincin domin ya samu wadda zai ci da gidansa a shekara tare da rage kashe kudaden da yake samu daga albashi, ko kasuwa ko kuma buga-buga da yakeyi , sai kawai ka samu ya sayar da abin noman tun farkon girbi don yaga kudi, a sak**akon haka sai ka sami mutum ya koma yana sayen abincin da shi da kansa ya noma, a farashi mai tsada a lokacin da kasuwa ta hau.

Ka TUNA: Noman Ka Shi Ne Jarinka!

Sai da HAKURI da JURIYA ake yin Nasara!

Idan kai manomi kuma har kana da aiki ko sana’a, amma har yanzu kana fama da matsin rayuwa, to akwai abin da bai daidaita ba a rayuwarka. Yana iya kasancewa ba aikin nomanka ba ne ya gaza – kai ne baka tsara yadda zaka ci ribar sa ba.
Ka duba menene abinda yafi cinye maka kudade a kowace rana cikin rayuwarka? A matsayinka na wadda bashi da abinda za aci a shekara cikin gidansa bana tsammanin amsa zata wuce abinci.

A noma koda abin da zakaci da iyalinka a shekara ka sha dashi kaci ribar noma domin zaka sami damar tara dan albashinka da ribar da kake samu a sana'a kaja jari ko ka biya wasu bakatun rayuwa masu muhimmanci k**ar kudin maganin rashin lafiya da kudin karatun yara tare da buda nomanka har ka zama babban manomi wata rana.
Idan kuma baka albashi ko sana'a tsayayyiya idan gidanka ya wadatu da abinci lokacin tsayawa da kafarka yayi.

Me Yake Faruwa da Manomi Mai saida amfanin gonarsa ba tare da ya ajiyewa iyali ba.
- Yana komawa ya saya da tsada a kasuwa
- Da Kudin Albashinsa ko na sana’arsa zai dinga sayen abincin da bai k**ata bayan ya noma ya rika saye ba.
- Dole mutum ya rika yawan ciwo bashi da kuma fuskantar karancin kudi.
- Dole ne mutum yayi fama da matsin rayuwa duk da yawan gumin sa a gona.
-Fadawa harkar aikin karfi marar tsari,maula,bara, roko da tumasanci.
Haka kuma irin wannan ne yake haifar da tsoro tare da zama kasan yan siyasa da masu wadata cikin rashin yanci tare da zubarwa kai kima ta hanyar biya musu gurbatattun bukatu.
MENENE MAFITA?
✅ Idan kayi noma kafin ka sayar da wani abu daga ciki ka lissafa adadin abincin da gidanka suke bukata na tsawon shekara idan bai kaiba saika saida abinda gida bai bukata ka cike gibin idan yayi saura sai ka sayi wani abu na kadara dashi ko kayi kasuwanci dashi domin samun jarin komawa noma wata shekarar a ciki. Kai idan ma abin da ka noma rabin shekara kawai zaiyi maka kafin ya kare kana da lokacin da zaka sayi wani ka cike gibin cikin nutsuwa.
✅ Na biyu kayiwa kanka adalci: Kada ka sayar da abincin da iyalanka zasuci saboda biki (na aure,sallah,da jin dadi) ko kuma sayen tufafin kece reni, mota ko kara jarin sana'a duk ba alheri bane. Domin saida abincin da iyali zasu ci ganganci ne tare da kasadar kakabawa kai talauci tare da saka iyalinka cikin damuwar da baka da dalili mai kyau, wani lokacin irin wannan ke kawo rabuwar aure da reni daga 'ya'ya tare da lalacewar tarbiya saboda yunwa.
Duk wani abu na jin dadi yana wucewa ko ba'ayi shi ba, kuma rashin yin nasa bazai hana yin rayuwa ba, abinci kuwa shine ke rayar da gida, haifar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da bada damar hutu ko tara kudi a huce. Don haka duk wadda ya sallami matsalar abinci gabadaya a gidansa ya k**a hanyar tara arziki.
✅ Idan kana ganin idan ka ajiye amfanin gona tsawon shekara zai lalace to yana da kyau ka koyi dabarun Ajiya tare da Sarrafa amfanin gonarka yadda zasu kai shekara basu lalace ba.
✅ Ka Rika Hada Noma da Ilimi domin kada noma ya zame maka kawai gumi da wahalar banza. Ka maida noma ya zame maka dabarar inganta rayuwa da habaka hanyar tara arziki.
A wannan rubutu mutum uku kawai zanyiwa uzuri bisa dalilai biyu da rabi (2.5)
1) Manomin da ya saida abin da za'a ci a gidansa domin neman lafiyarsa ko ta iyalansa don magani.

2) Manomin da yasan zai iya cike gibin abin da ya dauka, zai iya saida wani sashe na amfanin gonarsa domin karatun yayansa, amma shima babu uzuri idan duka ya saida domin ana iya dakatarwa da karatun idan babu abincin da za'a ci.

3) Manomin da ya saida amfanin gonarsa saboda yana da abincin da iyalansa zasu ci na tsawon shekaru.

“Manomi mai wayo shine wanda ke hada noma da ilimi.”

Ka zama mai hangen nesa. Kayi noma domin samun abinci, zaman lafiya, da habakar arziki. Idan kana noma ba ka tanadin na iyali – to ba kayi noma ba, shirmenka kawai kayi domin idan gida bai wadatu da abinci ba duk kudin da ka samu anan zai kare, babu kai babu damar tara kudi.
"Wannan hannuka mai sanda ne ga kowane manomi"
Ku tura wannan sako domin taimakawa dan uwanka manomi ya tashi daga dogon barcin da ke hanashi yin arziki!
Marubuci: Bashir Abdulaziz Bulangu
CEO Ilimin Noma Da Kiwo General Agricultural Services

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ilimin Noma Da Kiwo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Ilimin Noma Da Kiwo:

Shortcuts

Share